Sashe 31
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shiga gaba mana Inna ai kamar ba girmamawa in barki a baya" Cewar Imran yana matsawa gefe Inna ta wuce gaba ba dan ranta ya so ba, sai dan babu yadda za ta yi kuma ma bata son yin hayaniya dan tana ganin kwananta ya kusa ƙarewa bata da lokacin ɓatawa.
Haka ta shige falon jiki sanyi ƙalau. Imran kuwa sai da ya tsaya ya ɗan matse dariyarsa sannan ya shigo ɗauke da jakar Inna ya ajiyeta a inda take ajiyewa. Kallonta ya yi ya ga ta zauna a ƙasa ta rafka uban tagumi.
"To Inna ya ga kujera kuma za ki zauna a ƙasa?"
"Yo ai da na ga ƙarshen alewa ƙasa"
"Kamar ya Inna?"
"Yo duk mai rai mamaci ne kuma dai da ƙasa aka halicce mu kuma cikinta za mu koma sannan daga cikinta za a ƙara fito damu" Cewar Inna tana tuna nan da kwana goma sha huɗu tana cikin ƙasa hakan ya sanya ta share hawayenta tana jin bata da wani abu da ya wuce ta cigaba da kusanta kan ta ga Allah har ranar da mutuwarta za ta riske ta.
" To Inna ai kowa ya san da hakan amma ai manzo S.A.W ya ce, ka zauna a cikin duniya kamar matafiyi, sai hakan hakan ba yana nufin ka bar komai na jin daÉ—in duniyar ba" Ya faÉ—a yana kallonta sai ya ji duk tausayinta ya kama shi.
"To haka ne Allah dai ya sa mutuwa ta zame mana hutu, Allah sa mala'ika mutuwa ya zare ranmu a hankali, Allah raba mu da duhun kabari, azabar kabari nauyin ƙasa ya bamu ikon amsa tambayoyin kabari ya sanya aljanna maɗaukakiya ta zame mana makoma kuma madawwama" Cewar Inna cikin sanyin murya.
"Amin dan alfarmar annabi da alqur:ani" Cewar Imran yana neman wuri ya zauna a kan katifarsa.
"Amma Inna ki tashi ki koma ki kwanta mana tun da yanzu fa dare ne"
"Ina ni ina runtsawa Imirana ai sai dai ko na tashi na rinƙa nafilfili har asuba ta yi sallar asuba sai na zauna lazimi har garin Allah ya waye"
"To ikon Allah abu mai kyau gaskiya hakan ma ya yi Inna Allah dai ya ja da kwana ya sa ki yi tsawon rai dan ki yi ibada mai yawa"
"Kayya Imirana ni da wa'adina ya kusa cika ina zancen dogon kwana sai dai a ce Allah sa mu cika da kalmar shahada"
"Wa'adinki ya kusa Inna ta yaya aka yi kika sani kuma?"
"Uhmm da wasa nake kasan ɗan adam ana so ko yaushe ya kasance cikin shirin tafiya, in ya wayi gari ya sanya a ransa ba zai kai yammaci ba in ya kai yammaci ya sa a ransa ba zai wayi gari ba haka ne kawai ya sa na faɗi hakan" Cewar Inna cikin wayincewa dan ta ga ta kusa yin ɓaran ɓarama sai kuma ta tuna mala'ikan ya gargaɗeta.
"Eh kuma fa haka ne"
"Bata sake tanka masa ba ta fita ta É—auro alwala dan bata so ma zuciyarta ta cigaba da kissima mata dalilin sakkowar Imran har yana biya ta suna magana yana kuma nuna mata kulawa da tausayawa, ga sakin fuska, dan ita yanzu ta kanta take bata ma so ta fara tunanin wani abu ita da za ta bar duniyar ma dan me za ta damu kanta. Haka ta zo ta wuce ta É—auki sallayarta da hijab a jakar ta nufi É—aki.
"A sanya mu a addu'a Inna " Cewar Imran yana dariyar zuci.
"To Imirana" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.
"Yo ni ina ma na ga lokacin yiwa kowa addu'a yau ai yau kawai nafsi - nafsi, ta kai-ta kai, kaina kawai zan yi ta roƙawa gafara da neman dacewa a lahira"
09030283375
*MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3ï¸4ï¸âƒ£9ï¸âƒ£âž¡ï¸5ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
*LAST PAGE*😿😂
Barkanmu da kasancewa a ckn watan rahma watan ibadah RAMADAN MUBARAKðŸ˜
*RANAR SUNA*
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, Tasalla dai yau yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan gabaɗaya bacci ya kasa zuwar mata, tsaf ta nemesa ta rasa bacci ya ƙauracewa idanunta sai zumuɗi take d murnar a kan gari ya yi ya waye su ɗauki hanyar birni, tun kiran sallar farko ta tashi ta yi alwala ta zauna tana lazimi, ita kana murmushi sai ƙwace mata yake ita kaɗai ta san irin daɗin da take ji da irin farincikin da take ciki.
"Kai Allah da ikonsa komai sai Allah ya nufa shi yasa wasu ke cewa kishiya in alkairi ce Allah tabbatar da alkairi to ni dai gashi kishiya ta wani wajen ta zame mini alkairi tun da gashi sanadin kishiya (Buk ɗina, labarin yadda sanadin kishiya ta haɗu da ƙalubale gidan aurenta tun daga ranar da ta sanya ƙafarta a gidan aure ta fara arba da bala'i kala-kala har makancewa sai da ta yi sanadin kishiya) Duk da dai ta wani wajen Azumi ba kanwar lasa bace amma dai yau ta mini rana har da yammaci ma" Cewar Tasalla da ta tashi daga kan abin sallah tana linkewa da hijabinta.
Babu ɓata lokaci ta shiga wanka ta fito ta shiga shiryawa cikin atamfarta mai kyau, tana cikin sanya kwalli sai ga Malam ya shigo ɗakin nata daga masallaci yake, ganinta zaune da ƙaramin madubi a hannu tana gwale ido yake kallonta da mamaki, washe haƙora ta yi tana kallon Malam da ke mata kallon mamaki.
"Malam har an dawo daga masallacin"
"Eh na dawo" Ya faɗa yana kallon wani jambaki sabo da ta fito dashi daga wata baƙar leda ta daddage za ta shafa.
"Tasalla menene hakan kike yi dan Allah" Cewar Malam yana kallonta.
"Wai a ina ?" Ta faÉ—a tana kallonsa.
"Wannan ba gazar bane da yara ke sanyawa?"
"Au wai wannan? Ba gazar bane Malam jambaki ake ce masa fa"
"Ko ma dai menene, ba dai sawa za ki yi ba"
"Shafawa zan yi mana Malam, saƙo na yi kasuwa aka siyo mini saboda na shafa, ko so kake in tafi birni suna dangin kishiya ake nuna ni da baki ana gulmata ko kwalliya ban iya ba bare kuma dama Azumi da ke min kallon ban taɓa zuwa birni ba ta faɗa musu cewa babu abin da ma iya wallahi ba zan juri baƙinciki ba gwara dai na cancaɗa adona da kwalliya yadda babu mai mini kallon raini alqur'an"
Ta faɗa tana wani shafa jambakin tare da haɗe laɓɓanta waje ɗaya ta daidaita jambakin.
"Ni na ga ikon Allah saboda zuwa birnin ne za ki shafa gazar da girmanki da komai tsofe-tsofe da ke saboda gudun magana za ki shafa, kuma ma da kike cewa Azumi za ta faÉ—a musu magana a kan ki bake kika ce mini ita ta gayyaceki ba, kin ga Tasalla wallahi bana son tashin hankali kar fa ku je cikin mutane kuke raba jaha ke da ita ij kin san da matsala kamar kullum kawai ki yi zamanki dan ni ba na son haÉ—in gurugudu"
Wani uban bugawa ƙirjin Tasalla ya yi da ƙarfi jin Malam zai shiga tsakaninta da burinta na zuwa birni, sai yanzu ta gane ɓaran ɓaramar da ta yi na cewa Azumi za ta faɗi magana a kan ta ai da sauri ta washe bakin nan na tsohuwa da ya sha jambaki ta ce.
'Allah sarki Malam ni fa ba haka nake nufi ba ka dan san mu mata ba ma rabuwa da gutsuri tsoma dole dai idan aka haɗu a gidan suna ko biki sai an yi da mutum tun daga suturar da ya saka zuwa kwalliyar da ya yi kai hatta tafiyar mace ma sai an saka ido musamman kuma aka ce maka kishiya ce ya je dangin kishiyarta to qur'ani hatta ƙasan zanen da ta saka sai an duba an ga wace irin atamfa ce ko leshi shi yasa ka ga na faɗi hakan, kuma jambaki da na shafa ai ba haramun bane ko Malam, in kuma kana ganin na goge sai na goge, dama na siya ne dan kar a kawo maka raini"
"A kawo mini raini?"
"Eh mana wallahi idan ban gyara jikina ba na fito fes muna zuwa za a ke cewa baka adalci a tsakanin matanka banbanci kake nunawa a tsakaninmu wata tafi wata a wurinka" Ta faɗa cikin sanyin murya tana wani karkata kai kamar ƙadangaruwa ita a dole kissa.
"Kuma fa haka ne da gaskiyarki to in kwa haka ne ki gyara abinki fes ki fito É—oÉ—ar da ke" Cewar Malam yana washe baki dan yadda Tasalla ta yi magana da kissa sai ya ganta kamar Azumi dan ita ce mai irin wannan yanzu za ta sanya shi yin abin da bai yi niyya ba.
"Ka ce fa ai dama na ce bari in gwada yadda Azumi ke yi, dan ko ranar da za ta tafi birni ZAMAN WANKA haka ta shaƙe murya ta rinƙa karairaye murya har sai da ka barta ta tafi, shi yasa na ce ni ma yau dai bari na gwada sa'a ta" Ta faɗa a zuciyarta tana wani jin ita ma yau ita ce.
" Aikuwa zan gyara É—in dan ba na so a yiwa Malam É—ina kallon marar adalci a tsakanin iyalansa" Ta faÉ—a tana rufe fuska da tafin hannunta, alamar kunya wai ta ce Malam É—inta. Shi kuma wani irin murmushi ne da dariya suka haÉ—e masa lokaci guda yana jin wani kansa na neman fashewa.
"Wayyo daÉ—i kasheni wahala ta huta, ashe dai ni ma da saurana a fannin soyayya ashe dai matata bata ganin tsufana take ce min Malam É—inta duk da dama masana fannin so sun ce soyayya bata tsufa sai dai masu yinta su tsofe" Cewar Malam a zuciyarsa yana jin zuciyarsa fes.