← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gwara ke nono aka damƙa, wayyo ɗuwawuna za a cire min fatar" Ta faɗa jin an ƙara cafka da haƙori dan tana sakin tusa ita kuma ta ƙasanta ke gatsara mata cizo.

Inna da ke cikin freezer ta ƙyalƙyale da dariya duk da halin da take ciki, amma jin ana damƙe-damƙen ɗuwawu da nono sai abin ya bata dariya ta ce a zuciyarta

"Yau dai ana dara ga kuma dare ya yi, Hassan duk ya rabawa kowa aikin wahala"

Me ƙunshi ma kukan da take ne ya haɗe da dariya a ranta ta ce.

"Taɓɗi yau da a ce ba a halin ƙaƙanikayi nake ba dariyar da zan yi sai cikina ya yi ciwo, dan ko ni lokacin da na fara ƙirgen dangi ko wanka na zo sai dai in zuba musu ruwa in ɗauraye su, ba na yarda in sa soso in wanke saboda azaba" Ta faɗa tana dariyar da ta kusa fitowa fili saboda yadda dariyar ke cinta.

"Inna! Inna!! Inna!!!" Inna ta jiyo muryar Sadiya tana ƙwala mata kira tun ƙarfi.

"Inna dan Allah ki fito ki tayani mu dawo da Hassan gashi can ya kama hanyar ƙofar gida zai fice kuma ƙofar ba a rufe take ba, ni kaɗai ba zan iya ba dan ya ƙi tsayawa ko ɗaukansa zanyi zulalewa yake" Cewar Sadiya tana kuka ta rasa yadda za ta yi hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, bata so ɗan nata ya fice duk da kasancewarsa a siffar muciji tana ƙaunarsa, Allah sarki uwa!

"Mtssss" Inna ta ja wani dogon tsaki ta ce.

"Banza ta kori wofi ma kenan yo Allah na tuba da ba a cikin firinjin nan nake ba ma babu abin da zai sa na zo wallahi, da kaina zan kaɗashi ya tafi, gwara ma ya je ya fice abinsa wataƙila ma wahalarki ce ta yanke, yo Allah na tuba zama da wannan abu a gida ai jafa'i ne, ya je can daji ya samu ruwa ƴan ruwa su ja abinsu mu huta, ga Husaini nan ya isa" Ta faɗa tana ɗaɗɗaga kai take kallon saman freezer.

"Dan Allah ku taimaka mini" Cewar Sadiya tana É—aga murya.

Ashrof tausayin Æ´ar uwarta ya kamata amma ga kuma tsoro tana ganin kamar micijin zai iya cutar da ita, amma ita Sadiyar ba lallai ya cutar da ita ba saboda ita ce mahaifiyarsa.

"Ke dalla ɗaga ni kin wani min ɗirkaka a kaina kamar wani buhun hatsi" Ƴan cikin loka ke faɗa saboda sun ji an ce miciji ya kama hanyar fita waje.

"Kan ku ake ji wai mahaukaci ya faÉ—a rijiya ya ce ni wankana nake "Cewar Inna.

"Ƴan cikin kicin ga Hassan nan ya nufo kicin" Sadiya da ta shawo gaban Hassan daga hanyar gida ya iyo kwana ya dawo gida ta faɗa cikin ɗaga murya ganin gadan -gadan ya nufi kicin ɗin.

Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa ta taimakawa Sadiya ta dakata daga ƙoƙarin fitowa daga bayi jin Sadiya ta ce ya nufi kicin.

"Hahahaa na dawo in ji ɗan yawon duniya, yau akwai gwarama" Cewar Inna tana dariya ido na zubar da ruwan hanci ku sai tsiyaya yake kamar an kunna fanfo tsabar sanyin freezer da take shaƙa.

GabaÉ—aya masu faÉ—a a cikin loka sai suka sha jinin jikin su ko kyakkyawan motsi sun kasa yi, kowa bakinsa sai motsi yake alamar addu'a.

Sai da ya je tsakiyar kicin ɗin ya ja ya tsaya tare da fasa kai alamar sara, Sadiya da ke tsaye a bakin ƙofar sai kallonsa take so take ta koma ɗaki ta ɗauki wayarta ta kira Imran amma bata so ta matsa daga wurin wani abu ya faru kuma ma ta san shi ma Imran tsoron Hassan ɗin yake ji idan ya sawaya.

"Kar wanda ya motsa daga inda yake Hassan yana tsakiyar cikin kicin É—in" Cewar Sadiya cikin muryar kuka.

Ɗif kowa ya yi, me ƙunshi kwa da ta buɗe idonta guda ɗaya ta ɗan leƙo daga cikin buhun da ta lulluɓa da shi. Ganin micijin danƙarere ya fasa kai da alama sara kawai yake son yi, gashi kuma ta san babu wanda zai fi saurin gani sama da ita, a take ta ji ina ma ita ce a cikin freezer kuma freezer a buɗe a kan wannan tashin hankali da take ciki.

Bum-bum ƙaran bugun freezer da Inna take ya karaɗe wajen, duk bugu ɗaya sai micijin ya zabura, zaburarsa kuma ba ƙaramin ƙara razana me ƙunshi take ba, Inna kuma dama da niyya take bugawa saboda ko banza ta san ta rama kaɗan daga abin da yarinyar ta mata.

"Wayyo wannan tsohuwa masifarta ta yi yawa, yanzu sai ta firgita micijin nan ya shiga neman mutumin da zai sara a cikin kicin ɗin, tsoratar da yake yana wata girgiza yana fasa kai ta ko ina hakan ba ƙaramin tsurewa ya sanya me ƙunshi ta yi dan ita kaɗan ke ganinsa na cikin loka da Inna da ke freezer ra san ba za su gani ba.

Shigowar Imran gidan ɗauke da sallama shi ya sanya Sadiya nufarsa da sauri tana kuka tana faɗa masa, wani yawu ya haɗiye muƙut jin wai micijin har ya fara fitowa ya yi waricinsa a cikin gidan lallai babar magana . Haka dai ya daure tare da majewa ya nufi kicin ɗin, a haka ya sanya Sadiya ɗaukan micijin ta nufi ɗaki da shi har lokacin kuka take yi. Imran ganin matan nan na cikin loka ya ɓata mas rai ganinsu cunkushe kamar alhazai ranar arfa, wata da take leƙo idonta ta tsakanin murfin lokar ita ya dakawa wata uwar hararar da ta sanya ta runtse idanu, ƙafa ya sanya ya daki jikin lokar tare da cewa su fito haka, haka suka turo murfin suka fito simi-simi suna ciccira idanu kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya.Suna fitowa daga kicin ɗin ya tsaya a bakin ƙofar yana binsu da wani mugun kallo dan daga me zarnin fitsari sai wani wari da ya kasa gane na menene.

Me ƙunshi da ke ƙunshe cikin buhu ta buɗe a hankali ta fito daga ckn buhun, da ta lulluɓa, tana fitowa ta kalli freezer a ranta ta ce

"Ke kuma tsohuwa a nan za ki kwana uwar sababin tsiya" Tana zuwa za ta fito ta ga Imran ya yi bake-bake a bakin ƙofar aikuwa ta yi ƙoƙarin bin ta ƴar sauran ƙofar da ya bari, Imran da bai san da sauran mutum a cikin kicin ba sai ji ya yi an ɗan shafi gefen rigarsa aikuwa dama duk a tsorace yake, jin an ɗan taɓa shi sai ya yi zaton micijin ne dan jin an ce micijin da kansa ya fito abin ya matuƙar bashi tsoro sai dai bai faɗa bane. Da gudu ya ruga a sukwane ya nufi ɗaki, sauran matan da suka fito daga loka suka mara masa baya dan duk tunninsu wani abun ne.

Yadda ya zuro a guje babu birki haka su ma suka daddage ƙarfinsu suke binsa da gudun, har da masu tattare zane gudun samun mushkila. Imran da gabaɗaya a gigice yake sai da ya zo falo ya ga Sadiya da miciji a hannu ya ja ya tsaya a ransa yana ganin jarumta irin ta Sadiya yana kuma jaddada soyayyar uwa da ɗa, ganin Hassan ɗin ne ya dawo dashi daga firgici da tsurewar da ya yi sai a sannna ya tuna cewar ashe ma Sadiya ta taho da yaron kawai tsoro ne ya sanya ya ga kamar micijin ne ya biyo shi. Wani yawu ya haɗiye tare da sauke wani numfashi. Matan nan ma ganin ya tsaya sai kowacce ta dakata a wajen dan sun manta da micijin a ɗaki amma ganin Imran na gudu su ma suka fara suna jejjefa idanu kallonsu kawai yake, daga wacce take jige jagaf da fitsari sai wacce ke da ƙunshi ƙafa ɗaya ba a ƙarasa ɗayar ba, sai wacce baƙin lalle ya gogu a fuskar ta koma kamar wacce ta shafa shuni. Wata harara ya musu tare da jan wani uban tsaki, ya wani maje yana harare-harare amma ya kasa shiga ɗakin, hango me ƙunshi a ƙofar kicin ɗin sai lokacin ya ga rashin azancinsa da bai tsaya ya waiwaya ba bare ya gane ba miciji bane.

Harara ya dakawa matan nan da suka biyo shi, dan sun ma kasa shiga falon shi ma cikin wayancewa sai ya juya ya nufi kicin ɗin me ƙunshin da gudu ta bar wajan ganinsa ya taho. Imra n kuwa na shiga kicin ɗin sai ya tsaya a tsakiyar kicin ɗin yana maida numfashi dan ba ya so a raina shi shi yasa bai tsaya maida numfashi a gabansu ba, su ma suna nan tsaye sun yi carko-carko. Dafa kan freezer ya yi tare da ɗora kansa a kanta, Idanu ya rufe ruf yana jin yadda zuciyarsa ke lugude kamar me tseren gudu, hannayensa duka biyu ya ɗora a kan freezer sai ya kwantar da kansa a kan freezer, idanunsa a rufe yana tunano yadda Sadiya ke ɗauke da miciji a hannunta, Inna da tun daɗewa take ta faman magana a kan a kawo mata ɗauki babu wanda ya jiyo ta, dan haka ta raya a ranta za ta shiga jijjiga freezer da ƙarfi dan a jiyo ta a zo a buɗe ta. Wata jijjiga da ta yiwa freezer da Imran ke riƙe da ita gam, hakan ya sanya ya saki wata tusa ta tsurewa ba tare sa ya shirya ba, jin freezer na girgizashi tamkar ana girgizar ƙasa hakan ya sanya ya ƙanƙameta da ƙarfinsa.

Dan gabaÉ—aya ma sai tunanin guduwa ya kwance masa.

"Allah wannan baƙar wahalar da nake shiga tun ranar da Sadiya ta haihu Allah ka sa kaffara ne" Ya faɗa lokacin da ya saki wani kuka me cin rai Inna kuwa bata daina jijjiga a cikin freezer ba yi take tun ƙarfi.

"Ai wallahi da in mutu a binne ni a tsugunne na gwammace in daddara firinjin nan in bayyana kamar wata ɗan daren goma sha huɗu" Ta faɗa tana lokacin da ta kai hannunt ta ƙwarzani jikin freezer ganin yadda farin ƙanƙarar nan me kamar dusa ta fara baibaiye jikin freezer.
Chapter 4 · 0% Book details