← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 35

Sashe 13

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yau dai an yi kwaɗo, sirika a lokar siriki, hallaw sirika a ƙasan gadon sirika kuma duk jika ne ya haddasa hakan, sannu Amina, sannu Rakiya" Inna ta faɗa tana dariya. Babu wanda ya tanka ta dan su burinsu ma su bar gidan kawai.Haka suka fito suka bar Imran da ke shirin canja kaya, sai da ya canja ya fito daga ɗakin, sannan me ƙunshi ta buɗe kayan wankin da ke jibge a kanta ta fito. Tana fitowa ta zo za ta fita daga ɗakin kamar an ce ta duba mudubi ta hango wani baƙin aljani baƙiƙƙirin da shi ƙirji ta dafe tana ambaton Allah sai da ta yi gaba za ta fice daga ɗakin sai ta gane ashe ita ce, kawai baƙin lallan ya mayar da ita haka. Fuskarta ta tsaya ta ƙarewa kallo sai kawai ta rushe da kuka, a haka ta fito lokacin ƴan matan nan har sun fito daga maɓoyarsu sun tafi, sai Ashrof kaɗai, da kuka ta fito falon kowa yana kallonta Imran takaici ne yasa ya ɗauke kai Inna kuwa dariya kawai take tana cewa.

"Gobe ma ki ƙara yiwa tsoffi haka, ita ma yarinyar nan me ƙananun nono ta tafi wai ita nan mace ce ƙirji babu komai yo irinsu ne idan suka tarki saka rigar nono za ki ga rigar nonon da ban ƙirjin da ban"
Ba abin da ta ce a haka ta sanya mayafinta ta naɗe kamar niƙaf duk da haka ana iya ganinta amma hakan ya ɗan suturta ta dan idan bata rufe ba ta san duk inda ta fita gudunta za a ke.

Imran ɗaki ya koma ya ɗakko kayansa cikin jaka, ya fito. Mama da Ashrof sun tafi dan yau babu damar yin girki ko wani abu da gabaɗaya Ashrof a ruɗe take har lokacin tana zabura. Hajiya da ke yiwa Sadiya sallama ta kalli Imran da ya fito riƙi-riƙi da jaka. Kowa da mamaki yake kallonsa Hajiya ce ta yi ƙarfin halin cewa.

"Ina zaka da kaya haka Imran?"

"Tare za mu tafi"

"Tare za ku tafi da wa?"

"Da ke"

"Ina?"

"Gida mana , kawai tafiya zan yi can in zauna a tsohon ɗakina tun da ga Inna nan ta zo ZAMAN WANKA in ya so ta zauna ma har Sadiya ta yaye yaran" Ya faɗa yana sunkuyar da kai, dan kunyar Sadiya yake ji sun haifi ɗan amma yana so ya gudu, shi kuma har ga Allah so yake ya tafi dan ya gaji da darun gidan kuma dai ya ga alama Hassan ya ƙi dawo wa mutum.

" Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Taɓɗiiii, ashe kuwa za a yita a gidan nan, wane shegen ne zai zauna bayan kai ma uban micijin gudunsa kake, wato ga Inna kuka me daɗin hawa, wacce take so ta bar duniya a kwana kusa sai in zauna in maka ZAMAN WANKA, yo ai abin ma ya wuce ZAMAN WANKA ya koma reno wai har a yaye su in ya so idan micijin ma ya sareni baka da asara iyakarta idan na mutu a ZAMAN MAKOKI ka ce Allah jiƙan Inna, ana karɓar sadaka kana afa shinkafa kana kora lemo, haɗe da kunun zaƙi, to wallahi baka isa ba ko tsinke naka ba zai fita daga gidan nan ba" Cewar Inna da ta tashi ta kama tsantsa ta wani haƙiƙice ta rufe ido tana sababi..

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

3️🅰️➡️🅱️

Kowa da kallo ya bi Inna ganin yadda ta haƙiƙice tana sababi kamar dai za ta hau Imran da duka.

"To kai Imran ban da abinka ya za a yi kana namiji kuma me gida ka ce za ka fice ka bar gida, ina ka taɓa ji an yi wannan sha'ani?" Hajiya ta faɗa tana kallonsa.

"Dan Allah Inna ki yi haƙuri kin san sha'anin yara sai a hankali amma babu inda zai je ma in sha Allah yana nan" Cewar Hajiya tana kallon Imran da ya tamke fuska ita dai Sadiya bata ce komai ba sannan ko a cikin ranta bata ji haushin Imran ba dan tana ganin kowa ma zai iya yin haka duk da kasancewarsa mahaifi a wajen Hassan bai kamata ya yi hakan ba amma dama ta san Hajiya ba za ta barshi ya bita ba ko ya bar gidan.

"Haba Amina ai duk da ba zan haɗa kaina da Imirana a wajen shekaru ba, to kuwa tabbas ba ƙaramin yaro bane, mutumin da yake da aure garsamemen ƙato da shi har da ƙaruwar ƴaƴa biyu duka maza duk da dai ɗayan miciji mutum ne, wato rabi da rabi, kuma ma ai yana saka ƙafa ya bar gidan nan ni ma jikata zan ɗauka da Husaini na aika miki Hassan ɗin in tafi da ita can wajena, ya za a yi ma ya mata ciki ta haife masa amma saboda yaro na da baiwar da yake sanya kowa a taitayinsa ya ce wani zai bar gidan" Ta faɗa tana galla masa wata hararar.

"Ki yi haƙuri Inna" Cewar Hajiya tana mamakin halin Inna da bata iya sakaya abu ita babu ruwanta da kowa duk abin da ta yi niyyar faɗa, to faɗa take ba ruwanta d me zai je ya zo ko kuma ya wanda aka faɗawa zai ji.

"Kar ma ki kai kan ki da nisa na haƙura ma ba dai ba zai tafi ba ai ni bani da ɓacin rai indai zai zauna ɓacin raina a ce ya tafi ya bar Sadiya da ni da Hassan shi ne kawai" Ta faɗa fuskarta fes da alamun dariya, tana ɗan yi tana kallon Imran da zuwa lokacin ya cika fam babu masakar tsinke, ji yake kamar ya hau Inna da duka amma babu hali, nasiha sosai Hajiya ta musu shi da Sadiya a kansu rungumi ƙaddara Inna tana gefe tana tattaɓe baki haka dai Hajiya ta musu sallama ta kama hanyarta ta tafi.

Inna da ke ƙunshe dariyarta ta kalli Imran da ya tashi ɗauke da jakarsa yana wani harare- harare ya yi cikin ɗaki. Dariya Inna ta kyalkyale da ita ta ce.

"Oh ni Azumi Imirana manyan ƙasa ina ga nan gaba duka za ka fara hawan mutane da shi yo Allah na tuba, wannan haloƙoƙon da kake na menene zama dai daram a gidan nan, kuma kai ma muna nan tare da kai"

Shi dai bai ce mata komai ba ya shige É—aki wata Æ´ar dariyar ta yi ta ce

"Ni dai ban san ba harara sai ido ya faÉ—o" Ta faÉ—a tana kallon Sadiya da ke zaune kawai tana binta da ido.

"Sannu ƴar jikallena, Halimatus Sadiya, yo dole a miki sannu irin wannan ruwan hawaye, ke baki da aiki sai kuka daga kin ga Hassan ya zama miciji ko kuma ana ta tseran gudun famfalaƙi memakon ke ma ki rattaba naki gudun sai ki zauna kina kuka, ai har idanunki sa ke miki ciwo" Ta faɗa idanunta a kan Sadiya da bata ce komai ba.

"To ai shikenan, tun da ba za ki yi magana ba na lura kin gama ɗauke halayen wancan kurman mijin naki Imirana, duk da dai na kula zuwana gidan nan ya sa ya yi baki amma dai da sauran rina a kaba, bari in tashi in je in sake alwala, yo ɗazu ina alwalar na zo wankin fuska na ga yaran nan sun fito a guje, da faɗa zan fara musu amma ganin Hassan ya fito ya sa ni ma na ce ƙafa me na ci ban baki ba, wallahi haka nan na bar yin alwalar na gudu na samu mafaka a firinji amma yarinyar nan me ƙunshi wacce na yiwa yaɓe da lalle ta garƙameni a firinjin ta kunna shi a haka na daskare kamar ƙanƙara" Ta faɗa kamar ta saki kuka da ta tuno da wahalar da ta sha lokacin da ta tsinci kanta a freezer.

Ganin dai Sadiyar bata sake cewa komai ba sai binta da ido take ya sa ta ce.

"Ni fa wallahi Sa'adiyya da a ce ba ni na haifi ubanki ba da babu dalilin da zai sa in kasa yarda ke mayya bace, ko da kuwa baki ci mutum ba, yo ina dalili ki yi ta kallon mutane ba ƙaƙƙautawa ina ga ma ko ƙiftawa bakya yi" Ta ce tana hararar Sadiya da ta ɗauke kanta daga kallon Innar jin abin da ta ce.

"Oh to bari na tashi da wannan in je in yi abin da zai fishsheni, ana zaune ana darun gudu ba azahar ba la'asar" Ta faɗa tana tashi ta fita waje dan yin alwala. Tana zuwa wurin alwala ta ƙyalƙyale da dariya ganin butar da ta bi ta kanta lokacin da za ta gudu da ta ga Hassan ya fito daga ɗaki.

"Allahu akbar kabiran, Allah sarki ni Azumi na haɗu da gararin rayuwa, kalli yadda na yi ƙwallo da butar nan a gudun ceton rai, garin gudu kaɗan zani na ya faɗi in je in yi tsirara a gaban jama'a a shiga uku, dan ma dai lokacin kowa ta kai ta kai yake kamar a filin ƙiyama, ba lallai su gani ba" Ta faɗa tana ɗaukan murfin butar tare da butar ta zuba wani ruwan ta sake shiga bayi ta fito ta zauna tana yin alwalar.
Chapter 13 · 0% Book details