← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Imirana wai dama kai ne a cikin tukunyar wankan jegon matarka, soyayya ce ta sanya kakeso a dafa ka ta yi wankan da kai a memekon a dafa mata ruwa?" Cewar Inna tana ƙoƙarin danne dariyarta har da ƙwalla. Gefen leɓensa na ƙasa ya danne da haƙori ji yake kamar ya saki kuka dan takaici. Juyowa ya yi yana ƙoƙarin barin wurin dan dama wurin da murhun yake a ɗan lungu ne ba a sararin tsakar gidan yake ba.Sai da ya fito idanunsa suka sauka a kan Shek da ke ƙoƙarin raɓewa a bayan Sadiya ita kuma tana gocewa tana matsawa yana ƙara bin ta. A take maganar Inna da take cewa kwarto zai yi fyaɗe ta faɗo masa, ai ganin Shek kusa da matarsa ba ƙaramin fusata shi ya yi ba, in ba iskanci ba ya za a yi yake ɓuya a bayan matar aure, shin uban me ma zai shigo da shi cikin gidansa. Cikin jin haushi da fusata ya nufo wurin su dan gabaɗaya kishi ya rufe masa idanu har wani diri-diri yake gani, hakan ya mantar da shi ƙalubalen da yasa ya shiga cikin tukunya, dan gabaɗaya ya manta da batun miciji bare har ya yi tunanin shi ne dalilin da yasa Shek ɗin ɓuya a bayan matarsa. Idanunsa sun rufe ko lura da micijin da ke gaban su Sadiyar bai yi ba,a fusace ya nufo su, dan nufinsa yana zuwa wajen zai manta da mutunci da abokantakar da ke tsakaninsa da Shek ya shaƙe masa wuya sai an ƙwaceshi dakyar a hannunsa tun da shi ma bai ga mutunci da haƙƙin makotaka ba son zuciya ya rufe masa ido har ya zo yake neman yiwa matar aure fyaɗe.
Yadda ya taho a fusace kamar kumurcin miciji za ka ɗauka yana zuwa zai ɗauki hukuncin da ba zai yiwa kowa daɗi ba, amma me sai da ya zo dab da su idanunsa suka sauka a kan Hassan da ya yi wata alkafira, kansa ya cake a ƙasa sai jelar ta zama a sama sai wani wulwula ta yake kamar fanka. Wani uban birki Imran ya ja, tare da haɗiye wani yawu muƙuuut, ajiyar zuciyar ya fara saki a jere- a jere kamar wanda ya ƙwaci kansa daga hannun ƴan fashi. Cikin sauri ya fara kalle-kalle yana so ya ga ta inda zai tsere, yana waiwayawa bayansa sai suka haɗa ido da Inna da ke dariya marar sauti, ganin abin da ke faruwa dan dama ta gama karantar cewa Imran kishi ne ya rufe masa ido ya tafi ba tare da ya lura da micijin da ke juya jekarsa kamar an ƙurewa fanka gudu ba. Ita ma Inna a tsoracen take dan abubuwan da Hassan ke yi yau sun girmi tunaninsu, amma kuma ganin Imran ya taka birki ƙiiii kamar wanda ya kusa faɗawa kwalbati ya lura da ramin gabansa, hakan ya yi lolacin da ya yi ido huɗu da micijin.

"Dole ka nemi mafaka Shek ba lefinka bane, tabbas na daina ganin lefinka ko ni na na shiga gidan matar aure tuni zan manta da igiyar aurenta, in har a irin wannan bala'in ne ko a cikin ɗan kamfai (Pant) Ɗinta sai mutum ya totsu ya yi mafaka" Cewar Imran a ransa, fuskarsa kamar ya saki kuka, ga ruwan tukunyar da ya jiƙa masa jiki sai tsiyaya yake daga jikinsa, kallon Shek ya yi da gabaɗaya gumi ya gama wanke masa fuska sai tsiyayowa gumin ke yi ta jikin gemunsa yana ɗisa a ƙasa, ga yadda ya jiƙe da fitsari da alama ya yi fitsarin sama da kifi uku.

"Wayyo maƙocina, ashe kana cikin gidan nan, wallahi Sadiya ta ce min baka nan da tuni kai zan nema amma ganin baka nan ya sa nake nema ya rungumi wuta da hannu na, yo wuta mana duk inda na rafki matar aure da hannu na ai na san na kama wutar jahannama" Shek ya faɗa yana kallon Imran da ke kalle-kalle dan shi gabaɗaya ya kasa tantance a raye yake ko a mace ko mafarki yake da yake ta haɗuwa da wannan iftila'in.

"Imirana wai ya ka toge abokinka yana maka magana, amma ka ƙeƙashe ƙasa ka tsaya kamar wani gini, kar fa Allah ya kama ka a kan haƙƙin maƙotaka maƙocinka na cikin wani hali amma ka kasa kai masa taimakon gaggawa" Cewar Inna tana kallon Imran tare da danne dariyarta dan wata uwar harara ya aika mata kamar dai ta ce ya damƙi wuta.

"Allah dai ya miki albarka tsohuwa, nagode ƙwarai da gaske da kika ƙara fahimtar da shi" Cewar Shek yana kallon Inna da ke tsaye can hanyar murhu, so yake ya gudu bayan Imran amma yana tsoron abin da zai je ya zo domun kuwa ya ga micijin zai iya wartoshi lokaci guda , a gefe ɗaya kuma ga Imran ɗin ma kamar a tsorace yake, duk da kasancewarsa uba ga micijin.

A hankali Shek ya fara lallaɓawa sai da ya tsugunna daga tsayen da yake, cikin sanɗa ya fara rarrafawa ya nufi wajen da Imran yake, sai dai a matuƙar tsorace yake dan kar micijin ya biyo shi. Imran kuwa kafe Shek ya yi da ido ganin ya tunkaroshi zai je ya goga masa kashin kaji, dan idan da micijin zai masa kara saboda kasancewarsa uab a gareshi amma yanzu ganin Shek zai sa ya canja shawara, wani kallo ya yiwa Shek ɗin, yana kallon wannan hiramin da ya ci tumuri da shi a tsantsarsa. Shek kuwa ya raba hankalinsa biyu, ɗaya yana ƙoƙarin ya kai wajen Imran ɗayan kuma a kan micijin da ya ga duk wulwula jelar da yake amma kuma idanunsa a kan Shek ɗin suke. Har ya yi kamar zai dakata sai dai ya cigaba da rarrafen, sai da ya je daf da Imran micijin ya sauke jelarsa ƙasa, cikin kiɗima Shek ya dakata da rarrafe, bai san lokacin da ya tashi ba sai ganin kansa ya yi a tsaye cankarkar sai dai ya kasa tsayuwa dai dai sakamakon karkarwar da ƙafafunsa ke yi.
Inna kallonsu kawai take tana so ta ga ta yadda wasan zai fara dan ta san babu yadda za a yi a kwashe lafiya. Tun da Hassan ya ajiye jelarsa a ƙasa sai ya juyo ya maida hankalinsa ka su ya fasa kansa yana kallonsu, Shek ganin ya ƙura musu idanu sai ya sha jinin jikinsa cikin sauri ya buɗe baki ya ce.

"Ka masa magana mana Imran kai da É—anka, ka yi saurin bashi umarni ya koma É—aki ni in samu in bar gidan ma dan na rasa wane tsautsayi ne ya kawo ni" Ya faÉ—a yana kallon Imran da ke jifansa da wata muguwar harara.

"Da yana jin umarnin ai da baka zo ka tarar da abin da ka tarar ba hatta uwata tana cikin gidan nan ban san ma a ina ta ɓoye ba, kuma da ya san cewa ni ubansa ne ai ba sai na bashi umarni ba zai yi abu, ɗazu a gabana ya tsaya yana kai sara" Ya faɗa kamar zai saki kuka.

"Ka manta baka faɗa masa cewa har ƙwaƙumar Rakiya ka yi ba cikin rashin sani" Cewar Inna tana dariya tare da tuno lokacin da ta hangi Imran da Mama sun rungume juna kamar za su koma cikin juna saboda tsoro. Banza Imran ya mata dan shi yanzu kawai so yake ya fice daga gidan dan ya gaji da wannan wasan kwaikwayon. Yana tunanin mafita sai ganin micijin suka yi ya fara zulalowa a hankali kamar baya so, sai da ya zo tsakaninsu inda suke tsaye Imran da Shek ya ja ya tsaya, Shek na ƙoƙarin matsawa ya ɓuya a bayan Imran sai Imran ya ce.

"Kar ka kuskura ka motsa dan wallahi idan ya sareka ba ruwana"

Wani yawu Shek ya haɗiye yana kallon micijin kamar ya fasa ihu saboda yadda ya ganshi dab dashi abin ya matuƙar ƙara firgita shi amma ba yadda ya iya haka ya daure ya tsaya a inda yake. Zagayesu ya fara yi amma bai yi yinƙurin yin komai ba, ganin hakan ba ƙaramin ruɗewa Shek ya yi ba, amma kuma Imran ya hanashi motsi kamar yadda shi ma Imran ɗin bai motsa ba.

Wani tsalle da micijin ya yi shi yasa Shek da Imran rungume juna, yana komawa can gefe sai suka saki juna suna maida numfashi, kowa neman hanyar gudu yake, fara zagaya su ya fara yi cikin kuskure sai Imran ya ɗan motsa aikuwa Shek ma ya matsa wurinsa, miciji kwa ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da su ba, haka suka shiga tsere, Imran a gaba Shek a bayansa, sai miciji a bayan Shek suna cikin zagaye Shek da ya ga micijin a bayansa yake kuma yana neman kai masa cafka sai kawai ya yi tsalle sai gashi ya ɗane bayan Imran, da yake jallabiyar ce a cikinsa kuma da zai haye bayan Imran be tattare ta ba sai ya zamana ya kasa ware ƙafafunsa ya zamana kamar goyo ya yi, sai ya zama kamar ƙadangare a jikin bango. Ƙafafunsa a sake amma kuma sai ya maƙalƙalo wuyan Imran, Imran kuwa tsabar ruɗewa ma bai san Shek ya ɗane bayansa ba shi dai kawai ya ji wuyansa a maƙalƙale sai ya yi tunanin micijin ne, aikuwa ƙafa me na ci ban baki ba, a haka yake ta sheƙa uban gudu a tsakar gidan.

Inna da ke can jikin bango tana hango su dariya kuwa cikinta kamar ya yi ciwo. Suna cikin gudun Imran ya kalli bayansa da wutsiyar ido, aikuwa ya hango Hassan na binsu hakan ne ya ankarar da shi cewar ba Hassan bane a wuyansa hannu ya kai bayansa aikuwa ya taɓo Shek da ke manne da shi kamar cingam haushi ne ya turnuƙe shi, yana mamakin ya aka yi ma bai ji nauyi ba sai ya danganta hakan da ruɗanin da yake ciki.
Chapter 11 · 0% Book details