← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 35

Sashe 10

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar wanda aka faɗawa micijin sau saurin barin wurin Imran ya yi ya tafi wurin Hajiya yana zuwa ya tsaya a gabanta. Ai da sauri ta gyara tsayuwarta tana ɗaga hannaye yadda Imran ya yi ra sanya su a gefen kanta yadda sojoji ke yi ta buɗe baki kuka na neman ƙwace mata sai dai tana tsoron sakin kukan dan kar micijin ya sareta ta ɗan ɗaga murya amma kuma ƙasa-ƙasa ta ce.

"Imran karanto min taken Nigeri'ar sai in ke faɗa idan ka faɗa ka san ni ba iyawa na yi ba, amma idan kana karantowa sai in ke bita, tun da gashi a gabana layi ya zo kaina" Hajiya ta faɗa idanunta a kan Imran da har lokacin bai saki hannayensa ba haka zalika ƙafafunsa na nan yadsa suke a haɗe, bakinsa kuwa sai jerawa Nigeri'a kirari yake, kamar wanda aka ce Nigeri'ar za ta watse idan ya dakata da yi.Sara ya fara a gabanta ko ƙaƙƙautawa babu, kuma babu alamar zai dakata, dan haka Hajiya sai ta fara kuka, kuka kawai take wiwi dan ta rasa ma yadda za ta yi. Cikin ikon Allah sai ya bar gabanta amma bata bar yin kukan ba, gaban Inna ya nufa yana zuwa ya tsaya. Kallon kallo suka fara da Inna wacce majina ta taru cikin tafukan hannayenta da ta rufe bakin da su, ganin micijin a gabanta sai ta ce a zuciyarta.

"Yau na tabbatar kai ba mutum bane, É—an ruwa ne, in ba É—an ruwa ba a ce jariri da kai amma har ka aan ka je gaban wannan ka je gaban wancan"

Ganin yana shirin kaiwa ƙasa sara sai Inna ta yi karaf ta fara masa waƙa.

"Haba Hasanunu, ɗan aljanna, haba hasanunu ƙaton kirki, haba Hasanuna ɗan Imirana, haba Hasanunu me sauya kala" Ta faɗa tana wani rausaya kai ita a dole ya bar gabanta, ai sai gani ta yi ya kai wani sara me ƙarfi.

"Lanjeriya ƙasar ƴan baiwa, lanjeriya ƙasar talakawa, lanjeriya ƙasar Bahari ɗan daura" Ta faɗa tana kuka hawaye shaɓe-shaɓe.

Wani saran ya kai wanda ya kusa samun ƙafarta ta janye da sauri, cikin kuka ta ce.

"Wallahi tallahi, ƙur'ani ban iya yaren nasaraba (Turanci) Dan Allah tun da dai Nigeri'a ƙasar hausawa ce ka barni hakan dan wallahi ban iya irin wanda Imirana da sojojo ke yi ba" Kamar wanda aka tsikara ya fara tahowa, gabaɗaya matan nan suka sha jinin jikinsu.
Kowacce ta shiga addu'a tana fatan kar ya zo wajenta, zagayasu ya yi sau ɗaya Mama da Hajiya da ke gefe, suka ƙara matsawa kusa da sauran kowa yana jin matsanancin tsoro.Gafe ɗaya ya koma ya tsaya yana ƙare musu kallo har Sadiya da ke tsugunne a wajen, Ashrof kwa hawaye sam basa tsayawa ga tausayin kanta da na ƴar uwarta da ma mahaifiyarta.

"Sahuuuu" Cewar Inna cikin tsoro, kowa da ido ya bita alamar tambaya.

"Yo jama'a ba dole na ce sahu ba tun da haka Allah ya ƙaddara mana yau, zama inuwa ɗaya da miciji, kuma miciji me son taken Nigeri'a to tun da Imirana ne ya fi iyawa sai mu bi ayari mu yi sahu, mu bi bayansa idan ya faɗa sai mu ke masa amshi da dai mu tsaya micijin nan ya mana ɗauki ɗai ɗai, dan ni kuma ban shirya mutuwa yanzu ba in barwa Tasalla Malam" Cewar Inna tana kuka abin tausayi abin dariya.
Gabaɗaya kowa sai ya fahimci maganar Inna haka take dan suna ganin kamar micijin ya fi son national anthem dan haka sai suka fara yin lafi a bayan Imran banda Sadiya da ke tsugunne a tsakiyar wurin, Imran da har lokacin yake a ƙame bakinsa bao huta ba da taken Nigeri'a yana kaiwa ƙarshe sai ya dawo farko. Yana faɗa su ma suna faɗa duk da ba kowa ke faɗa daidai ba irin su Inna da su Mama su ma sauran matan tsoro ya mantar da su cewa sun iya national anthem sai suka dawo kamar wasu ƴan koyo dan suna ganin kamar Imran ne ya fi iya wanda micijin ke so.

Suna cikin yi sai micijin ganin sun tattaru a waje ɗaya sai kawai ya shiga zagaye su, a mugun guje yake zagaye su har wani tsalle-tsalle yake, ganin hakan ya sanya suka ƙara tsorata, cikin tsoro da ruɗewa suka dunƙule a waje ɗaya, kowa ƙoƙarinsa ya samu mafaka a jikin ɗan uwansa, dan gani suke kamar in kana kusa da wani micijin ba zai zo wurinka ba. Imran da Mama sun ƙanƙame juna cikin rashin sani dan ita bata san shi bane shi ma bai san ita bace an haka kowa ya ƙwamusu baka jin komai sai sautin koke -koke.

Sai da ya gaji dan kansa ya koma waje ɗaya ya tsaya, kowa ya ɗan fara sakin ajiyar zuciya, Mama da Imran sai lokacin suka ankare sa sauri suka saki juna Mama na saurin juyawa ta dafe haɓa tana zabga salati a ranta, idan ba larura ba ya za a yi a ce sun rungume juna ita da Imran mijin ƴarta Sadiya. Kafin kowa ya gama tantancewa micijin ya buga wani uban tsalle ya hau kan bishiyar da ke tsakar gidan gabaɗaya kallo ne ya koma sama, kowa na kallon micijin da mamaki har da Sadiya ma da ta rasa bakin magana sai kuka, jelar ya kanannaɗe a jikin reshien bishiyar ya zaro kan sa yana kallon kowa da kowa, ganin haka sai kowa ya fara neman inda zai fake idan an sakko micijin ya dawo mutum sa fito.
Imran da gudu ya nufi wajen tukunyar dafa ruwan wankan jego da ke ɗore a kan murhun sai dai ba a kunna wutar ba, a ka Inna ke barinta saboda wahalar ɗorawa sai dai wani lokacin ta kan bar ruwa kaɗan a ciki. Yana zuwa bai yi wata-wata ba ya gotar da murfin tukunyar da yake babbace sai ya samu ya shiga ba tare da ya cire murfin duka ba, yana shiga ya ringisa a ciki, ya miƙo hannu ɗaya ya ja murfin ya rufe kamar me rufe ƙofa.

Matan nan sai gasu suna tseren shiga kicin da Inna, Inna ce a kan gaba, tana shiga ra sauke idanunta a kan freezer da sauri ta ɗauke idanunta dan ko ƙaunar ganin freezer bata yi.

Wasu lokarsu ta ɗazu suka ƙara komawa bayan sun garƙamawa ƙofar kicin ɗin sakata. Me fulawa da Hajiya da Mama suka shige ɗaki Hajiya ta shiga ƙasan gado dakyar tana kukkujewa amma ba damuwarra bace hakan mafaka kawai take nema. Mama cikin wardrobe ɗin Imran ta shige ta rufe, tana kallon yadda ta zaune kayan sirikinta har da gajerunan wandunansa. Me ƙunshi kuwa kayan wankin da ta gani a ƙulle a zanen gado masu yawa su ta sunce cikin sauri ta kwasa ta libgawa kanta.Sai wani zarnin fitsari take ji a hancinta ashe wandon Imran ne da ya jabgawa fitsari ranar da Inna ta rufe shi a ɗaki a ranar farko da Hassan ya zama miciji. Amma bata damu da warinnba tun da ta samu mafaka.

Ashrof kuwa bayi ta koma, ta banke ta aka bar Sadiya kawai a tsakar gidan tana kallon Hassan rataye a sama.

Inna da ke ƙasan wani dogon benci da da ake ɗora kayan abinci a kai ta rufa buhhuna kusan goma a kanta ta daddage ƙarfinta ta ce.

"Halima in ce dai kin samu mafaka, dan na ga Imirana tuni ya yi hanyar murhu, in kuwa tukunyar da nake dafa ruwa ya shiga dan na ji ƙaran murfin ina samun kaina wuta zan galgala masa sai na dafashi luguf ya dahu...
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣

Yadda Imran ya fito a firgice cikin kiɗemewa ko lura bai yi ba da Inna da ke tsaye, ƙaran dariyar da ta saki ne ya sanya ya dakata daga ƙoƙarin gudun da yake wanda shi kansa bai san ina ya nufa ba. Ganin Inna tana dariya har da nuna shi da yatsa sai ya dakata tare da haɗe rai kamar ba shi ne ya iyo gudun ceton rai ba daga cikin tukunya, sanadin zafin da ya ziyarceshi.

Kallon murhun ya yi ya ga yadda wuta ta kama take ci kamar wanda aka sanya fetur, ga sauran buhun nan wanda Inna ta saka bai gama ƙonewa ba.

"Lallai tsohuwar nan ta ga makwancina da yawa, yanzu ni ta balbalawa wuta? Dan na san dai ai ba za ta ce bata san ina cikin tukunyar ba, " Ya faÉ—a a zuciyarsa sai muzurai yake kamar zai hau Inna da duka.
Chapter 10 · 0% Book details