Sashe 16
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna kuwa da dariya ke neman kunya tata ta ƙara danne dariyar ta shiga sakin wani munshari kamar wata jakin dawa, ita a dole bacci take, amma kawai Imran lura ne bai yi ba da ace ya lura har cikin Inna zai ga yana loɓawa irin na ƙyaƙyata dariyar nan.
"Innarmu, Innata, Innar Malam, ɗaya tamkar miliyan a wajen Malam ki tashi ki taimake ni kar in mutu in bar iyalina, dan ko micijin bai sare ni na mutu ba to tsabar fargaba za ta sanya zuciyata ta buga in mutu" Ya faɗa cikin kuka yana jijjiga ƙafar Inna.
"Kai duniya , wato wuya in ji tsula, wa ya faÉ—a maka barno gabas take, yaro ya ga uwar bari, to da wa ya ce maka karo da Azumi abu ne mai kyau, wai Imirana ne ke cewa Innarmu, kai har da Innata ma, wai ni Azumi da ya rainawa hankali da wayo ni ce Innarsa" Ta faÉ—a a zuciyarta tana dariyar mugunta.
"Wayyo zan yi gawa" Ya faɗa yana sakin kuka a hankali. Wani juya Inna ta ɗan yi ta koma ɗaya ɓangaren tana sakin munshari, so take sai ta gama wana shi sannan za ta tashin, a haka ya cigaba da magiya har dai ta ɗan tashi tana murtsuka ido duk da ba haske a ɗakin amma kuma kana iya hango hasken farin wata ya ɗan shigo ɗakin ga kuma asuba ma da ta kawo ki masallatai sao kiran assalatu ake.
"Waye wai ya dameni da shegen kira kamar wanda na ci bashi ban biya ba" Cewar Inna cikin muryar bacci wai ita ala dole yanzu ta falka daga bacci"
",Inna jikan ki ne Imran" Ya faÉ—a cikin sanyin murya yana addu'a da fatan Allah ya É—ora shi a kan Inna ta taimaka masa kar ta ja masa rai.
"Wa ka ce sunan naka, ba Imirana bane?" Ta faÉ—a dariya na son fito mata.
"Eh Imirana ne" Ya faɗa kamar yadda take faɗa masa dan shi gabaɗaya fatansa kawai su rabu lafiya dan ba zai iya da sabgar Inna ba gwara ya lallaɓata su rabu lafiya.
"Wai menene halan, ciwon ciki ne ya koro ka gabannin assalatun nan?"
"Dan Allah Inna kunna fitila ki ga, wallahi Hassan ne a cikin rigar jikina"
Murmushi Inna ta yi tare da tashi ta sakko ta kunna fitalar aikuwa haske ya gauraye É—akin.
"Meye wai ka wani surƙusa kamar mai naƙudar da ke yinƙurin haihuwa?" Cewar Inna tana danne dariyarta ganin yadda Imran yake kallonta idanu a gwagwgwale.
"Inna kalli ki ga cikin rigata" Ya faɗa yana daga durƙusan hannayensa a ƙasa haka gwiwoyinsa ma.
Ɗan yatsina fuska ta yi, sannan ta ɗan ranƙafa ta leƙa wai ita a dole bata ga micijin ba daga yadda take a tsaye. Ganin micijin da ta yi sai ta wani taɓe baki tare da sakin wani tsaki da ya matuƙar ɓatawa Imran rai, ta ce.
"Wai dama a kan ɗanka kake ta ƙwala min kira ka katse min baccina na gabannin asuba mai daɗi tsiya? Kana ta rafka kuka kamar an aiko maka cewar Amina ta mutu, wai me yasa kake da ɗan karan raki ne kamar mace"
Wani haushi ne ya turnuƙe Imran amma haka da daure ya ce.
"Wallahi Inna kawai ina tashi daga bacci na ganshi a jikina ban san yadda aka yi ba, ki taimaka ki fitar min shi ko ki taya ni tashin Sadiya ta fitar min da shi dan na tashe ta bata tashi ba"
"To sai me dan ya je wurinka, ina ce dai ita kaɗai Sadiya ke riƙitu da shi kuma dan ya je ya shiga rigarka shi wani abu wataƙila so yake ka karɓeta ma'ana nono yake so ka bashi...
"Nono kuma Inna?" Ya katse Inna da tambaya cikin tsoro
"Nono mana baka ga inda ya shiga ba kawai ka bashi ya tsotsa ka bani shi in kwantar da shi"
"Haba Inna wace magana kike haka wai? Nono kuma sai ka ce wata mace, baki ga ba yau d bai dawo mutum ba ko ita ma uwar tasa bata shayar da shi ba sai ni da ba nono nake da shi ba za ki ce wai na bashi"
"Ya baka da nono É—in nan, kuma wanda Allah ya halitta maka fa?"
"Inna!!! Wai me yasa kike haka dan Allah ki bar faɗa ma kar ki sa ya kafa min haƙora a ƙirji yana neman nono in bai samu ba ya cije ni in shiga uku"
Wata dariya Inna ta fashe da ita ta ce
"Imirana ni ka sanya wa ɓawon ayaba?"
Wani irin zare ido Imran ya yi jin furucin Inna.
"Ba dai matar nan bace ta sanya min micijin nan ba saboda ƙarfin hali...
"Na ce ba ni ka sanya wa ɓawon ayaba ya kada ni ba??? " Muryar Inna ta katse masa zancen zucin da yake.
"Inna ni ba da niyya na ajiye ba ban san ma na jefar ba kuma tsautsayi ne ya kawo kika faÉ—i"
"Ni ban san miciji ma ya je wurinka ba, kawai dai na ga kana buƙatar taimakona shi ne nake faɗa maka ta yaya zan taimaka maka bayan kai ma ka sa na faɗi"
"Dan Allah Inna ki taimaka min"
"To zan taimaka maka amma sai ka yi abin da nake so dan ka san ko a nan Kano ba a aikin banza, idan kuma ka ƙi to dan wannan matar taka mai kamar mesa ba tashi za ta yi ba gwara ma ka min abin da nake so"
"To Inna faɗi" Cewar Imran cikin ƙosawa da maganganunta da ya matsu a raba shi da micijin nan da ya masa ƙabe-ƙabe.
"So nake ka min rawa"
"Rawa kuma Inna?"
"Rawa mana in ba haka ba, ba zan cire maka ba"
"Ni da bani da ƙafa da me zan taka rawar"
"Gurguncewa ka yi ne?"
"A'a amma ba zan iya tsayuwa da ƙafafuna ba saboda gudun matsala" Inna ta fahimci me yake son faɗa dan haka sai ta ƙudurta ko ta ina ya biyo tana da hanyar ɓullewa.
"Ka min rawar a durƙushen nan da kake"
Shiru ya yi sai kuma ya ga mafita yake nema dan haka sai ya shiga rawa daga tsugunnen da yake yana ta rausaya kai. Kallonsa kawai Inna take dariya na cin ta.
"Haba Imirana rawa haka salam -salam babu ko kiÉ—a"
"Haba Inna da gabannin asubar nan wane irin kiÉ—a kuma ni da nake so na je na tafi masallaci"
"To jeka masallacin da micijinka ma gani ina Æ´an masallacin basu dare sun barka ba, kowa gudu zai ke kamar ya ga fatalwa"
"To ai ban san ya zan yi kiÉ—an ba"
"Waƙa zan ke maka kana yin rawar"
"To" Ya faÉ—a kamar ya fashe da kuka
In na faÉ—a sai kana min amshi, kana dawa kana cewa maliyo"
"To"
"ÆŠan maliyo maliyo"
Shiru ya yi bai ce komai ba takaici duk ya cika shi tsohuwar na son kaishi bango.
"Ba za ka yi ba?"
"Maliyo"
"Ya je ina ne"
"Maliyo"
"Ya je ilori"
"Maliyo" Cewar Imran yana amshi yana rawa ransa sai ƙuna yake yana jin kamar ya mammake Inna ga takaicin nauyin baccin Sadiya da ya addabeshi.
"Kake zazzakuɗa wa mana" Cewar Inna da ke ɗan tafi ƙasa-ƙasa.
ÆŠuwawu ya shiga zazzakuÉ—a wa yana yi hawaye na zuba gashi ba ya so micijin ya tashi, amma ya fahimci da gangan Inna fa sa yake rawa wai har da wani zazzakuÉ—a wa kawai dan ta sanyashi a bala'i.
Yana cikin rawar sai jin inna ya yi ta sauya baitin waƙar.
"Mu kama sana'a mata macen da bata sana'a aura ce, lale-lale maraba da ke zinariya"
Ai kawai Imran da ya lura Inna dan ta yi ta sanya shi rawar ne ba wai za ta rabashi da micijin bane sai kawai ya saki wani kuka mai ƙarfi wanda hakan ya sanya Sadiya tashi ba shiri, ta tashi a firgice jin kuka Imran tana tashi ta yi arba da Inna da ke tsaye kan Imran ta daddage tana tafi da waƙa.
"Ikon Allah yau kuma me yake faruwa wane irin dogon bacci na yi ne da ake wannan bidirin ban sani ba" Ta faÉ—a a ranta tana saurin sakkowa daga gadon.
*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, ku ma masu karantawa baku biya ba haƙƙina ne, kowa ya san Allah na gafarta zunubai gabaki ɗaya amma ba ya gafarta haƙƙin wani a kan wani! dk mai so ta biyabta karanta 300 kacal*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
*I* âž¡ï¸ *J*
" Subhanallahi Abban twins lafiya" Cewar Sadiya lokacin da ta sakko idanunta a kan Imran. Kafin Imran da ke kukan zuci da sarari ya yi magana Inna ta yi karaf ta ce.
"Haba Halima yo kya yi maganar lafiya ma kina ganjn mijinki a wannan hali na durƙuso, ƙura'ani ni duk tunani na naƙuda yake ashe wai duk labarin ƙanzan kurege ne mutum a dudduƙe ya zo cewa yake Innarmu, Innata" Cewar Inna tana sakin dariya. Da mamaki Sadiya take kallon wani uban gumi da hawaye ratata a fuskar mijin nata.Ga miciji a cikin singlet ɗinsa sai wani nishi yake fitarwa kamar wanda aka biyo da gudu.
"Ya Allah ni dai ina ganin abubuwan da na kasa gane ko fahimtar inda suka dosa shin wai meye tsakanin Inna da Imran ne?" Sadiya ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta tana miƙa hannu za ta fara ƙoƙarin cire masa Hassan ɗin.