Sashe 14
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imran tun da ya shiga ɗaki yake jin wani ƙululun baƙinciki ya tokare masa ya ƙi gaba ya ƙi baya, takaicin abubuwan da Inna take masa kaɗai ya ishe sa musamman yau da ta balbala masa wuta har da sanya buhu kamar ta samu ganda ko naman kai. Baki ya cije a ransa yana raya sai ya rama abin da ta masa in bata gaji ba shi ma ba zai fasa ba an ringa yi kenan, sai dai ramuwar gayya ta fi ta gayya zafi.Tasowa ya yi domin ya fito ya je ya yi alwala dan bai yi sallar ka'asar ba, dama daga masallacin azahar ya shigo gidan ya tarar da abin da ke faruwa.
Yana zuwa falo ya kalli Sadiya cikin jin tausayinta ya ƙarasa kusa da ita ya kama hannunta cikin taushin murya ya ce.
"Ki yi haƙuri Sadiya komai ya yi farko yana da ƙarshe, duk abubuwan nan da kike gani jarabawa ce akwai ranar da za ta wuce komai ya zama tarihi kamar ba a yi ba" Ya faɗa yana rausayar da kai idanunsa cikin nata.
Hannunta da ya riƙe ta sanya ɗayan hannun da bai riƙe ba ta ɗora a kan hannun nasa da ke riƴe da hannunta, ta ɗan damƙe hannun tana kallon cikin ƙwayar idanunsa, tana jin yadda soyayyarsa ke huda kowane kungu da saƙo na zuciyarta a gefe ɗaya kuma wani tausayinsa ne ya mata dirar mikiyar da har sai da idanunta suka kawo ƙwalla, Allah sarki so, so hana ganin laifi in ji masoya.
"Babu komai masoyina na san komai dama muƙaddari ne amma kai ma ka daina sanya damuwar hakan a ranka kamar yadda ka umarce ni na daina, sheɗan ne ke maka jagora har yake neman nisanta ka da iyalinka"
"Allah sarki Sadiya nagode ƙwarai kuma ina ƙara yiwa Allah godiya ya azurtani da mace ta gari wacce ta san damuwata da kuma farincikina wacce ta san samu na da kuma rashina in sha Allah zan kiyaye tare da ƙoƙarin yaƙi da shaiɗan waje ganin bai cimma burinsa a kaina ba ya samu nasara" Ya faɗa yana sanya hannu ya shafo gefen fuskarta suka sakarwa juna murmushi a lokaci guda kowa ya ji zuciyarsa fes damuwarsa ta wanke, domin kowacce zuciya tana son lallashi da kuma samun jin ƙai daga abokin tarayyarta.
"Ni ma nagode kuma ina alfahri da samunka matsayin mijina kuma uban Æ´aÆ´ana" Ta faÉ—a ita ma tana É—auke hannun da ta É—ora a kan hannunsa ta shafo fuskarsa kamar yadda ya mata.
"I luv u" Ya faÉ—a yana mata wani kallo da ita kaÉ—ai ta san ma'anarsa.
"I luv u too" Ta faÉ—a ita ma tana sakar masa murmushi mai ratsa zuciya.
Haka ya tashi domin zuwa ya yi alwala har ya kai Æ™ofa ya dawo ya buÉ—e frige É—in falon ayaba ya É—akko guda É—aya. Æarewa ya yi ya cinye Sadiya dai tana kallonsa sai da ya cinye ya fira riÆ™e da É“awon a hannunsa yana zuwa kan barandar Æ™ofar falon ya faki idon Inna ya jefar da É“awon. Zuwa ya yi zai shige bayin ta kallesa tana É“oye dariyarta ta ce.
"Imirana na cikin tukunyar wankan jego, an sha zafin wuta" Banza ya mata ya shige bayi, har ta kammla alwalarta ta bar wajen, tana tafiya tana kallon tsakar gidan abubuwan da suka faru yau a tsakar gidan na faɗo mata tana ɗan murmushi, aikuwa tana cire takalmanta ta taka barandar ta sauke ƙafarta a kan ɓawon ayabar da Imran ya jefar, gabaɗaya ta tafi luuuu tana rafka uban salati ƙafar ɗaya ta yi gabas ɗayar ta yi yamma ji kake timmm ta rafku da ƙasa, Imran da ke laɓe yana leƙe ta bayi ta koma cikin yana shan dariya abinsa. Sadiya da gudu ta fito domin ganin me ke faruwa.
"Taimaka min Halima wallahi kamar wanda na yi hatsarin mota, motar ta yi sama da ni haka na ji"
Cikin tausayawa Sadiya ta shiga ƙoƙarin ɗaga Inna, hammatarta ta kama tana ƙoƙarin ɗaga ta.
"Sannu Inna da na ga ba da hammatar kika faÉ—i ba shi yasa ma na kama nan É—in sa...
"Haba Sa'adiyya yo a yi zancen ma ba da hammata na faÉ—i ba, to billahil lazi ko ina na jikina ciwo yake, bakya ganin jikin tsufa ne dama kamar jira jikin yake in faÉ—i ko ina na jikina sai da ya amsa hatta gashin kaina ban É—auke ba, har tsakar kaina amsawa yake" Inna ta katse Sadiya daga maganar da take son faÉ—a.
"Yanzu ina zan kama?"
"Kama ƙuguna daga gefen dama ki ɗaga ni"
"Haba Inna ta ya zan iya ɗaga ki kuma ta ƙugu, ni fa dama taimaka miki zan yi ki tashi amma ai kinsan dai ba zan iya ɗaga ki ba"
"Wato ga buhun gero, ai da uwaki Rakiya ce da tuni kin sunkuce ta kamar kin É—auki auduga, amma da yake ni ce cewa kike nauyi gareni" Ta faÉ—a tana sakin kuka.
Imran da ke laɓe daga bayi yana leƙensu sai dariya yake ƙasa-ƙasa ko banza ya rama abin da ta masa.
Haka Sadiya ta yi dibara ta taimaka mata ta shiga da ita falon tana ta sababin wane shegen ne ya jefar da ɓawon ayaba a kan hanya. Sai da Sadiya ta zaunar da ita a kan kujera sannan ta ce.
"Inna ba fa cikin sani aka jefar da ɓawon nan ba, Abban twins ne fa yanzu ya ci ayaba shi ne da zai fita yin alwala ya fita da shi a hannunsa to ina jin bai san ya jefar ba ma, kin san shi dai da tsafta babu abin da zai sa ya jefar da abu a ƙofar falo dan...
"Ni kwa na san shi da tsafta, kuma na san shi da mugunta" Ta faÉ—a a zuciyarta a fili kuma ta ce.
"Guda nawa ya ci ayabar?" Inna da tun da Sadiya ta fara magana take kallonta da baki sake tana son gano wani abu ta jefa mata tambayar.
"Kamar ya guda nawa ya ci kuma Inna sai ka ce ayabar ajiya ko ta haram sai an tamabayi mutum nawa ya ci"
"Ke ba na son iskancin wofi ki bani amsar tambayata"
"Guda É—aya ce fa ya É—akko ya ci"
"ÆŠaya tak?"
"Eh"
"Tabbas Imirana da gangan ya jefar da ɓawon nan dan in taka in faɗi amma kuma da Azumi yake magana indai ni ce mu zuba ɗan halak ka fasa"Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
"Allah sarki Imirana kam akwai tsabta, bai san ya jefar ba" Ta faÉ—a tana sanya hannu ta dafe bayanta tare da yatsina fuska ta ce.
"Bayan nan nawa yadda kika san an yi yaƙi a kansa haka nake ji yana sara min wallahi ko ina ma ciwo yake"
"Bari in ɗakko miki aboniki ki shafa" Cewar Sadiya ta shige bedroom sai gata ta dawo riƙe da abonikin. Haka ta shiga shafawa Inna a ƙafafunta hatta kafaɗunta da wuyanta sai da aka lafta abonikin, tana ta rakin ciwo-ciwo.
"Bani in shafa a kwankwasona da haƙarƙarina" Ta faɗa tana karɓa ta shiga shafawa tana yatsina fuska.
"Sannu Inna"
"Yawwa Halima, ni wallahi wannan ba mini zai yi ba, ku nan ba a siyar da wasai?"
"Inna meye wasai kuma?"
"Ke dalla rufe min baki, yanzu wasan ne baki sani ba, mu a can akwai wani me siyar da maganin hausa, me suna wasai, za ki ji yana talla yana cewa, sai na ji wasai in baka wasai, to da wannan maganin na samu da tuni na ji wasai"
"Gaskiya ni ban ma taɓa jin sunan ba"
Shiru Inna ta yi ita kaÉ—ai ta san me take ji a jikinta.
"Inna ki yi sallar mana"
"Haba Sa'adiyya ke ma tun da kika ga bam tashi ba ai kin san akwai magana ya za a yi ma in ƙi yin sallah da gangan bayan dama na san salloli biyu ne , a kaina ai sai dai Allah gafarta mana" Ta faɗa tana yin dibara ta sakko ƙasa ta dafe hannunta a ƙasa tana durƙushe. Imran kuwa dama tun da ya yi alwala ya fice daga gidan ya tafi masallaci duk da ba jam'i zai samu ba tun da an daɗe da idar da sallar, ransa fari ƙal ya rama abin da Inna ta masa.
"Tsohuwa sai dai ki yi haƙuri kin haɗu da mijin jika ɗan zamani, dan dai dama ke ma ba a barki a baya ba" Ya faɗa yana tafiya ya ƙyalƙyale da dariya.
"Inna ya kika durƙusa kuma?" Sadiya ta tambaya da mamaki.
"Bari ke dai Sa'adiyya kwankwason nan nawa ne nake ji kamar ba a jikina yake ba, wallahi yadda kika san mace tana naƙuda take jin mararta kamar ba tata ba, tsantsarta kamar za ta ɓalle to haka nake ji"
"Me naƙuda kuma Inna?"
"Yo me naƙuda mana, ai wai na miki misali ne da yadda za ki gane, tun da baki daɗe da haihuwa ba na san baki manta yanayin da kika ji ba"
"Allah sarki sannu Inna zai daina in sha Allahu"
"Kayya Sa'adiyya baki ga na tashi daga zaune ba yo mazaunan nawa ne nake jin suna wani mamar-mamar sun ƙi zaunuwa dai dai ko za ki samu abu ki bubbuga mini su ɗan lafa in yi sallar ko da a zaune ne" Ta faɗa cikin murya kamar ta yi kuka.
" Buga mazaune kuma Inna?"
"Ke in ba za ki buga mini ba ƙyale ni, sai ka ce wani abu yo Allah ma tuba ma in ba larura ba mai zai sa in ce ki bubbuga min mazaunai,ai tun da na haifa miki ubanki na gama miki komai" Ta faɗa tana sababi. Ita dai Sadiya bata ce komai ba kuma bata buga mata ba, haka ta gaji da durƙuson da ya lafa mata ta yi sallar a zaune, tana idar wa ganin ta ji dama-dama kuma ta gama shirya abin da za ta yiwa Imran dan gabaɗaya ta gama gano da gangan ya jefar da ɓawon, dan ko bayan da ya dawo daga masallacin da Sadiya ke faɗa masa Innar ta faɗi lokacin yana bayi, dakyar ya iya danne dariyarsa kuma ya mata sannu kuma bai san cewa duk abin da yake Innar tana ankare da shi ba. Yana shigewa ɗaki ta ce.