← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai ana dara ga dare ya yi" Cewar Inna tana da dariya abinta sai nishaÉ—i take dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya dama tana sane wai karuwa ta taka matar aure, ta san sai an yi artabu dama. Sadiya kuwa kallonta kawai take ita dariya ma Innar ta bata ganin irin abubuwan da take ita kullum Inna ta san ta kan mugunta, sai dai hakan ya yiwa Sadiya daÉ—i dan ba a cutar mata da É—a ba.

Habu da Ƙasimu kuwa suna nan a durƙushe a takure wuri ɗaya ganin micijin a wurin Malam sai Habu ya ware jikinsa daga jikin Ƙasimu cikin zafin nama ya tashi tsaye Ƙasimu bai ankara ba sai jin Habu ya yi ya taka gadon bayansa, kafin ya ɗago ka ce me Habu ya kama drower ya ƙanƙameta cikin sakan biyu sai gashi ɗare-ɗare a saman drower, har wani murmushin jin daɗi ne ya kuɓucewa Habu ganin ya sha, dan ya san dai miciji iya ƙasa zai tsaya ba zai hau sama ba kuma ma jikin drower ɗin santsi gareshi miciji ba zai iya hawa ba. Wani haushi ne ya kama Ƙasimu ganin Habu ya tsira ya barshi.

"Habu ya ka min haka tun muna yara muke tare ko bara muka je in baka samu abinci ba nawa nake baka mu ci tare amma yau za ka mini halin ɗan adam yanzu da ka taka ni ka haye ni kan wa kake so in taka in hayo?" Cewar Ƙasimu kukan takaici na fito masa.

"Taka Malam ka hayo shi dama ai ya ci duniyarsa saura mu tun da ya tsofe ko yanzu ya mutu to dai dai ne" Cewar Habu har wani fito ya saki dan daɗi. Ƙasimu saitin Malam ya kalla amma ya ga Malam bai ma san me suke cewa ba bakinsu na kusa da na juna shi da miciji kawai ruwan hawaye kake iya hangowa daga idanun Malam suna rige-rigen sauka, ga majina sai zuba take rawanin nan ya kalle gabas maso yamma bakinsa kuwa kamar an kunna inji sai zuwa yake yana dawo wa. Ganin haka Ƙasimu sai dibara ta faɗo masa dan yana so shi ma ya haye wurin Habu su bar Malam tun da dai hankalin micijin na wurin Malam ƙwara ya haye kafin micijin ya ankara. Da sauri ya tashi ya hau kan mudubi ganin wuri ya yi nisa da drower ya sauka, wani uban tsalle ya yi sai gashi ya ɗane jikin drower a haka ya daddage ya haye suka rungume juna da Habu dan daɗi. A hankali micijin ya ja baya kaɗan ya waiwaya bayansa sai gani ya yi babu kowa a wurin da su Ƙasimu suke. Ja da baya ya fara yi har ya sauka daga kan gadon wata uwar ajiyar zuciya Malam ya sauke yana sanya hannu ya ciro rawanin hiraminsa da hularsa ya yi wurgi da su.

" Haba Isuhu mai sittin wata kan wata ya da cire rawanin ban girma kuma" Cewar Inna da ke tsaye a window tana dariya duk abin da ake a kan idonta, dan gani ta yi tsayuwa a jikin ƙofa ba zai mata yadda take so ba shi yasa ta dawo daga window take gani muraran a kan idonta. Malam kuwa jin muryar Inna a saitin windown da yake kusa da gado ya juya aikuwa suka yi ido huɗu da Inna tana masa dariya, ji ya yi kamar ya shaƙo ta ya shigo da ita ɗakin ita ma ta ɗanɗani bala'in da suke ciki. Amma babu hali ɗauke kansa ya yi daga kallon Inna dan za ta iya sa zuciyarsa ta buga kan miciji ya maida ya ga ya bashi baya ya tsaya cak kuma bai waiwayo ba bai kuma cigaba da tafiya ba. Malam sai ya fara tunanin ina almajiransa suke ganin bai ga ko ɗaya ba. Wani tsoro ne ya ziyarceshi dan duk tunaninsa micijin ne ya haɗiye su a taka ya saki fitsarin wahala dan gabaɗaya ya gama tsurewa cewa saura ahi za a haɗiye Hannu ya miƙa ya taɓo wandonsa jin lema jagaf ya ƙwalalo idanu yana ayyana cewa shi Malam ne uban Jamila da Jamilu da fitsarin wando yau, lallai firgici ya yi firgici.

*Masu fitar min littafi ku daina dan haƙƙina ne masu karantawa ma basu biya ni ba haƙƙina ne kowa ya san Allah na gafarta zunubai baki ɗaya amma baya gafarta haƙƙin wani a kan wani!*

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

*M* ➡️ *N*

*IMRAN*

Bayan an idar da sallar ya kira Sadiya a waya suka yi magana a kan snacks da zai siyo wanda za a raba a suna, dama saboda ma Hassan sai suka shawarta ba sai an zo gidan an yi wani abin rabo ba dan haka sai ya ce a sayi lemuka kawai in ya so sai a haɗa da snack dan hatta jakar da za a saka kayan duk ya bayar a yi yanzu zai je ya karɓo. Bayan sun gama wayar Inna ta kalli Sadiya ta ce.

"Halima ki tabbtar dai kin ɗauka min kyak (Cake) Ɗin mai yawa da dannat(Donot) Ɗin nan dan wallahi ina so Tsahare ta tafi da kayan sunan nan himili guda dan bana so ta je ƙauyenmu babu kaya mai yawa ƙwara ta je da abin arziƙin da za a daɗe ana batunsa a ƙauyen" Ta faɗa tana tashi ɗauke da kwanukan da ta ci abinci. Da kallo kawai Sadiya ta bita.

Bayan Inna ta wanki Husaini ta shirya shi lokacin Sadiya tana bayi tana wanka Imran kuma bai dawo ba, ƙaran bugun da ake yiwa ƙofar gidan da alama ma ba wai da yatsu ake ƙwanƙwasawa ba, hannu kawai aka jimƙe, ake faman doka ƙofar Inna tana zaune ta yi ɗai-ɗai tana ji amma ko alamar tashi bata yi ba bare a sanya ran za ta buɗe. Hannu ma ta sanya ta ɗakko wani lemo a frige da ta sanya wanda ta fasa ɗaya daga cikin cartoon ɗin da za a raba, buɗewa ta yi tana sha tana lunshe ido.

"Kai duniya budurwar wawa, wallahi daɗi da sanyin lemon nan har tsakar kaina, wayyo Tasalla gaskiya ana yi ba ke ni bana jin ma Tasalla ta taɓa shan lemon roba amma dai zan daure in danne kishi na in baiwa Tsahare robobi guda biyu wanda aka shanye lemon ta kai mata ta tsage ɗan ƙasan robar da ake bari da bai fi cikin cokali ba, ta suɗe in ya so ta ajiye robobin take ganin hoton lemon na jikin robar tana jin haushin ina ma tana da ƴan uwa a birni take shan lemo" Cewar Inna a ranta tana dariyar mugunta, tana ɗaga lemonta tana sha hankali kwance.Wani uban bugu da aka yi wanda ya sanya Inna zabura har lemon ya tafi wa Inna ba shiri har yana biyo wa ta hanci, robar ta ajiye ta tashi a fusace ta yi hanyar ƙofar gidan, tana zuwa ta ce

"Wai uban waye yake wannan bugun kamar wanda yake binmu bashi?"

"Buɗe ƙofa uban Jamila da Jamilu ne Malam Isuhu mai haddar izufi sittin wata kan wata" Ta ji an bata amsa. Shiru ta yi tana son gano inda ta ji wannan sunan kafin ƙwaƙwakwarta ta tuno mata ta sanya hannu ta cire jamlock ɗin a fusace ta buɗe ƙofar Idanunta ne suka sauka a kan wani ƙaton mutum da manyan kaya har da babbar riga ga wani hirami ya naɗa a kansa sai ka ce gammo ga wani carbi irin mai dubun nan guda biyu yana riƙe da su hagu da dama. Sai wasu manyan ƙartin maza guda biyu suna tsaye su ne ke bugun ƙofar shi kuma yana tsaye ya kame sai jan carbunan yake hagu da dama bakinsa yana motsi mismis. Mazan guda biyu ɗaya yana riƙe da manyan dorina guda biyu ɗayan kuma galan irin na mai da wata hula da alama wani abu ne a cikin hular.
"Ikon Allah kun yi ɓatan kai nan ai ba turu bane, ba kuma gidan maza bane(Gidan yari) Cewar Inna tana galla musu harara tare da sanya hannu a hancinta ta fato sauran lemon da ya biyo mata ta hanci dan har lokacin bata daina jin zafinsa a hancinta ba.

"Ke tsohuwa ki iya bakinki ba a faÉ—a mini magana" Cewar Malamin daga inda yake tsaye ya cigaba da jan carbunan kamar ba shi ne ya yi maganar ba.

"To fa lallai yau ake yinta to buÉ—e idonka da kyau ka gani Azumi ce ba matarka bace, har ni za ka kalla ka wani ce in iya bakina yo Allah na tuba kai har ka ma isa, yo meye a cikin ido banda ruwa"

"Ki kama bakin ki Iya" Cewar É—aya daga cikin Mazan nan.

"Oh abin da ya sa kuka riƙo dorinai dan ku daki mutane to indai zan daku ga wurin nan, dan wallahi sai uwaku ta yi da na sanin haihuwarku"

"Ba ta duka ake ba tsohuwa muna jiye miki Malam ya fusata ya maidaki tsuntsuwa" Cewar ɗaya yana kallon Inna da ta yatsina fuska tana kallon Malam ɗin da ke ta jan carbuna, a shelaƙe.

"Ah jemage zai maidani, ko baka ji ba na ce jemage zai maidani, ko ya maidani É—an tsako in hakan bai masa ba ma zai iya maidani tururuwa"

Gabaɗaya sai suka maida Inna kamar TV kowa kallonta yake cike da mamaki yadda ta haƙiƙice take magana babu tsoro ko ɗarr a tare da ita bayan kuma sun san Malam ɗin yana yiwa mutane kwarjini.
Chapter 20 · 0% Book details