← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murde mata kunne tace idan naji labarin kinje asibiti sena yankaki a gidan nan na idasa idon ya tsiyaye kinji ko baki ji ba tace naji ta rankwasheta ta fita washegari ranar jaji bari gidan ya kacame game kitso da lalle sunzo ana masu an gama ma husna kitso salma lalle me kitson tace zarah matso in maki ke kuma husna jeki a maki lallan [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 salma tace aiko se an fara min kitso an gama min za a mata me kitson tace haba salma baki ga naki lallan be bushe ba ko so kike ya lalace ki bari a gama ma zarah kitson se a maki tace nana dole fa ni zaki fara ma kitson nan kuma idan ma lallan ya lalace ai a jikina yake kuma idan kince se zarah zaki fara yi mawa sede dukanmu mu rasa kitson wata kuma tazo tamin kuluwa me lalle tace haba salma wai ke meyasa baki da kunya ne tace eh naji banda kunyar ai ke kina dashi taja mata tsaki mommy ta fito tace hayaniyar me nake ji haka salma tace wai nana ce dole se ta fara ma zarah kitso shine dan nayi magana har wannan kuluwan ke cewa banda kunya mommy tace wane irin bata da kunya ni ban haifi mara kunya ba nana ki fara mata kitson banso ana matsa ma yarana ba nana ta matso ta fara ma salma kitson tace zarah bari nayi sauri na mata se na maki naki ko amma ta shigo da sallama da gudu zarah taje ta rungumeta ta fara kuka amma tace daga zuwana se kuka to bari in tafi in barki tace a'a ta rikota ta zauna suka ga tace ina maman taku zarah kirata mu gaisa ta tashi taje ta fada mata seda ta mula ta fito se amma cema ta gaidata zarah ta mike ta shiga wurin daddy tace ga amma tazo a tare suka fito ya gaidata tace nazo ganin zarah ne yace aiko kin kyauta amma tace ko zaka bani ita tamin sallah yace ko zaki bari gobe a kawota tunda yanzu kitso za a mata tace inde ba damuwa ka bani ita zansa a mata a can akwai diyar kanwata da tazo ba abinda bata iya ba seta mata yaceyace shikenan ba damuwa zarah jeki dauko kayanki da gudu cikin murna ta shiga ta dibo kayanta ta fito mommy tace hala shekara zaki yi kika dauko katon jaka tace ai kayan ciki basu da yawa amma tace inma yana da yawa ai da adadin kwanakin ya kare za a maidota ne daddy ya dauko mata karamin jaka da kanshi ya maida mata kayan a jaka suka fito ta tafi sashin su gaje ta amshi maganinta ta fito suka tafi suka tarar da ahmad yace Amma kika yi zamanki tace to ba gani na fito ba zarah aka hada ma kaya zarah tace uncle ahmad ina wuni ya amsa yace baki zuwa gidanmu ko tace ina zuwa duk sanda naje baka nan kuma a gidan mommy bata barina zuwa ko ina suna isa gida amma ta fara bata abinci taci tayi wanka ta fito ta tadda bakuwar a palour ta gaidata tace amma wannan ce diyar aunty halima tace eh tace aiko tayi wayau sosai zarah zo kinji baiwar Allah taje wurinta tace to ke ya sunanki amma tace aunty falmata tace zauna na maki kitson ta tsara mata shi da kyau ta koma ta mata lalle ta kalli kitson ta kalli lallan tayi murmushi tace nawa ma yafi wanda ake ma su salma da suka hana Amin zarah tayi sallanta cikin kwanciyar hankali da kulawa se abinda take so take yi ji take inama a barta a nan haka uncle ahmad ke fita da ita yawo abin na mata dadi ga aunty falmata na kula da ita ta sake abinta ranar da za a maidata asibiti daddy da kanshi yazo ya dauketa ya kaita doctor ya gama dubata ya kara bata magani yace alh yanzu se maganar glass da za a mata yace ba matsala a mata suka mashi sallama suka tafi be maidata gida ba seda ya gama yawo da ita ya mata siyayya kana ya maidata gidan amma ana gobe zasu koma hutu aka zo dukanta ba dan rai yaso ba suka rabu zarah ta koma cikin kunci haka take tafiya school wataran da dadi wataran ba dadi sede hakuri zarah na class yunwa ya isheta ta kasa jurewa tasa hannu ta dauki roban wanda ke kusa da ita samosa da spring roll ne a ciki ta hada da capri sonne ana break ta hau neman abinta tace anty an sace min abincina tace wa ze dauke miki kuma wa yace baki aje a inda ake ajewa ba [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 tace anty saboda ban sa a basket bane shiyasa ban aje a nan ba zarah na kokarin fita anty tace zarah dawo ciki ta dawo tace kawo inga school bag dinki kowa ya tashi tana amsan hakan ta bude ta gani ta fito dashi tace mata wannan ne tace eh yaran class suka fara mata ihu anty da dakatar dasu zarah ta fara kuka anty taja mata hannu suka fita ta zaunar da ita tace zarah meyasa kika dauki abinda ba naki ba ta fara kuka tace ki dena kuka ki fada min tace yunwa nake ji tun jiya da rana dana ci abinci ban kara ci ba idan na tambaya se ace min ya kare tace meyasa da kina jin yunwa baki fada min ba baki san sata ba kyau ba duk wanda yayi sata fa yankashi za ayi ya mutu ko kina so in fada kinyi sata a yankaki cikin tsoro tace a'a ba zan kara ba kada ki fada tace to ba zan fada ba yanzu zan rufa maki asiri amma idan kika kara zan fada cikin kuka tace na dena anty kiyi hakuri tace kudin nan ma dana ganki dashi na wani ne kika dauka ko kika ce min daddynki ya baki tace bana wani na dauka ba shi ya bani tace to ko da wasa kada ki kara taba abin wani in bashi ya baki ba in ba haka ba kafin a yankaki ki mutu se an fara yanke miki hannu kinga jini na zuba sannan sannan za a ci gaba da yankaki tace ai na dena ba zan kara ba da kanta ta siyo mata abinda zata ci seda ta gama suka koma class sun koma gida husna da gudu ta isa gida tace mommy yau zarah tayi sata a class zarah na shigowa mommy tace zo nan ta cire mata kayan jikinta ta hau dukanta kamar ta samu babba zarah ihu take tana ba zan kara ba na dena mommy dukanta kawai take tana karawa zakiyi ihu take bame cetonta aka hankada mommy tayi baya zata fadi zarah ta mike da sauri ta fada jikin yaya deen goggo rabi tace kede wannan mata anyi muguwar mata ba imani a tare dake me zaki buga a jikin yarinyar nan aunty tace na gaji da mugunta da cin kashin da kike ma yarinyata dan haka yau zan kawo karshen azabtar da kike mata da UKUBA da kanta ta shiga dakin ta kwaso mata gaba 1 kayanta ta fito tace ku tashi mu tafi mommy tace ba inda zaku tafi da ita aunty tace ba wanda ya isa ya hanani tafiya da ita deen fitar min da ita gani nan zuwa goggo rabi tace haka nake so inji daga bakinki mommy tace ku tafi da ita yanda kuka tafi da ita haka zaku dawo da ita ba wanda ya kulata suka tafi ta kira waya tace kina ina kizo yanzu tace gani nan a layin gidanki zanzo tace yauwa tana isowa ta fada mata komi suka bazama se wurin tsubbu bayan gama surutunsu yace ga wannan kisa a gabanki seya dade ki cire ki busar dashi se ki rinka zuba mashi a abinci wannan kuma se ince kin samu duniya dan se yanda kikayi dashi bashi ba kara musa maki da kin mashi maganar ya dawo da ita seya daukota ya dawo da ita dan yanzu ba maganar wanda ze kara saurara se naki tace kace zan zuba mulkina son raina yace sosai kuwa suka kwashe da daria [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 isan su zarah gida goggo rabi ta samu ruwan zafi ta gasa mata jikinta da ruwan zafi ta bi jikin nata da rubb tasa mata kaya suka fito palour ta dibo abinci ta mika mata zarah tace na koshi goggo rabi tace me kika ci da zaki ce kin koshi da kanta ta rinka bata seda taga ta koshi sannan ta kyaleta aunty ta fito ta zauna tace sannu goggo rabi tace yauwa aunty tace zarah meyasa kika dauki abinda ba naki ba ke kika ajiye tace a'a to me yasa kika dauka irin tarbiyar da aka koya maki kenan tace a'a aunty tace sata fa kenan kikayi tunda ba naki bane ba baki akayi ba ko kinaso yan class dinku su tsaneki da sun ganki su rinka boye kayansu tace a'a to inde baki son haka to kada ki kara daukan abinda ba a baki ba ko ba naki ba kinji ko inba haka ba nima da kaina ba ruwana dake zance su minal ma kada su kara maki mgn har yaya deen dinki ma zance ba ruwanshi dake tunda kina daukan abinda ba naki ba tace a'a aunty na dena ba zan kara ba tace kinyi alkawari ko ta daga kanta tare da cewa eh nan taci gaba da bata kulawa da sauran yan gidan a nan ake kaita school da an kusa tashi aje a daukota kafin a tashi daga shool itako mommy gaba 1 ta gama aiwatar da komi nata se jiran sakamako bata tada mashi da maganar ba a zuwan da yayi saboda koda ya dawo be samun zaman gidan lokacin da ze dawo sunyi barci shiyasa be san bata gidan ba gaba 1 ta riga ta gama rikitashi tasan yanzu ta gama dashi dawowar da yayi kowa yaje gaidashi bega zarah ba yace ina zarah tace wace
Chapter 9 · 0% Book details