← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 35

Sashe 12

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata mugunta ya yiwa Shek wani uban wujijjiga Shek Imran ɗin ya yi sai kuwa ga Shek yashe a ƙasa ya je da reran, miciji da je binsu da gudu yana zuwa sai ya bi ta kan ruwan cikin Shek, gabaɗaya Shek numfashinsa ya ɗauke lokacin da micijin ya bi ta kansa, bai ankara ba ya ji saukar wani fitsarin daga jikinsa. Imran kuwa wani tsalle ya yi ya koma gefe, micijin kamar an ce bi Inna kawai sai ya yi hanyar lungun murhu a mugun guje yana haɗawa da tsalle.

"Inna ce a nan lungun me maka ZAMAN WANKA" Cewar Inna cikin ruɗewa dan bata taɓa zaton zai zo inda take ba, ganin ya kusa ƙarasowa sai kawai ya saddaƙar ta yi wani uban tsalle ta faɗa cikin tukunyar da Imran ya fito.

Azaba da raÉ—aÉ—in ruwan ne da ya É—au zafi ya ziyarce ta, kuka ta saki a zuciyarta tana cewa.

"Gwara na silsilge in yaso daga nan a kai ni maƙera su bani maganin wuta in ke shafawa a kan in bari ka sareni in mutu in barwa Tasalla Malam" Tana daga cikin tukunyar ta hangi micijin ya bar wajen, a sukwane ta fito ta ɗauki wani ruwa da ke cikin bukiti ta sheƙa tun daga kanta ta jiƙe jargaf.

"Kai Allah ka rabamu da wuta, ka haramtawa wuta cin naman mu duniya da lahira, yo ni da nake cewa sai na yiwa jikina ruwan zafi, saboda sanyin da na shaƙa a firinji ai yanzu na huta duk da sai cewa ruwan zafinsa ya wuce misali, oh duniya shi yasa ake cewa idan za ka gina ramin mugunta ginashi gajere gudun kar ka afka wata rana, gashi dai Imirana bai dahu ba ni na kusa dafewa lugugu ma ba luguf ba" Ta faɗa idanunta kafe a tsakar gisdan tana leƙawa dan ganin ƙwaƙwaf.

Shek da ganin miciji ya nufi lungun nan bai san lokacin da wani ƙarfi ya zo masa ba, da mugun gudu ya nufi bishi wani tsalle ya yi sai gashi ya ɗane bishiyar lokaci guda kamar wani biri, wani reshe ya samu ya hau ya zauna ya kama ya riƙe ƙam. Yana a saman nan, Sadiya da zuwa lokacin kawai ta daina kuka tana daga inda take tana ganin iko da ƙudurar da ta sauka a gidanta, micijin kuma yana dawo wa daga lungun sai ya daina gudu yake tafiya a hankali a hankali yana zuwa tsakiyar gidan sai kawai ya yi lifet kamar ya mutu, idanunsa ma a rufe ruf. A hankali Sadiya ta nufi wurinsa cikin sanyin jiki ta sanya hannu ta ɗan taɓa shi amma ko motsi bai yi ba.

"Shikenan ke ma Allah ya yanke miki wahala É—iyar nan Hassan ya mutu kowa ya huta Husainin kaÉ—ai ma ya isheki" Cewar Inna cikin sanyin murya tana tahowa wajen.

"Inna da ransa fa bai mutu ba da alama gajiya ya yi ko kuma bacci ne ya É—auke shi.
" Cewar Sadiya tana kallon micijin da tausayawa a gefe ɗaya kuma tana haushi da zafin maganar da Inna ta faɗa na cewar Hassan ya mutu.Taɓe baki Inna ta yi tana wani kallon Hassan ɗin da ke kwance kamar babu rai a tare da shi.

Shek da ke maƙale saman bishiya ya musu ƙuri da ido, duk abin da suje a kan idonsa, ganin dai micijin kwance magashiyan sai ya fara tunanin durƙowa daga sama domin ya gudu. Ƙasa ya kalla daga saman bishiyar wani uban zurfi ya gani daga saman zuwa ƙasa.

"Allah da iko ashe dai wurin haka yake da zurfi amma lokaci guda na haye saman nan ko dan a tsorace nake" Ya faɗa yana jinjina irin namijin ƙoƙarin da ya yi wajen hawa bishiyar.

"Duk da haka dai sai na durƙo na gudu ya faɗa yana seta inda zai faɗo, aikuwa wara Bismillah da ya yi sai ji kake tik ya faɗo, a tsugunne ya faɗo, dan haka ko kallon su Inna da ke wajen micijin bai yi ba da Imran da shi ma yake tsaye ya kama tsantsa a wajen. A 360 Shek ya busawa rigarsa iska.

"Yaka liman zo karɓi yajin gayyata ka kaiwa matarka" Cewar Inna tana dariyar ganin yadda ya sanya gabansa hanyar ƙofar gida a guje ko waiwaye ba ya yi.

"La shakka laisal mushkila ku riƙe abinku" Cewar Shek lokacin da ya je ga ganshi ya buɗe ƙofar gida, shi ne ya ɓuga amsar da ya baiwa Inna.

Ƙo ƙofar bai rufe musu ba yana fita ya rinƙa zabga gudu kamar an biyo shi, mutane a hanya wanda basu san shi ba sai kallon mahaukaci suke masa waɗanda suka san shi kuwa sai kallon ba lafiya ba suke masa, a haka dai ya ƙaraso ƙofar gidansa yana haki. Wani uban bugu ya yiwa ƙofar gidan sai da ƙofar ta bugu da jikin bango, Barira da ke zaune tana tankaɗe garin tuwo jin buga ƙofar da aka yi a bango sai ta tsorata, bata tantance ba sai ganin Shek ta yi ya shigo jallabiya tattare a hannunsa ga hiraminsa ɗaure a ƙugunsa ko takalmi babu a ƙafarsa.

Ta san ba abu bane ƙarami kuma ba wani abu ne me sauƙi zai sa Shek wannan gudun famfalaƙin, tunaninta sai ya bata ko dai wani aka harba ko kuma bomb aka saka a wani wurin, ai tana ganin ya nufi ɗaki da gudu ita ma ta suri robar da take tankaɗe da kuma rariya a ciki dan ta san garin nan shi kaɗai garesu idan ya salwanta sai dai su kwana da yunwa. Tana shigowa falon nasu ta garƙame ƙofa ganin Shek ba ya falon sai ta bishi bedroom ɗin, a can ma sai sa ta sanya mukulli ta kulle ƙofar sannan ta ajiye garin da ke cikin roba ta kalli Shek da ya yi zaman ƴan bori a tsakar ɗaki, wata dariya ce ta ƙwace mata gani yadda farar jallabiyarsa ta jiƙe ga kuma ƙasa a jiki sannan kuma ga tumurin hirami a ƙugunsa sannan bakinsa sai mismis yake. Sai da ta yi dariyarta son ranta sannan ta kalleshi ganin ko kulata bai yi ba ta ce.

"Ya Shak wai duk wannan gudun bomb ɗin ne kamar wanda ke gudu ranar ƙiyama, ashe dai ku ma Malamai kuna tsoron mutuwa?"

Saurin wayancewa ya yi tare da ƙoƙarin seta kansa ya ce.

"Ba haka bane Barira, wato ainihin komai muƙaddari ne amma mutuwa ai dole ce in kin ga ana irin wannan wahala ake gudu bi ma'ana ceton rai kena" Ya faɗa cikin maganar Ustazai.

"Allahu akbar Kabiran, ni wallahi na É—auka ma wani ne ya É—ora maka bakin bindiga a kan ka" Ta faÉ—a tana kallonsa.

"To kusan hakan ne, ko ma fiye da haka, wallahi arangama muka yi da zulƙululu"

"Me ye kuma zulƙululu?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Miciji" Ya faɗa yana kwashe komai ya faɗa mata. Dariya take tun ƙarfinta har da hawaye.

"Yo Ya Shek ai dama na faÉ—a maka amma ka ca wai zancenmu ne na mata wai mu mata mun saba gutsuri tsoma da yaÉ—a jita-jita, yanzu kuma ai idanunka sun gani"

"Ki bari kawai Barira ai yau na yi mugun gamon da zai daɗe yana zaune daram a ƙwalƙwalwata, ni dai ko hanyar gidan Imran na daina bi"

"Kai da abokin ka"

"An bar abotar, ko fitsarin da na yiwa jallabiyar nan ya fi a ƙirga, ita kanta na san sai ta ce Shek da fitsari a jikina kuma, carbina ma a can na barshi, ko dan wa ma yake ta carbi ana ta kai wa yake ta kaya" Ya faɗa yana since ƙullin hiramin ya fitar da takalmansa na dai suka sha dariyarsu, ya yi wanka ya canja kayansa.

A can gidan Imran kuwa Imran yana ganin Sadiya ta ɗauki micijin da sauri ya yi ɗaki dan shi abin ya wuce tunaninsa. Yana shiga bedroom ua nufi wardrobe ɗinsa zai canja kaya, yana buɗewa Mama da ke can ciki ta tsorata tare da maƙurewa a can ciki, Imran da bai lura da ita ba ya miƙa hannu zai ɗakko riga sai ya ɗora hannunsa a kan ƙafar Mama da sauri ta janye ƙafar tana zazzare ido, jin ya taɓa mutum ya miƙa kansa ya leƙo ciki aikuwa suka yi ido biyu da Mama, tuna abin da ya faru tsakaninsu ɗazunya sanya ya ji kunya, Mama ma kunyar ce ta rufe ta, cikin ƴar murya ta ce .

"Ashe Imran ne" Ta faÉ—a tana jin kunyarsa bayan abin da ya faru É—azu yanzu kuma ya kamata a cikin lokarsa.

"Mama micijin nan fa ya yi bacci" Ya faÉ—a, jin hakan sai Mama ta ce.

"To, to, to" Ta faɗa tana zuro ƙafarta ta fito daga drower wata muguwar kunyar Imran na kama ta.

Hajiya da ke ƙasan gado jin Imran ya ce miciji ya yi bacci sai ta ɗan yunƙura za ta tashi amma ta ji ba hali.

"Imran, Imran, Imran" Ta shiga kiran É—an nata.
Imran jin muryar Hajiya a ƙasan gado cikin sauri ya durƙusa ya kamo hannunta, jin ta maƙale a take ya, ya ɗage katifar ya fito da ita yana mata sannu.

"Kai yau mun ga ta kan mu, ko ma in ce na ga ta kaina, wallahi cinnaku ne a ƙasan gadon nan haka suka rinƙa safa da marwa a jikina babu yadda na iya, cizo kamar wani ƙudan cizo haka nake ji idan suka manne a jikin fatata" Ta faɗa kamar za ta yi kuka, sannun dai Imran ya cigaba da mata, ana haka sai ga Inna ta shigo, ganin Hajiya na karkaɗe jiki tana faɗar zaman uƙubar da ta yi a ƙasan gado sai ta shiga dariya, kowa kallonta yake da mamaki ta ce.

"Yo ni dama kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha kuma sata a gidan ɓarawo wallahi rance ce, ba ni ka yi ta yiwa dariya ba ranar da na ƙarasa kwana a ƙasan gado ba yau na rama a kan uwaka dama ai ɗan kuka shi ke jawa uwarsa jifa" Cewar Inna tana dariya.
Chapter 12 · 0% Book details