Sashe 21
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki faɗawa masu gidan Malam Isuhu ne da ya zo cirewa Hassan aljannu wanda Hajiya Amina ta turo" Cewar Malan dan ya ɗan ji shayin Inna ya ga kuma tana neman kunyata shi a gaban almajiransa, manyan almajiransa ne da ya riƙe tun suna yara har suka girma yanzu sun zama manyan garada amma da yake ba wani karatun kirki ake a makarantar ba har yau ba su yi sauka ba, kawai ya ajiyesu in zai je yin ruƙiyya ya tafi da su suke danne masa mai aljanin saboda majiya ƙarfi ne.
Shiru Inna ta yi sai lokacin ta tuna da inda ta ji sunan wato wanda Amina ta faɗawa Imran a waya zai zo. Kallon Malamin ta yi ta ga yadda ba ya barin bakinsa ya huta da mismis ko ambaton Allah yake ko kuma dan a ce yana yi ne shi dai ya sani.Jibgegiyar babbar rigarsa ta bi da kallo sai wani baza ta yake yana wani bada faɗi shi a dole Malami. Wata ƴar dariya ce ta suɓuce mata wacce a ranta ta so yinta amma ta kufce ta fito fili.
"Dariya kuma?" Cewar Malamin yana kallon Inna dan ya ɗauka ta gane shi ba wani Malami bane kawai dai yana son a ce ya yi suna amma ko almajiransa ba wani tsayawa yake a kan su, su yi karatu ba kawai dai ya ajiye su ne dan yawanci duk su ke ci da masa gida idan sun samo abinci. Da kuma aikin ƙarfi da suke duk wajensa nemansu ke ƙarewa.
" Lah dariyar farinciki ce na yi ganin babban Malami ya zo gidan nan, ashe kai ne Malam Isuhun da ake ta labari, yo da na san kai ne ma ai da tuni kuna cikin gidan nan kuna gabatar da aikin" Cewar Inna a fili a ranta kuma ƙwafa ta yi tana fatan Allah kai damo ga harawa.
Wani uban washe haƙoransa da basa samun wanki Malamin ya yi, ya ƙara gyara zaman babbar rigarsa jin Inna ta ce ana labarinsa ai tuni ya ji kansa ya fashe ya masa wani gingirim.
"Haka ne ai duk yankin nan da ni ake ji kuma da ni suke ƙafafa a matsayin babban Malamin da ya yi fice"
"Gaskia dai na ga alama" Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ƙara washe baki ta ce.
"Allah ja da ran Malam ai na yi komai cikin rashin sani ne, bari na maka iso dan babban Malami kamar ka ba ya shigo ba tare da an kintsa ba saboda girmama wa" Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gidan, tana zuwa ta ɗauke robar lemonta ta shanye tas, ta ɗauke Husaini ta mayar da shi ɗaki, shi dama Hassan yana ɗakin bata fito da shi falo ba dan ba wanka za a masa ba dan yana siffar miciji. Kallon Hassan ɗin ta yi ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa ta ce a ranta.
"Yau akwai daru" A fili kuma ta ce.
"Hasanunu bawan Allah kana da baƙon Malami"
Suna nan tsaye sai gata ta dawo ta ce su shigo. Matsawa gefe samarin suka yi Malam ya shiga gaba su kuma suka take masa baya suna wani wasa shi tare da koɗa shi sai ka ce wani basarake. Har falon Inna ta shigar da su Malam ya samu wuri ya zauna a kan kujera haka almajiransa ma suka zauna a ƙasa dan girmamawa. Inna da ke ƙoƙarin zama a kujera almajiran Malam suka ce.
"Iya ba a zama a sama idan Malam yana zaune sai dai ki zauna a ƙasa"
Galala Inna ta saki baki tana bin su da kallon mamaki, shiru ta É—an yi ta dakata da zama a kujerar ta kallesu ta ce.
"A min afuwa ƴan samari jikokina, ai ban sani ba, kuma ni ma na yi tunanin hakan ai girman Malam ne a masa komai" Cewar Inna tana neman ƙasa ta zauna. Malam Isuhu kuma sai ya fara wani gyara zama yana wani ƙara jan carbunansa bakin nan kwa sai mismis yake.
"A wane ɗakin aka kulle marar lafiyar? Dan yau ƙaryarsu ta ƙare sai mun fitar da kowa daga jikinsa" Cewar Malam yana wani gyaɗa kai.
"Eh gaskiya kam da ana samun irinku ai da aljannu ba za su yarda ma su zauna a jikin mutane ba" Cewar Inna tana ɗan ƙunshe dariyarta.
"Hakane kam ai nan da kika ganni ba na barin aljani sosai muka zuba artabu da su har sai sun gaji sun sakar min ragamar tare da bani haƙuri da kuma yin alƙawarin barin jikin mutum har abada" Cewar Malam yana nannaɗe hannun rigar kamar wanda aka ce za a hau dambe da shi.
"To Allah gafarta Malam yanzu za a fara aikin ne?" Inna ta faÉ—a cikin É—an girmamawa.
"Haba tsohuwa ya ba a tsadance ba za ki ce a fara aiki ai sai an tsadance tukunna mun daidaita na ji nawa za a bani"
"To gafarta Malam kai kake yanke abin sadakar da za a baka kenan"
"Eh" Kawai ya ce yana wani ɓata rai ganin Inna ta ce wai yana yanke abin sadaka, ita ma Inna baki ta taɓe ta ce.
"To bari matar gidan ta fito daga bayi sai ku tsadance"
"To" Kawai ya ce ya É—auki carbunansa wanda ya ajiye lokacin da zai naÉ—e hannun riga ya cigaba da laziminsa.
Suna nan zaune sai ga Sadiya ta fito daga wanka da sallama ta shigo da yake ma ta shiga da hijab wanka sai ta sanyo abinta gaishe da Malam É—in ta yi sauran samarin suka gaishe ta, haka kawai ta ji haushin ganin su musamman da ta ga uwar dorinan da suka zo da su, ban da sirikarta ce ta turo Malamin nan da babu wanda ya isa ya shigo mata gida da sunan wani abu.
Ɗaki ta shiga ta shafa mai ta sanya kaya ta ɗoro hijab ta fito da yake Inna ta ce ita ake jira falon ta dawo tana ƙoƙarin zama a kan kujera Inna ta dakatar da ita tana nuna mata cewa Malam ni kaɗai ya kamata ya zauna a sama. Mamaki duk ya hana Sadiya cewa komai ita abin da ya fi bata mamaki ma yadda Inna ta yarda ta zauna a ƙasa kuma take wani kaffa-kaffa da su tana wani sanyaya murya sai wani baiwa Malam ɗin girma take.
" Wato jiranki dama muke tun da me gidan naki baya nan za mu ƙididdige abin sadakar da za a bayar na aikin fidda aljanin"
Wani zaro idanu Sadiya ta yi jin wai ya ce za a fitar da aljani gabaÉ—aya ta diririce amma kuma Inna ta mata alama da kar ta furta komai kan hakan babu yadda ta iya ta yi shiru da bakinta.
"Wato za a bada dubu hamsin sannan ƙwaryar nono mayan manya guda biyu, da ƙwaryar zuma ɗaya sai kuma ƙwaryar dabino dukansu manya" Cewar Malam yana wani gyara zama. Daga Inna har Sadiya sa kallon mamaki suka bishi, Inna ce ta yi karaf ta ce.
"Haba Malam sai ka ce wanda za ka É—auki aljanin da hannu ka fitar dashi, in ce dai addu'a za ka yi ya fita kawai to wannan kayan ko aljanin ne zai tafi da su wato toshiyar baki za ka bashi" Cewar Inna tana kallonsa.
Wani irin haÉ—e fuska Malam ya yi ya fara wani zazzare ido cikin kaushin murya ya ce
"Babu wanda zai muku wannan aikin in ba ni ba ko da kun samu wanda zai muku to ba zai muku aiki kamar ni ba, ko da an fitar da aljannun to za su dawo ne"
"Ikon Allah to wallahi da sake dubu hamsin fa ga ƙwaraken nono da na zuma kai wai har da dabino, yo ai ka manta ka ce da manyan zabbi riƙaƙƙu guda bakwai" Inna ta faɗa ita ma tana ɓata ran.
"Idan baku da kuÉ—in mu za mu tafi"
"Yo Allah na tuba ku fi ruwa gudu mana, indai kuɗin nan da ƙwaraken abubuwan nan za a bayar wallahi ƙwara mijina Malam ya zo ya yi aikin a bashi kuɗin ni ma in san na mori wani abu nono da zumar kuwa da dabinon ma tsakurawa Tasalla a farar leda ladan ganin ido mu ajiye muna cin kayanmu, da dai a baka kai kaɗai da ranka ni ma ai matar Malam ce kai ni da kaina ma sai in yi aikin"
Wata uwar harara ya jefawa Inna ya ce
"Babu mai ja dani sai wawa, dan duk mai hankali ba zai ja da Malam Isuhu ba dan hukuncin Malam ba ya yin kyau" Ya faÉ—a yana kallonsu.
"Yo Allah na tuba ni zaka faɗawa haka? To kalleni da kyau fara nake ba baƙa nake ba ruwan sama ne ya wanke ni ruwan datti ya ɓata ni da zaman ƙauye ne ya mulke ni, Allah na tuba me zaka min wallahi ni Azumi matar Malam na sha tabara na sha lahaula"
"Allah gafarta Malam a bar aikin kawai" Cewar Sadiya cikin sanyin murya dan dama ita bata son wani aiki kawai an tashi an ɗakko wani Malami tausayinka sa sauƙi har da wasu uban dorinai ko wa ma za a duka da dorinan.
"Gidanku Sa'adiyya babu mai fasa aiki Malam indai aikin ka ya yi to za a baka duk kan abin da ka buƙata" Cewar Inna da ta danne fushinta tana ɗan murmushi.
Shi ma murmushin ya yi ya ce
"Yawwa ko ku fa ai duka abin da na lissafa haƙƙina ne a bani dan Allah kaɗai ya san artabun da za a yi da mu da su"
"Babu komai ai komai ma aka bada ba faɗuwa aka yi ba" Cewar Inna cikin sanyin murya. Sosai Malam ya ji daɗin maganar Inna yana wani jin kamar ya tashi ya taka rawa dan murna dan tun da yake ko aikin dubu uku bai taɓa yi ba amma gashi zai yi na dubu hamsin har da wasu kaya a ka.