Sashe 27
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta since farar ledarta wacce ta zubo ƙaiƙayin hatsi ta haɗa da barkono ta daka ta zuba a leda ta ƙulle. Ya daɗe a ajiye a cikin jakarta dan tun kafin cikin Halima ya tsufa ta ajiye saboda idan za ta je ZAMAN WANKA ta ajiye saboda shirin ko ta kwana. Ledar ta since ta lallaɓa cikin falon da suke da yake sun baiwa ƙofa baya ne basi san me ke faruwa ba idanunsu a kan TV. Sai da Inna ta je bayansu kawai sai ta ga matar za ta juyo da sauri ta durƙusa Allah ya sa ma matar bata ganta ba sai da ta bari ta ɗan jima ta ji suna ta hirar yadda za a azabtar da ita, ta tashi ta zuba musu ƙaiƙayin nan mai barkono a cikin wuyan rigarsu sai da ta barbaɗawa mata da mijin ta lallaɓa ta fice. Ta baya ta bi tana yi tana laɓewa dan so take ta gano inda sauran sojojin nan suke wanda suka ɗakko ta. aikuwa ta hangosu zaune a kan benci sun bata baya suna cin wani abu haka su ma ta lallaɓa ta je sai da ta zubawa kowane a cikin wuyan rigarsa cikin hanzari ta bar wajen ta koma ɗakin da aka ajiyeta. Ta maida mukullin yadda suka ajiye shi a jiki ta rufo ƙofar sai dai bata kulle ba.
Sojojo suna kallo bai ankara ba sai ganin ya yi ya miƙe tsaye zimbet yana zazzare ido dan raɗaɗin barkonon da ya ziyarci fatar bayansa ya haɗe da ƙaiƙayin ya bashi wani azababben zafi da raɗaɗi. Yatsina fuska matar ta yi tare da taɓe baki ganin abin da mijin nata yake yi kamar wani mahaukaci sabon kamu. Tana shirin masa magana sai ita ma a take ta ji wani raɗaɗi ya ratsa fatarta kamar wanda aka tsatstsaga mata fatar bayan da wuƙa ko reza aka zuba gishiri ko yaji haka ta ji a take ita ma ta miƙe suka shiga zarzage -zazzage sai idanu take zarewa kamar ta yi ƙarya an zo mata cakar ƙarya.
A take suka shiga zirya a falon babu wanda ke iya taimakawa ɗan uwansa kowa ta kai ta kai yake kowa ɗauki yake nema sai ife-ife da soshe-soshe suke kamar za su karce fatar jikinsu amma kuma ƙaiƙayin ƙaruwa yake . Su sa suke hannu bibbiyu dan shi mijin ma ya yi xaman ƴan bori a ƙasa sai susa yake amma kamar ya yi hauka ga ƙaiƙai ga raɗaɗi , ita ma matar da ta gaji sai zaman dirshan ta yi ta miƙe ƙafa tana sosawa shi ya kalli gabas ita ta kalli yamma sun raba jaha mijin da matar, can ya gaji ya kwanta a ƙasa yana gurza bayansa a ƙasa amma ina jin abin na neman wuce gona da iri sai ya fara kiciniyar cire riga, yana gama cirewa ya cigaba da soshe soshe ƴarsu na musu sannu.
Hakan bai masa ba sai da ya tuɓe kayansa duka daga shi sai gajeren wando, tashi tsaye ya yi sai zagaya falon yake yana wani dira ƙaƙafu, matar ma kiciniyar cire riga ta fara ganin tana neman cire kayan ya doka mata wata uwar tsawar da ta sa ta suka shige ɗaki ita da ƴarta shi kuma ya yi hakan dan kar wani cikin yaransa ya shigo duk da dai basa shigowa sai ya musu izini amma dai idan wani uzurin ya tashi zasu iya shigowa bare yau da ya san ya ajiye Inna a gidan ya san ba za a rasa nono a ruga ba.
Suna shigewa ɗaki da ya ji bala'in ya yi bala'i a sukwane ya fito daga part ɗin nasa ya fito yana ƙwalawa yaran nasa kira, daga inda suke suna ta tutumurtu suka rugo wurinsa a guje cikin son cila umarninsa ganinsu su duka a tuɓe da gajerunan wanduna kowa hannu a jiki kowa na susa kamar su yi hauka.
Shi ma yana susar ya kalle su yana wani zare idanu.
"Meye hakan kuma kuke yi kuna min yawo a gida a tuɓe?" Ya jefa musu tambayar yana soshe soshe. Sara masa suka yi suna ta susar kowanne idanunsa jajur.
" Oga wallahi kawai muna can baya a zaune sai kowa ya fara jin ƙaiƙayi da raɗaɗi mun rasa menene" Suka haɗa baki wurin bashi amsa har lokacin kowa susar yake har ogan.
Yana shirin yin magana ai da ya ji wani azababen ƙaiƙai sai ya manta da basu amsa tun yana yi a tsaye har ya kwanta reran a ƙasa sai birgima yake su ma maimakon su taimaka masa sai ƙaiƙan ya ci ƙarfinsu suka kwanta a ƙasan daga gefe duk da halin da suke ciki amma sun san Ogan su ne basu jeru da shi ba, yana gefe yana birgima da gurza bayansa a ƙasa suma suna gefe suna yi kamar yadda yake, sai da suka ji ƙaiƙan ya ɗan lafa suka dakata Oga ne ya fara tasho sai wani cin magani yake yana wani harare-harate shi a dole kar a kawo masa raini cikin haɗe rai ya ce.
"Ina tsohuwar nan?"
"Tana É—akin da ka ce a kai ta"
"Kun kulle ta kuwa"
"Eh Oga da mukulli ma"
Sai lokacin ya ɗan ji ya daina zargin Inna dan ya san dai babu yadda za ta yi ta fito ɗaki a kulle amma da ba zai taɓa yadda ba ita ce silar shigarsu halin da suke ciki ba sbd ya san za ta iya yin komai sai dai ai babu wanda ya ga wanda ya aikata wani abu kowa ya tsinci kansa ne a halin dan haka sai aka dangana hakan da ko aljannun gidan ne suka musu hakan.
Ɗakin da Inna take suka nufa domin a je a mata hukunci tun yau za ta fara karɓar hukunci dan ya yi alƙawarin sai ta kwana uku suna azabtar da ita sannan za a maidata sunan da damun mutane da shi ma ba za a yi tana nan ba sai dai a bata labari haka ya ƙudurta a ransa.
Inna da ke cikin ɗakin tana ta addu'a a kan Allah ya fitar da ita daga gidan sojojo lafiya dan ta sha jin ana cewa sojoji basa ragawa mutane babu ruwansu sai su zartarwa mutum hukuncin da ya musu, tana kuma fatan kar su gane wani shiri da ta musu dan ta san shirin shi kaɗai ne zai ƙwace ta daga uƙubarsu, tana nan zaune tana ta jan sunayen Allah sai ta fara jiyo maganarsu, hakan ya sanya ta cigaba da addu'a, suna zuwa ɗaya daga ciki ya sanya hannu ya murɗa mukullin bai lura cewa a buɗe mukullin yake ba, dan haka shiga kawai suka yi.
Inna da tun da suka shigo ta kafe su da idanu dariya na cin ta yadda gabaɗayansu suka yi ankon gajerunan wanduna ga wata ƙasa tun daga kan su har bayansu. Cikin izza Ogan ya kalli Inna zai fara magana sai kuwa ya ji ƙaiƙayin ya dawo sabo dal, kamar an haɗa baki su ma sai suka ji hakan a take suka layu a jikin bango suna susa da jikin bangon kowa yana goga bayansa dan lokacin ma sun manta matsayin Ogan nasu a wajensu kowa ta kai ta kai yake.Inna sadda kanta ƙasa ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa ganin duk sun haukaci lokaci guda.
"Oh ni Azumi ko ina matar sojojon take, tana can ita ma tana fama ga ƙaton ciki ga susa, ai dama in zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wato kun kawo ni za ku azabtar da ni gashi nan ido ya juye da mujiya. Cewar Inna a ranta.
Sai da suka É—an dakata da su sar sai kawai idanunsu ya sauka a kan wani miciji da ke can gefe kusa da Inna sai dai ba su yake kallo ba ya basu baya, sai dai ya fasa kansa. GabaÉ—aya sai suka sha jinin jikinsu, gashi ko bindiga babu a wurinsu lokacin bare su ce za su harbeshi, a take Inna ta gane tarkonta ya kama su.
" Kuna gani na haka to wallahi ni lunbu-lunbu wutar ƙaiƙayi ce, kuma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya, wa ya faɗa muku barno gabas take ai wallahi faɗa da aljani ba daɗi, wai ku nan wayon a ci an kori kare daga bakin ɗinya, ai iya gani ƙyalewa" Cewar Inna a zuciyarta tana tashi tsaye daga inda take zaune da ta fahimci tarkonta ya kama tsuntsu.
Sai da ta ɗaure mayafinta a tsantsa sannan ta turo ɗankwalinta gaban goshi ta taka a hankali ta isa wajensu da suka takure a waje ɗaya su duka dan gabaɗayansu Oga ya basu labarin micijin gidan Imran da ya faɗa musu jariri ne yake zama micijin, dan haka kuma abin da ya ƙara ɗaure musu kai sun san dai su suka kawo Inna ita kaɗai suka kulle ta a ɗaki ita kaɗai amma yanzu ga miciji tunaninsu micijin aljani ne dama shi yasa ya biyo ya ceci Inna. Tana zuwa gaban abokin Imran ta kama tsantsa ta ce.
"Sojojo har ni za ka sa a kamo a kawo gidan nan a kulle ni dan ka cutar da ni, to ga Hassan nan ya biyo ni zai cece ni dan haka sai ku shirya artabu da shi"
"Dan Allah ki taimaka mana ki ce ya tafi wallahi za mu maidaki gida yanzu ba tare da mun taɓa lafiyarki ba" Suka haɗa baki wurin faɗa. Wata dariya ce ta zo wa Inna ganin yadda suka yi buɗu-buɗu da ƙasa kamar wanda aka tono daga cikin rami wai duk garin susa suka zama kamar wasu fatake, danne dariyar ta yi ta kallesu ta ce to ni zan tafi na barku tate da shi a sha gumurzu lafiya ai kai sojojo ina fatan baka manta ba da karonku da shi"
Gabaɗaya sun ruɗe da maganar Inna dan haka suka shiga ihu da kururuwar bata haƙuri ba ga Ogan ba, ba ga yaran nasa ba.
"Ai ya faɗa min ba zai juyo gareku ba sai na bashi umarni dan haka yanzu zan bashi umarni ya cika aiki" Ta faɗa tana ɗakko mukullinta daga cikjn ɗan tofinta dan Ogan da suka shigo sai ya kulle ƙofar ya cire mukullin dan haka mukullin yana hannunsa.