← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 35

Sashe 32

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai ta cigaba da shirinta ta shirya tsaf ta shafa turare ta ajiye bokitin da ta zuba fura a ciki da galan É—in nonon da za ta kai gidan sunan. Tana gamawa lokacin Malam ya shiga É—akinsa ta fito ta galgala wuta ta É—ora É—umamen tuwo, tana É—orawa kuwa ta barshi kafin ya yi zafi ta tafi gidan Tsahare tun daga nesa ta fara hango Tsahare tana haÉ—a kan ita ce a murhu ko wanka bata yi ba wani takaici ne ya cikata tana ji a ranta dama da a ce ta san birnij nan da tafiyarta za ta yi in ya so ita Tsaharen ta taho daga baya, dan ta ga aminiyarta ce Azumin shi yasa take mata wani jan aji.

Da sallama ta ƙaraso a bakinta kana kallon fuskarta za ka fahimci cewa ranta a ɓace yake. Amsa mata sallamar Tsahare ta yi ta ɗago daga sunkuyen da take tana ƙarewa Tasalla kalko. Babu inda ya ɗauki hankalinta haɗe da bata mamaki irin bakin Tasalla da ya sha jambaki gashi ta zana jagira da kwalli sai ka ce wata ƙaramar yarinya.

"Haba Tsahare wai ma baki shirya ba kuma na ga kina ƙoƙarin haɗa wuta ga wani ƙullin ƙosai a gefe in ce dai wata za ki barwa ta soya miki" Tasalla ta katsewa Tsahare tunanin mamakin da take na mai ya kai jambaki bakin Tasalla har da su jagira da girmanta da komai.

"Wai kamar ya wace irin magana kike haka, kawai dan zan tafi suna sai in kasa yin sana'ata shin kin manta ba a ƙafa za mu je ba kuɗin mota za mu biya daga nan ma zuwa tasha sai mun biya kuɗin machine, a can ma in an sauke mu sai mun hau adaidaita sahu, ga kuɗin gudunmuwa mutum ba ya je baƙiƙƙirin ba" Ta faɗa tana kallon ƙafar Tasalla da ta sha wani uban vasiline sanye da takalmi ɗan madina kore.

"Haba Tsahare yanzu dan wannan ne zaki yi sana'a yau so kike sai shinkafar da za a dafa ta suna ta ƙare bamu je ba gaskiya dai baki kyauta ba"

"Dan Allah ki rabu dani da wani zancen shinkafa yunwa za mu je, da za a ke tunanin shinkafar rabo, duk wannan abin da kike fa har yanzu a ƙarfe bakwai saura ake dan Allah ki koma gida duka ƙullin ma na kwano guda ne yanxu zan gama kinsan dai na kwano uku da rabi nake yi kullum"

"To ai shikenan ya na iya da abin da ya fi ƙarfina ni da ko hanyar ban sani ba ai dole na jira ki" Cewar Tasalla tana taɓe baki ta juya ta tafi.

Da kallo kawai Tsahare ta bi bayanta tana mamakin irin kwalliyar yaran da ta yi a fuskarta, gashi har yanxu ta kasa daina mamakin wai Azumi ce ya gayyaci Tasalla suna, dan ta san dai basa ga miciji da juna.

Sai wajen ƙarfe tara suka baro ƙauyen, zuwa lokacin sawun Tasalla ya fi biyar gidan Tsahare a kan ta yi ta shirya su tafi ƙarshe dai sai da suka yi faɗa a haka dai suka samu mashinan da suka kai su Garki L.G inda suka samu motar Kano suka hau. Tun da aka fara tafiya bakin Tasalla bai rufu ba ta ce wannan ta ce wancan tun Tsahare na biya ta har ta gaji ta yi shiru dan ta ga abin nata ba na ƙare bane, kuma kamar ma duk murna da zazzaɗin zuwa birnin ne ya sanya bakinta ya ƙi rufuwa. Tun da motar ta shigo garin Kano ta dabo tunbin giwa sai kuma gabaɗaya Tasalla ta ruɗe bakinta ko rufuwa ba ya yi ta sake shi galala saboda kallon motoci da kuma gine-gine kai ba ma su kaɗai ba hatta mutanen da ta gani masu yawa kowa yana harkar gabansa suj zame mata TV saboda ita bata taɓa zuwa gari kamar Kano ba iyakacinta ƙauyukan wajejensu kawai.
Tsahare da ta É—auke kanta ta mayar gefe daga kallon Tasalla saboda nune -nune abubuwa da ta dame ta da su, ta ji Tasalla ta saki kuka cikin sauri ta waiwayo wajenta take tambayarta dalili dan har lokacin fa basu sauka daga mota ba kawai dai sun shigo garin Kano ne, motar tana tafiya zuwa tasha ne dan ta sauke lodi.

"Dole na yi kuka Tsahare wallahi dole na yi kuka, kawai ki barni kar ma ki baiwa kan ki wahala wajen lallashina dan ba shiru ba zan yi sai na yi mai isata na ji zuciyata ta yi sanyi"

"To ikon Allah" Cewar wasu daga cikin motar da suka haÉ—a baki wajen faÉ—a.

"Haba ke kuwa baiwar Allah ana zaune ƙalaw muna murna Allah ya kawo mu lafiya saura mu sauka, kawai za ki fashe da kuka kuma ki ce wai ba za ki saurara ba sai ka ce wata ƙaramar yarinya, kuma mu babu wanda ya ga kin ɗaga waya bare a ce ko mutuwa aka faɗa miki" Cewar wani mutum da ke gefe.

"Wallahi bawan Allah ba mutuwa aka faɗa mini ba, kawai takaici ne na abin da ka mini, ni nan da kake gani ina da shanaye da dabobi da nake kiwo ina dai da abin hannuna amma a ce a duniya akwai gari ya Kano amma ban taɓa zuwa ba? Kuma ko bani da kowa a Kano wallahi da na san haka take da ko iya tasha ne na biya kuɗi na zo na ga gari na koma amma aka barni a can ƙauye a garƙame, kuma dan baƙin hali irin na kishiyata, bata taɓa gayyata ta garin nan ba wajen ƴan uwanta ai ko, dan na kashe ƙwarƙwatar idona a faɗa min Kano haka take"

GabaÉ—aya motar dariya aka kwashe da ita kowa yana jin abin da Tasalla ke faÉ—a sai ya yi dariya, abin nasu sai ya sosa mata rai dan haka ta É—auke kan ta gefe ta cigaba da baiwa idonta nama. Kowa ya fita daga motar Tasalla kuwa tun da ta fito sai idanunta suka kasa samun matsaya ta kalli can ta kalli nan, da yake bakin titi aka sauke su a tashar ba a shiga cikin tasha ba. Sosai Tsahare ta yi da na sanin zuwa da Tasalla saboda babu abin d take sai kalle-kalle, a haka dai ta samu dakyar ta tsayar musu da É—an sahu suka shiga suka nufi gidan suna murna fal cikin Tasalla dan har lokacin ma a É—an sahun kalle-kalle take.

"Taɓɗi shi yasa ashe ake cewa hankali shi ne gani wai wani ya je Kano bai ga mota ba, yo in ba haka irin motocin nan na garin Kano kwantsam kamar jamfa a jos duk da ban taɓa zuwa Jos ɗin ba, amma gaskiya yawan motocin Kano ya ɓaci yadda ka san ba mutane kaɗai ke hawa motocin ba har da aljannu" Cewar Tasalla da ke ta kalle -kalle. Daga Tsahare har ɗan sahun babu wanda ya tanka mata a haka suka cigaba da tafiya.

A daidai ƙofar gidan aka sauke su, suna sauka sai Tsahare t tsaya tana baiwa ɗan sahun kuɗinsa, Tasalla kwa dama ta biya shi, dan haka sai ta ɗan tsaya daga gefe take jiranta kusa da wasu mata guda biyu da ke ƙusƙus.

"Wallahi fa nake faɗa miki miciji sak Hassan ɗin ke zama ya yi ta firgita mutane, in kika ji irin uƙubar da mutanen gidan ke fuskanta za ki yi mamaki" Cewar ɗaya daga cikin matan da ke tsaye gefe, Tasalla da ke saurarensu cikinta ne ya bada wani ƙululuuuu ta fara zare ido a take ta ji gabaɗaya Kanon ma ta ginsheta ji take kamar ma kar ta shiga gidan.

"Ikon Allah shi kuma irin tashi baiwar kenan, to gaskiya dole mutane suke tsorata yo ina kai ina miciji"

"Himm ke dai bari kuma fa a haka suke kwana da shi É—aki É—aya har kakar mai jego kin jo sunanta Inna Azumi"

Ai sunan Azumi da aka ambata shi ya ƙara tabbatarwa Tasalla da jariran ƴan biyun da suka zo sunan ake.

"Mu je mana ga gidan fa kina gani mutane sai shige da fita suke ni wallahi na ƙosa na sanya amini a idanuna " Cewar Tsahare tana kallon Tasalla da gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalaw kamar dai ba ita ce ta ishi mutane da surutu ba ɗazu.
"Kai ai ni unguwar ce duk sai na ji kaina yaba juyawa da alama mutanen ɓoye na ne ke son tashi shi yasa, idan kika sa ni a ɗan sahu za su maida ni tashar mota in koma gida" Cewar Tasalla dan duk son da take yiwa birni gabaɗaya ya fice mata a rai dan gabaɗaya hanjin cikinta ya hautsina.

"Ki koma gida kuma garin yaya wato sai da kika zo har ƙofar gida sannan tsoron mai zai je ya dawo ya zo miki, ai ni dama na san babu yadda za a yi Azumi ta ce ki zo sunan nan" Cewar Tsahare tana yiwa Tasalla wani kallo.

"Eh bata gayyace ni ba da Allah yi maza ki sama mini É—an sahu ya maidani tasha" Cewar Tasalla dan gwara Tsahare ta ce mata komai a kan ta shiga gidan da miciji yake.

"Ai fa tun da kin riga kin zo to komai ta famjama fanjam jam" Cewar Tsahare tana kaÉ—a kan Tasalla suka tasarma cikin gidan.

*INNA*

Tun sanda ta fara nafilfilin nan ko hutawa bata yi haka take bari sai ta yi raka'a huɗu sannan ta sallame ta rinƙa jero addu'oi ta rinƙa kuka hawaye na zuba tana ta neman yafiyar ubangiji.
Chapter 32 · 0% Book details