← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Halima tun da na ji dama-dama bari in je in kwalfe ruwan can da muka sha tsunduma ni da mijinki a ciki, in ɗauraye tukunyar in ɗora miki na wankan yamma wuri ma ya ƙure ki yi wankan a wanki Hussaini shi kuma wancan lokacin da ya sawaya ya dawo mutum sai a wankeshi dan wallahi ban iya wankan miciji da hannun nan nawa"

"To Inna"

"Kai ai yau dai an sha bidiri a gidan nan, yo wuta na babbakawa Imirana, ai yana jin ba kanta sai gashi ya fito a guje har yana gwara kansa a murfin tukunyar, ashe dara za ta ci gida, ni ma miciji an biyo ni sai gani ina iyo a cikin ruwan zafi" Ta faÉ—a tana dariya.

"Allah kyauta" Cewar Sadiya tana danne dariyarta.

"Amin dai wallahi ai na ji zafin ruwan nan, na É—auka ma wutar za ta tashi, sai Allah ya dube ni bata tashi ba"

"Inna ki bar É—ora ruwan tun da bakya jin daÉ—i"

"A'a wallahi sai an É—ora so kike jikin ki ya yi tsami kike ciwon jiki, ai wankan jego shi ne zai sa kike jin daÉ—in jikin ki.

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

3️
*E* ➡️ *F*

~DARE~

Bayan kowa ya kwanta a makwancinsa kamar kullum, Hassan dai a haka yake bai dawo mutum ba dan haka, kwantar da shi kawai aka yi a gadonsa. Inna da ke ta jiran dare ya tsala ta aikata abin da ta shirya, dan haka bakam ta yi babu wani bacci da take. Bayan ta ga dare ya tsala ta tashi zaune ganin Sadiya tana ta bacci abinta ta taɓe baki ta ce.

"Oh ni Azumi yarinyar nan shegen nauyin bacci gareta kullum bacci kamar wata kasa, ni dai ba ni kika biyo ba, dan ni ina cikin mutane wanda basu da nauyin bacci" Ta faɗa a zuciyarta tana sako ƙafafunta ta sakko daga gadon, a hankali ta nufi falon tana zuwa ta kunna fitilar falon ganin Imran lulluɓe a cikin bargo yana ta zabgar bacci ta taɓe baki tare da jijjiga kai ta yi dariyar ƙeta a ranta ta ce.

"Imirana ba dai ni ka jefarwa ɓawon ayaba ya niƙa ni da ƙasa ba dan mugunta, to zan nuna maka kowa ya ci tuwo d Azumi miya ya sha, in dai Azumi ce an buga an ba mu. KoTasalla ta yi iya yinta ta gaji ta bari, a hankali ta shiga janye bargon da Imran ya rufa da shi sai da ta cire gabaɗaya ta ga har lokacin baccinsa yake bai ma san abin da take yi ba. Ƙwafa ta yi a ranta ta wuce bedroom cikin sanɗa saboda tsabar ƙarfin hali Hassan ta kinkimo a siffar miciji, falon ta dawo, Imran ta kalla da ke sanye da singlet sai dogon wando na bacci, cikin sanɗa ta nufi wurin Imran, ajiye micijin ta yi duk da faɗuwar da gabanta yake amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ta daure tare da danne tsoron da take ji, dan ta yi alƙawarin sai ta aikata abin da ta shirya. Singlet ɗin ta ɗan ɗaga daga ƙasa sai da ta tabbatar ta buɗu ta ɗakko Hassan da ta ajiye a gefe guda ta sanya shi daga ƙasan singlet ɗin Hassan da ke ta bacci ya ɗan motsa sakamakon ɗan jijjigashi da Inna ta yi, tana saka shi cikin singlet ɗin sai ya fara tafiya a hankali sai da ya sanyo kansa ta wuyan singlet ɗin Imran, sai ya kwanta a jikin Imran ɗin.

Inna kuwa ganin komai ya mata yadda take so sai ta yi dariya a ranta ta ce.

"Mu zuba mu gani"

Imran da ke bacci jin sanyi na shigarsa sai ya ɗan motsa kaɗan, ya ɗan takure jikinsa, jin abu manne a ƙirjinsa cikin giyar bacci sai ya miƙa hannayensa ya ƙara rungume abun tare da sakin ajiyar zuciya kallonsa Inna ta yi a ranta ta ce.

"Kudurarre me shegiyar jarabar tsiya duk tunaninsa Sa'adiyya ce ya runguma, da ni kake zancen" Ta faɗa tana ɗaukan bargonsa ta rufesu shi da micijin, a hankali ta kashe fitilar ta lallaɓa ta koma makwancinta.

*IMRAN*

Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, dan da ya ji ɗumi ma lokacin da Inna ta maida masa bargon ta rufa masa sai ya ƙara ƙanƙame micijin ya cigaba da yin baccinsa abinsa. Da yake wajen sha biyu da wani abu ne Inna ta yi masa wannan aiki, wajen ƙarfe haɗu da wani abu na asuba sai ya ɗan yi juyi kaɗan ya miƙa hannu idanunsa a rufe ya ja bargo ya rufe ƙafarsa da ta buɗe. Gefen kan micijin ne a wajen hancinsa dan haka da kan micijin ya dan dunguri hancinsa sai ya ɗauka Sadiyarsa ce a cikin baccin aikuwa ya ƙara ƙaƙumeta tare da ƙara gyarawa hancinsa zama a saitin kan micijin yana cigaba da baccinsa. Ƙaran wayarsa na alerm ɗin da ya sanya shi ne abu na farko da ya farkar da shi daga bacci, dafe micijin ya yi da hannu ɗaya duk zatonsa Sadiya ce dan a bacci -bacci yake ya ma manta cewa Sadiya ta haihu kuma Inna tana ZAMAN WANKA babu ma dalilin da zai sa su kasance shi da Sadiya a katifa ɗaya har ma a bargo ɗaya indai Inna tana nan.

Ɗayan hannun ya miƙa ya lalumo wayarsa da ke neman ɗauki, har lokacin idanunsa a rufe ruf, sai da ya ɗakko wayar ne ya ɗan buɗe idanunsa cikin yatsina fuska ya kalli screen ɗin wayar, alerm ɗin ya kashe yana shirin maida wayar ya ajiye ya tashi sai kawai hasken fuskar wayar ya sauka a kan micijin, da mamaki ya ji hannunsa ɗaya rungume da abu, ƙwaƙwalwarsa ce ta fara kai masa tunanin me Sadiya take yi a jikinsa bayan Inna tana gidan, dan son ta addabi mutane da sababi, idanu ya ware fesss a kan micijin wani uban ihu ya ƙwala ya buɗe bargon yana ƙoƙarin tashi zaune dan gabaɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, gabansa sai faɗuwa yake, hannu ya kai yana son yakice micijin daga jikinsa amma me sai ya ji a manne suke da juna a cikin singlet ɗaya wacce dama ta ɗan masa faɗi kuma sai micijin ya ƙara taɓata tare da buɗata duk da hakan dai a ɗame take a jikinsu sun zama kamar tif da taya.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Wace ƙarar kwana ce ta sanya wannan tsautsayin kasancewa da ni" Ya faɗa a zuciyarsa wasu hawaye da bai san da su ba suka fara yiwa fuskarsa tsinke. Dakyar ya samu ya tashi zaune yana jin jelar micijin a kan cinyarsa, haka ya tashi yana kiciniyar ɓanɓaresa daga jikinsa amma sanyin da jikinsa ya yi ga kuma karkarwa da kuma tsabar fargabar da yake ciki ya kasa yin haka. Tsaye yake so ya miƙe amma ina hakan ya gagareshi, dan haka kawai sai ya yanke hukuncin ta tafi bedroom neman ɗauki dan bashi da ƙwarin gwiwar da zai iya yin ihu a jiyo shi har a taimaka masa, gashi kuma ya ga da alama ma micijin bacci yake dan haka ba ya so ya tashe shi a samu matsala dan haka sai ya yanke hukuncin tafiya ɗakin ko da, da rarrafe ne. Hannayensa duk biyun ya ajiye a ƙasa yana ɗan lallaɓawa ya saukar da gwiwoyinsa daga kan katifar a haka ya fara rarrafawa micijin na cikin singlet ɗin kamar dama a nan aka halicce shi.

"Yiiiii, wayyo Allah, yau kuma haka na tashi ni Imran" Yake kukan cikin ɗan ƙasa da murya yana tsoron kar kukan nasa ya tashi micijin.

A haka har ya je tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan rarrafawa kamar wanda aka cirewa laka, dan ko kaɗan bashi da ƙarfi gwiwar tasa ma idan ya ɗaga ji yake kamar wanda aka mata dabaibayi da igiya.

"Sadiya, Sadiya,Sadiya" Cewar Imran cikin raɗa-raɗa, kamar wanda aka shaƙewa wuyansa. Inna da tun falkawar Imran tana jin yadda yake ta tutumurtu da miciji a cikin singlet, dan hatta shashshekar kukan da yake duk tana jin sa. Bare kuma yanzu da ya zo tsakar ɗakin da suke ji take kamar ta tashi ta taka rawa dan murna saboda kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Tun yana kiran da bakinsa har ya dawo yana ɗan buga jikin gadon a hankali dan shi ba ya so ko kaɗan ya tashi micijin ya je ya sare shi a samu matsala, hakan ne ma yasa yake lallaɓawa ya tashi Sadiya domin ta kawo masa ɗauki dan ya san ita kaɗai ce za ta taimakeshi. Ganin dai Sadiya da shegen nauyin baccinta ba za ta tashi ba dan har ƙafarta yake ɗan ja amma shiru sai ka ce wata matacciya. A hankali ya lallaɓa ya koma wajen setin da Inna take kwance, dan ya tashe ta, ta taimaka masa duk da ya san karon su da Inna ba daɗi amma yaya ya iya dole ce uwar naƙi za ta sa ya nemi agaji a wurin Inna dan ko kusa bai kawo cewa ita ce ummul aba isin shigar da micijin cikin jikin nasa ba.
"Inna! Inna!! Inna!!!" Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya kaɗan dan ji yake tsabar tsoro fitsari na neman kuɓuce masa dan har cikinsa ma murɗawa yake ba ya so kuma a yi abi kunya dan ya san dai matasawar aka ɗauki wani lokaci ba a rabashi da micijin ba to ba kallon fitsari da kashi ba da a ce maza na haihuwa to ya tabbata har haihuwa sai ya yi ko da kuwa hanji ne zai haifa.
Chapter 15 · 0% Book details