← Book details Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh Allah ni Azumi kamar wanda aka sanyani cikin buhun fulawa ji yadda farin ƙanƙanarar nan ya maida ni kamar furfura ta kar ni, ganin mukullin ya faɗo daga jiki, saboda bugawar da ake, cikin sanyin jiki da tsoro ya ɗau mukullin ya sanya jikin freezer ya buɗe a tsorace tare da ja baya kaɗan bakinsa sai kaiwa da komowa yake wajen addu'a amma baka jin me yake cewa shi kansa be sai me yake karantawa ba.

Yana buɗe freezer sai ya yi baya ya maƙe a bango, yadda ya tsaya kamar ka ce as ya zura a guje, jira yake kawai wani abu ya fito ya arce a na kare, dan ya yi alƙawarin idan ya doshi ƙofar gida sai dai idan ya je ƙofa ya ce kowa ya taho sarkin aljannu a frezer.

Inna ganin an buɗe dan ta ga alama murfin ya ɗan ɗaga da take ɗaga shi sama da kanta, hamdala ta yi a zuciyarta, ta fara kiciniyar miƙewa amma ina, ashe gabaɗaya zanin setin mazaunanta ya haɗu da ɗan sauran ruwan ƙasan freezer ya daskare har zanin. Hannu ta kai ta taɓo sai ji ta yi gabaɗaya ɗuwawunta yana danne da zani da ƙanƙarar.

Bata gama tsurewa ba sai da ta jita gabaɗaya a daskare har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa saboda ta san ita tana jiyo maganar mutane amma ita ta ga duk kwakwazon da take ba a jinta.Zunkuɗa kanta ta yi cikin sa'a kuwa sai ƙoƙon kanta ya buɗe murfin ya yi sama. Imran da ke rakuɓe a jikin bango dan tun lokacin da ya buɗe ya koma ya rakuɓe sai karkarwa yake kamar shi ne a freezer, ganin an buɗe ƙofar sai kawai ya saki kuka yana ta matse ƙafafunsa amma tsoro sai da y sa fitsarin da yake ta matsewa tun daga lokacin da freezer ta fara girgiza ya ƙwace masa ya zubo. Tsoro ne marar misali ya baibaiyeshi.

"Ku min rai dan Allah, in gidan ma kuke so mu bari a yau É—in nan za mu bari a yanzu ma kuma ko tsinke ba za mu É—auka ba, ku taimaka mana" Ya faÉ—a yana ta so ya zura a guje amma gani yake kamar ma rafkoshi za a yi a dawo dashi kicin É—in.

Inna kuwa gyaran murya ta shiga yi dan muryar duk ta shaƙe. Ai gyaran muryar da ta yi sai ya bala'in ƙara sanya Imran cikin tashin hankali da mummunan tsoro, bai ankara ba sai jin bakinsa ya yi yana faɗin

"Ya kusamu ya mu rasa, ya kusamu ya mu rasa" Sai maimaitawa yake kamar wanda aka sa tilawar ƙur'ani, shi kansa bai san me yake faɗa ba. Ya gama jiƙewa da hawaye da fitsari ga majina duk shi kaɗai kawai sai ji ya yi ta cikin freezer an ce.

"Imirana, Imirana, Imirana" Jikinsa ne ya fara karkarwa be ma san ya aka yi ba kawai dai ya ga ya fara zagaye wani kofi da ke tskiyar kicin É—in, sai zagawa yake kamar yadda ake É—awafi yana cewa

"Ya ku samu, ya mu rasa" Dan yadda aka kira sunan nasa ya tsorata shi dan yanzu dai ya tabbatar sarkin aljannu ne dan ya ji an kira shi d sunansa da alama suna ganinsa suna kuma sane da motsinsa. Dan yadda muryar Inna ke shaƙe idan ta yi magana kamar an shaƙewa kuturu wuya haka sautin ke fita, gabaɗaya ma ya manta da wata Inna bare kuma ya gane ita ke kiransa Imirana.

"Imirana, yaka buÉ—e firinjin nan" Cewar Inna dan duk abin nan da ake murfin freezer É—agawa yake kawai idan Inna ta buga kai a jiki.Imran kuwa ji ya yi tamkar ya zura a guje, amma ba hali.

A hankali ya taka ya ƙarasa wajen hannunsa na karkarwa ya kama murfin freezer yana sakin wani kuka me cin rai marar sauti, haka ya buɗe freezer cikin cika umarninsu amma sai ya rufe idanunsa gam dan gani yake idan suka yi ido huɗu ganinsu zai sa ya haukace.

"Oh ni Azumi matar Malam sai yanzu kuka kawo min ɗauki" Imran da ke riƙe da murfin freezer ido a rufe hawaye na kwaranyowa sai karkarwa jikinsa ke yi ya tsinkayi muryar Inna daga cikin freezer da sauri ya buɗe idon aikuwa idanunsa ya sauka a kan Inna da ke cikin freezer ita ba a zaune ba ita ba a tsugunne ba, ga wani ɗankwalinta ya yi gefe ɗaya ya mata wani zungurgur kamar hular ibro.Ta yi wani yamutsatsa kamar an tsamo ɓera daga ruwa, Gabaɗaya sai Imran ya manta halin da yake ciki na damuwa, a take ya saki wata dariya dan har ya hango dalilin shigar Inna freezer.

"Hassan" Ya faÉ—a a zuciyarsa, wato dai saboda miciji ta shiga freezer ya baiwa kansa amsa.

"Ko wa ya kulleta kuma?" Ya faÉ—a a ransa.

"Tabbas a kwai ayar tambaya da...

"Imirana tsamoni dan Allah"Cewar Inna murya a shaƙe.

"Me kika ce " Ya faɗa dariya na fitowa daga bakinsa irin dariyar ƙetar nan, Wani haushi ne ya turnuƙe Inna dan ita babu yadda za a yi ta fito dan ɗuwawunta daskare yake a jikin zani"

"Ni yau na ga abin mamaki ɓatan nono a ƙirjin budurwa" Cewar Inna cikin shaƙewar murya

Lura da Imran ya yi cewar Inna a daskare take sai ya miƙa hannu zai fiddota, aikuwa ya finciko ta da ƙeta.

"Wayyo mafitar kashina, wayyo Allah na haba Imirana ƙanƙara fa na yi" Cewar Inna cikin shaƙeƙƙiyar murya.

Dariya Imran ya ƙyalƙyale da ita, dan daga yadda ya finciko hannun Inna ya jita a manne da freezer, amma a haka yake ƙoƙarin fiddota amma ta ƙi ɓanɓaruwa.

"Haba Imirana ka kashe firinjin mana mazaunan nan nawa su ɗan saka mana, amma kake janyoni baka ji yadda muka yi tif da taya ni da firinjin ba kamar an manne tangaran da sufagilu" Cewar Inna cikin fuskar tausayi, haka dai ya kashe soket ɗin sai da ta ɗan saka ya taimaka mata ta fito, amma dariya na cinsa, haka ta fara takwa dakyar saboda yadda jikinta duk ya yi tsami ga karkarwa da atishawa da take yi a kai- a kai. Haka ta dudduƙo ta fito daga kicin ɗin tana dudduƙawa, tana ta kwashewa yarinyar nan me ƙunshi albarka, a haka ta fito ta kwa yi ido huɗu da sauran matan nan tsaye cirko-cirko har Ashrof lokacin ita ma ta fito sai maida yanda aka yi suke. Ganin Inna a yanayin da take sai kowa ya zura mata ido. Banda yarinyar da aka riƙewa mamanta, ta daddage sai masifa take a kan an riƙe mata nono a loka har sai da ta yi fitsarin wuya.Ita kuma ɗayar sai bata haƙuri take ta ce ba da niyya ta yi ba amma sai masifa take. Inna na ƙarasowa ta kalli yarinyar a shelaƙe ta ce

"Ni ina dalili kin damu mutane tun ina cikin firinji nake jin kina an damƙe miki nono, wai a nan ina nonon yake? Ba dan fuskarki ba ma babu yadda za a yi a banbance gabanki da bayanki, abu kamar an sawa muciya zani ba gaba ba baya, amma a haka kike cewa an damƙi nono, yo an damƙi nono ko dai an damƙi fata da fatar ma kika ce da daɗi, dan ban ga nono a nan ba wannan ƙirji naki kamar ƙirjin babe"

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣

Tsit gidan ya yi baka jin motsin kowa, sai sautin kuka Sadiya da ke tashi, dan kowa yana mafakarsa ya ɓuya. Inna duk da sanyin da ake amm sai jabga uban gumi take saboda tsabar tsoro da kuma yanayin da take ciki, uban buhhunan da ta libgawa kanta kaɗai sun ishe ta da zafi sai zufa ke ta faman kwaranyo mata tana sanya hannu tana gogewa.

"Oh Allah mutubi am, in ji fulani wai yau ni Azumi ce cikin buhhuna rufe sai kace masara, da a ce wani zao yiwa Tasalla video na ya tura mata da na san sai na gaggara komawa gida saboda tsoron abin da zan je in tarar, yo ni da nake ƙafafa da birni kullum ina mata gorin bata ƴan uwa a birni amma a tura mata videona ina ƙunshe a buhu ni ba tafasa ba sai ka ce wata kukar kaɗi"

Cewar Inna ta haɗa hawayen da gumin ta goge, tana tuna duka -duka ba a ɗauke wasu lokuta masu yawa ba da ta baro cikin freezer yanzu kumangata ƙasan benci rufe da buhu.

"Allah ka yafe mana idan saɓo muka yi amma lallai muna haɗuwa da jarabawa musamman ni Azumi" Cewar Inna tana hararo abubuwan da suka faru da ita daga barowarta ƙauye zuwa birni.
Dariya ta ƙyalƙyake da ita marar sauti sai da ta yi dariyarta son ranta har sai da dariyar ta tsagaita dan kanta sannan ta ce.

"Kai Allahu akbar Imirana Baban miciji ana can garƙame a cikin tukunya, yau dai ƙarshen tsafta da karkaɗar jiki sun ƙare tun da ana cikin sauran ruwan wankan jego luntsum" Ta faɗa tana ƙara dariyar ƙeta.
Jim kaɗan ta yi shiru kamar ruwa ya cita, can kuma da ta tuna kicin ɗin a kulle babu hanyar da micijin zai shigo ko da ya ji motsi ko magana sai ta dage ƙarfinta ta ce

"An ɓuya? An ɓuya?? An ɓuya???" Ta faɗa tana dakatawa dan jin abin da zai wakana, aikuwa kafin laɓɓanta su gama haɗuwa wuri ɗaya sai ta ji ƴan cikin loka suna ta surkune surkune alamar sun, a gyara zama dan jin abin da Innar ke faɗa sai suka ɗauka wani abu ne na da ban.
Chapter 5 · 0% Book details