Sashe 33
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haƙiƙa Inna tana cikin tashin hankali domin ba ƙaramin abu bane a ce ka san ranar mutuwarka duk da zai kasance za kake neman yafiya kafin lokacin amma tabbas za ka shiga tashin hankali, shi yasa yana daga cikin hikima ta ubangiji da ya ɓoyewa bayinsa sanin ranar mutuwarsu, da a ce kowa ya san ranar da wa'adinsa zai cika tabbas zai cigaba da rayuwa a cikin tashin hankali to wannan halin shi Inna ta shiga. Tana jin sanda Sadiya ta tashi tana shayar da yaranta da suka tashi amma ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba. Har sai da aka kira sallar asuba tana nan tana ibada amma kuma ko alamar bacci babu a idanunta dan gani take ita da ke shirin barin duniyar ma baki ɗaya to bata da wani lokacin jin daɗi a cikinta.
Haka ta tashi ta je ta tsaya a kan Imran tana kiran sunansa, ya tashi ya tafi masallaci Imran kuwa dama shi ma bai koma bacci ba dan gabaɗaya sai ya ji tausayin Inna har ma yana da na sanin mata abin da ya mata, dan tun lokacin da ya kama hannunta irin yadda ya ga ta rikice da kuma bayyanar tashin hankali a tare da ita shi yasa ma ya yi saurin cewa sai nan d sati biyu amma da niyyarsa sai ya dinga ja mata rai yadda za ta tsure sosai amma ganin ta tsorata sosai shi yasa ma ya ƙyaleta. Kuma yanzu yana tsoron ya fito ya faɗa mata gaskiya ido ya kuye da mujiya dan ya san Inna ba kanwar lasa bace dole za ta yi shirin ɗaukan fansa dan haka sai ya bar maganar a zuciyarsa yana fatan Allah sa ta saki ranta ta yi rayuwa cikin salama a kwanaki sha huɗun da yace za ta mutu duk da ya san da kamar wuya gurguwa da auren nesa amma yana fatan hakan.
Tana kiran sunansa sai alerm ɗin wayarsa ya shiga ƙara dan haka sai ya yi kamar ƙaran wayar ne ya tashe sa.
"Inna har kin tashi ke ma" Ya faɗa cikin sanyin murya dan duk da a gabansa take tana kiran sunansa amma in ta kirashi sau ɗaya sai ta ja carbin da ke hannunta bakinta ya motsa sannan za ta ƙara kiran nasa abin ya so bashi dariya sosai amma sai ya ji tausayin ya danne dariyar.
"Kayya Imirana ni dama ina nan ido biyu ai ban ko yi gyangyaÉ—i ba"
"Allah sarki Inna ki ce dai yau duk mun sha addu'a mun more?" Ya faÉ—a dan ya É—an jata da hira ta saki ranta ko yaya ne dan ya ji daÉ—i dan yana ganin ya tauyeta, saboda ita duk abin da take masa na iya duniya ne ma'ana bata masa abin da zai nuna barinsa duniya ba duk da miciji ma abin halakarwa ne amma ya san daga an raba shi dashi to zai daina jin tsoro ita kuma y mat abin da a ko yaushe za ta kasance cikin tsoro mai tsanani.
"An muku kam ba laifi, fa kaina kaɗai name yiwa amma daga baya sai nake yi da sauran al'umma ma dan addu'ar da ka yi a jama'i tafi saurin karɓuwa a kan wacce ka yiwa kan ka kai kaɗai"
"Allah sarki Inna mun gode, bari na yi sallah a je a shigo da abin yanka na suna wanda tun ranar da kika zo kikr yi da bakin ki cewa ba a kawo ba" Cewar Imran lokacin da ya tashi yana Æ´ar dariya duk dan ya sanya Inna farinciki.
"To Imirana" Cewar Inna cikin halin ko in kula É—in nan. Haka ta shige É—aki ta barshi dan bata so ta yawaita magana lokacinta ya tafi a banza ba tare da ta yi istigfari ba.
Haka dai Imran ya yi shirin zuwa masallacin zuciyarsa duk ba daɗi bai taɓa jin ya yi da na sani ba a kan abin da yake yiwa Inna sai yau, duk da a da ya ɗauka cewa duk abin da ta masa sai ya rama har ma yana ikirarin ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi, amma kuma yau ya ji ba daɗi sosai. Yana dawo wa daga masallaci ya samu suna ɗan zantawa da Sadiya amma har lokacin carbinta yana hannunta, haka Inna ta fito dan ɗora ruwan wanka a lokacin ne kuma Imran ya ɗauki kayan nan da ya yi amfani da su ya ɓoye a drowersa kafin gari ya waye ya fice d su dga gidan.
"Wai ni Inna dama kin san bakya iya kwanciya da ƙunshi kika yi kika kwanta, kalli yadda kika ɓata ƙafarki ai dama baki yi ba da dai wannan caɓe ƙafar da kika yi, kuma gashi ya kama sosai sai dai gabaɗaya kin caɓe shi" Cewar Sadiya da za ta tafi ta shiga wanka tana kallon Inna da ke ajiye ruwan wankan za ta fara yiwa yaran wanka. Kallon ƙafar kawai Inna ta yi ta sauke wata ajiyar zuciya tana rayawa a ranta cewa ƙafar da saura kwana sha uku a binne ta a cikin ƙasa menene ma na damuwa da caɓewar kunshi. Sadiya jin Inna bata, bata amsa ba sai kawai ta kaɗa kanta ta fita dan ta lura Inna shiru ya fiye mata yau ko magana bata so ga babu walwala a tare da ita bare ma ita da ke murna aminiyarta za ta zo yau amma sai ta ga yau ko murna fa maganar Tsaharen ma bata yi kawai ko yaushe bakin motsi yake alamar tana karanta wani abu ta kasa gane dalilin yin hakan. Ta san halin Inna dai bakinta baya shiru baya rabuwa d abin faɗa amma kuma yau sai ta ga Innar ta canja mata.
Bayan Sadiya ta yi wankanta shirya abinta tsaf lokacin har Mama da Ashrof sun zo ga kuma ƴan uwan Mama duk sun fara zuwa haka zalika Hajiya ma da maƙotanta da wasu dga cikin danginta sun iso gidan dai sai san barka amma gida ya fara cika, kuma sai maganar miciji ta kwanta kamar ma babu ita dan kowa sai sabgar gabansa yake. Ashrof da Mama da Hajiya kai da duk wani wanda ya san Inna kawai mamakin ta yake yau dan akwai wasu daga cikin matan nan da suka zo ranar da aka musu ƙunshi ƴan uwan su Imran amma ganin Inna shiru yau su ma sun fahimci akwai damuwa a tare da ita kowa sai ya tambaya ko lafiya sai ta ce lafiya lau wasu dai sun danganta hakan da cewa ko wani abu ke damunta kuma bata so ta faɗa. Dan dakyar ma ta yi wanka ko shi ma sai da Sadiya ta matsa mata, ko da ta fito babu abin da ta shafa kawai atamfarta ta ɗauka ta sanya ta ɗaura ɗankwali ta ɗauki carbinta ta zauna a kan kujera take lazimi tana kallon shige da ficen mutane ana ta hada hadar yin abubuwan suna. Dan ko lokacin da aka shigo da raguna manya -manya guda biyu da tinkiyoyi su ma manya guda biyu Inna tana gani aka shigo da su, jim kaɗan aka fita da su aka dawo da su a yanke aka rataye amma ko ci kan ka inna bata ce ba. Imran ma lemuka katan uku ya siyo mata da cake irin mai biyun nan ƙanana guda hamsin dan ta yi farinciki ya ce ga kashinya ta rabawa wanda take so amma haka ta karɓa ta yi godiya da fatan alkairi ta ajiye amma ba wai dan ta ji abin ya birgeta ba sai dai kawai ita yanzu komai na duniyar ya fice a ranta tafi so kawai ta ganta a gidan mijinta hankalinta zai fi kwanciya.
Tana nan zaune kamar an ce ta ɗaga kai sai kawai ta hango aminiyarta Tsahare riƙe da kaya ta shigo, tabbas ta ji daɗi a ranta amma ba kamar yadda take zaton ji ba a baya.Kafin ta tantance sai kawai ta hango Tasalla da wani bokiti da galan da wata jakar kaya madaidaiciya a hannnunta. Ai Inna da ta wani ajiye carbi a gefe ta ji wani takaici ya turnuƙeta ai cikin hanzari ta tashi tsaye kafin ka ce kwabo ita ma bata tantance ba sai kawai ganinta ta yi a bakin ƙofa ta taho a fusace kamar kumurcin miciji.