← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 24

Sashe 8

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bada gangan na zubar ba tace me k jira ki jawo min ita ta jawota da sauri zarah ta zube kasa tace mommy dan Allah kiyi hakuri aunty Khadija kiyi hakuri mommy ta fara dukanta tana ihu tana mommy kiyi hakuri ba zan kara ba seda ta gaji da kanta sannan ta kyaleta ta tureta ta tashi da gudu zata fita waje tace dawo ina zaki ta dawo tayi daki da gudu taci gaba da kuka ranar taki fitowa har seda lesson teacher dinsu yazo ta fito bayan ya gama ma husna yace zarah muga naki ta mika mashi yace ya akayi baki yi homework din jiya ba tace uncle idona kemin ciwo bana gani sosai sbd idon rufewa yake gashi yana min zafi yace ayya ba a sa maki magani ba tace ya kare yace kice a kaiki asibiti tace to yace an baki homework a school tace eh ya amsa ya mata duka sannan ya bata yace tashi ki tafi ta mike ta tafi zarah baiwar Allah da dadi ba dadi haka take ta hidimanta makaranta kuwa bata fasa zuwa ba duk da bata yin komai a school din malama suwaiba da kanta taje ta samu mansir ta amshi number din daddy ta kirashi bayan ya dauka ta gaidashi sannan tace malamar zarah ce wai ba za a kai zarah asibiti ba se idonta ya kai ga tsiyayewa sannan za a nema mata magani yace ai bana gari nayi tunanin idon nata ya warke tace ka bata magani ne yace yanzu de zan kira gida a kaita asibiti tace alhaji idan ba zaka damu ba ka bar komi a wurina zan kaita asibiti se ka bada abinda za a bukata yace to ba damuwa zanyi waya da driver seya rinka kaiku haka ko akayi sunje asibiti doctor ya dubata ya bata magunguna na sati 1 yace ga su nan tayi amfani dasu na sati 1 pls kada ayi wasa da maganin tace insha Allahu zamu kiyaye yace Allah ya bata lfy tace Amin suka fito bala ya maidasu makaranta nan malama suwaiba ta bata magani ta diga mata a ido ana tashi ta riko hannun zarah ta samu bala tace to kaga maganin zarah doctor yace kada ayi wasa dashi wa kake ganin ze juri bata saboda kaga harda dare za a bata yayi jim sannan yace juma tunda tana gyara masu daki da daddare kinga seta zauna a dakin data sa mata seta kwanta tace hakan yayi yanzu ga maganinmaganin ka tabbatar ka damka ma juma a hannuntahannunta yace insha Allahu ranki ya dade zarah kinde ji ko ta daga kanta suka mata sallama suka tafi gida haka ko akayi wurinwurin amfani da maganinta sati na zagayowa bala yazo makaranta ya daukesu ya maidasu asibiti [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 suna isa doctor ya amshesu da wuri ya gama dubata ya bata takarda me rubutu kanana yace ta karanta bata ganin me aka rubuta yace ga magani amma idan ta gama sha kika dawo da ita next week naga ba canji to se an mata glass sbd kada wurin karatunta taci gaba da samun matsala kinga yanzu jan idon da jagwalewan da yayi ya ragu sosai tace to shikenan ya maida kallonshi ga zarah yace kuma ki rage kuka kinji ko kina so idonki ya tsiyaye ki dena ganin kowa cikin sauri tace a'a yace yauwa to ki dena kuka ta daga mashi kai alamun taji suka mashi sallama suka tafi malama suwaiba ta samu bala tace gashi gobe za suyi hutu gashi za a koma da ita asibiti next week yanzu ya zamuyi tace na manta ne dana sati 2 muka amsa yace aikuwa tace amma kana ganin ba matsala zaka kaita a ranar yace eh insha Allahu ba matsala se inyi magana da alhaji inama tunanin ranar ma alhaji yana gari tunda kinga ranar ze anyi sallah da kwana 3 tace hakane da aka tasheku tace zarah gobe ba se kinzo ba tunda hutu za ayi dama ba abinda kike ko kinzo ta daga mata kai har mota ta rakata tace se kun dawo ko Allah ya baki lfy husna ki gaida mommy zarah taci gaba da daga mata hannu har suka bar wurin suna isa dakin su gaje ta fara isa cikin sanda dama seda ta bari duk suka gama shiga daki tayi sauri ta shiga ta fito da maganin tace inna juma ga maganina ta amsa tace kuma kun san abinda doctor yace suka hada baki sukace a'a tace yace idan ina kuka wai zan dena gani ta dafa gaje tace kuma kina ganin da gaske yake inna gaje zan dena gani tace tunda likita ya fada maki ki yadda tayi kallan tausayi tace bari nayi sauri na tafi kada mommy ta nemeni da gudu ta fita ta bar dakin tana shiga mommy tace ke ina kika tsaya cikin tsoro tace garden naje tace wai in tambayeki an maki asiri da wurin ne da dole se kinje wurin tace a'a khadija tace waya sani ko akwai abinda munafukar uwarta ta aje a wurin mommy tace ze iya yuwuwa idan na Kara ganinki a wurin sena yankaki kinde san halina ta girgiza mata kai tashi ki bani waje ta mike ta shiga daki tayi zamanta husna ta shigo zata shiga toilet ta tarar zarah na alwalan magriba ta jawota tace fita zanyi fitsari zarah tace baki ga alwala nake ba ba zan fita ba tunda ke ba alwalan zaki yi ba husna ta kai mata duka bata kulata ba ta cakumeta da fada ta yadata kasa zarah ta tashi cikin zafin zuciya taci gaba da dukan husna ta fara kuka zarah ta fito ta bar mata toilet husna ta dibo ruwa ta kwara mata akan gadonta zarah ta kara fisgota taci gaba da dukanta har ta yaddata ta haye kanta salma ta shigo ta daga zarah akan husna ta hau dukanta husna ta fita dakin se gata ita da mommy tace me ta maki tace itace ta fara dukana kuma ta jika min gado shine zaki bigeta kamar kin samu jaka tace ai salma ta bigeni tace nima yanzu zanyi nawa ta farafara dukanta tana ihu seda ta bigeta son ranta ta kyaleta lesson teacher yazo duk suka fita ta tashi tayi wurinsu gaje tana kuka gaje ta rikota tace zarah lafia tace mommy suka bigeni akan husna kuma ita ta fara tonona gaje tace kiyi hakuri ki dena kuka ba ke kikace likita yace in kina kuka idonki ze rufe ba ko kinaso ya rufe din ki dena gani tace a'a tace to ki dena kukan [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 juma tace kinci abinci tace a'a ta dauko ta bata tace share hawayenki kiyi sauri kici ki tafi ta dauka ta fara ci tana gamawa ta mike ta tafi ta koma daki ta rakube a kasa ta kudundune bayan juma ta shigo gyara masu daki tare da maganin zarah ta bata ta diga mata a ido sannan ta fara aikinta tazo gadon zarah taji shi a jike sosai tace zarah dama haka aka jika gadon sosai zarah ta taba gadon cikin muryan kuka tace wai meyasa kun cika mugunta ne inna juma kara jikawa akayi ta fara goge mata hawaye tace zarah kada kiyi kuka kinji watarana da kudi ma akace su maki haka ba zasuyi ba tace a yaushe tace lokacin na nan zuwa zarah tayi shiru bata kara cewa komi ba juma tace ki shimfida bargo a kasa ina wanda daddy ya siyo maku kwanan nan tunda har wannan ta jikashi tace ai tun ranar mommy tazo ta amshe tace 1 ya isheni da aunty Khadija zata tafi makaranta naga dashi ta tafi juma tace Allah ya kyauta ta gama ta fita nan zarah ta kwanta a kasa ta samu ta rufa da towel dinta seda ta jera kwana uku tana kwana a kasa gaba daya gidan ya isheta burinta taga an koma makaranta yafi mata dadi dan jinta take kamar akan kaya sati biyun da aka basu ya mata yawa tafi sakewa a makaranta nan gida ko in banda wahala da tsangwama ba abinda take fuskanta wannan ya zaga wannan ya buga daddy ya dawo ana jibi sallah duk kowa yaje ya tareshi suna zaune dakinshi duk sun zagayeshi ta shigo ta duka can nesa dashi ta gaidashi yace zarah zo nan kusa da yanuwanki zo ma nan wurina ki bani labari a tsorace ta isa wurinshi ya riketa yace ya idonki tace yayi sauki ya dago idon yace eh gaskia kin samu lafia maganin de baki wasa dashi ko tace eh kullum ina amfani dashi yace yaushe zaku koma asibitin tace saura kwana uku yace Allah ya kaimu ya baki lafia tace amin mommy tace wai maganar me kuke ne yace asibiti ne da ake kaita kan matsalan idonta tace shine ina gidan ban sani ba a matsayina na uwar rikonta kuma har a kaita asibiti ta shigo da magani gidan nan ban sani ba saboda munafurci a kanki ya kare yar karama dake kin iya munafurci ko da yake ai barewa ba tayi gudu danta yayi rarrafe ba ansha an gada a gun uwa daddy yace haba hafsat duk me ya kawo haka tace ban sani ba gara tun wuri kasa ma bakinka linzami dan kasan bana son raini yaja bakinshi yayi shiru haka taci gaba da fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba daddy daya gaji ya sallami yara shima ya tashi ya shige bed room dinshi ya barta nan ta mike ta koma dakinta ta dauki waya ta kira can bangaren ana dauka ko gaisawa basu yi ba tace hajia Amina akwai matsala baban khadija ina tunanin ya dawo hayyacinshi hajia jamila tayi tsaki tace ai ke keda matsala da kinyi magani so daya kika ga ya kama baki kara waiwaya ai ko shuka kikayi se kina ban ruwa kina tusashi da taki zaki ga ya maki tofo mai kyau da ban sha'awa mommy tace to yanzu miye mafita dan ko kudina ze kare inyi yawo tsirara sena maida zarah abin kwatance hajia jamila tace yanzu sede mu bari a gama sallah se muje ta fito ta shiga wurin zarah ta
Chapter 8 · 0% Book details