Sashe 5
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuke so kenan aita yawo suna isa da sauri suka shige gidan ta dago tace baki nayi haka da yamma daddy yace aikuwa suka zauna aka gaisa auta kwana 2 baffanki yace be ganki ba yaji shiru nace mashi ai lafia take buya tunda kaji shiru tana lafia halima tayi daria tace ina ruwan baffa se gashi ya shigo tace aiko maganarka muke yace auta kune da yamma haka suka gaidashi Amma ta kawo masu kunun aya suka sha minal tace Amma ina kunun gyada da kika ce zaki min tace tofa ai ban san da zuwanku ba se in zaku kara zuwa a fada min se in tanaji kunun gyada [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 1 tace to gobe zan dawo Amma tayi daria tace minal kenan daddy yace kin bata ajiya ne Amma tace ina ruwanka tsakaninmu ne yace to Amma nayi shiru tace da yafi baffa ya kalli zarah yace ya banji matar nawa na magana ba me aka maki zo ki fada min tace bakomai yace to shikenan Amma tace jibi fa zan tafi maiduguri halima tace kai amma shine baki fada min da wuri ba tace ai dama yau zan kiraki in fada maki tace se yaushe zaki dawo tace sati 1 zanyi kawai zarah tace amma zan biki tace ke ba zaki iya tadiyan nan ba barmu mu da muka saba tace nide zani tace ai kinga kun kusa komawa makaranta wataran maje tare tace ai har maje mu dawo to ke da kin kusa komawa gida tayi dariyan farin ciki tace albishirinki ai daddy yace ba zan koma ba tunda suna min mugunta amma tace haba tace da gaske halima tace bari mu tafi zan ma babansu girki tace ai na kusa gama miya bari insa mashi tuwon shinkafa ne da miyar da yake so na shuwaka daddy yace aiko amma bari mu tsaya a gama halima tace ai an hutar dani suka jira ta gama sannan suka tafi gida an koma hutu aka fara shirya ma zarah komawa gida tunda taga an fara shirya mata kaya ta fara kuka duk yan gidan suma kuka suke halima ita kanta dauriya take tana basu hakuri tace idan kuna kuka aka kara bada hutu ba zata zo ba kamar kara zigasu take minal tace aunty kinfa ji tace ana mata mugunta se a maidata ta jawo zarah jikinta tace kinga na kusa tafiya makka suma kinga bauchi zasu tafi sena dawo zasu dawo kinga dana dawo zanzo na daukeki tace to ba daddy yace a nan zan zauna ba kuma ba yace daga bauchi za a zo a zauna dasu ba da baba jummai ta tankwashe kafa tare da nade hannunta tace ba inda zan koma jummai tace aunty to ki barta mana tace ta ya zan barta idan inaso ya kara bani ita ai gara na maidata kan lokaci jummai ta fita itama cikin jimami aunty tace kamal dauko key mu tafi maidata yace aunty ba zani ba zarah tace inde ba zaka ba nima ba zani ba da kyar aunty ta lallabashi suka tafi suna isa gidan duk a tsorace take kamal yaki shiga ta makalkaleshi dole ya riketa suka shiga ciki mommy tace se yau ake dawo da ita aunty tace mun karya doka ko gade ta nan mun maidota ta mike to mude mun tafi zarah ta kwalla kara ta biyosu da gudu halima tace bala kamata ka maidata cikin gida suka fita idon kamal jajir ya kasa jurewa ya kifa kanshi a saman mota ya saki kuka aunty tace haba kamal namiji da dauriya aka sanshi ba bani key din ba musu ya mika mata tace shiga mu tafi taja suka bar wurin zarah taci gaba da kuka khadija ta taso ta bige mata baki tace yimin shiru kinbi kin cika ma mutane gida da kuka ta rike bakin tana ajiyan zuciya yaya mansir yace tashi ki fita kiba mutane wuri taja jakan kayanta takai dakinsu ta kara fitowa daukan jakan kayan wasanta mommy tace wancan jakan miye a ciki tace kayan sawana ne tace wannan fa tace na wasa ne bude in gani ta bude mommy ta hau dagawa duk wanda ta daga se husna tace tana so haka duk ta gama mika mata zarah tace mommy nawane fa itama husna ba tana da nata ba tace eh ai nasan tana da natan na bata naki ta turo mata akwatin tace tashi ki bani wuri zarah taki tashi ta fara kuka mommy ta kai mata duka tace yimin shiru zarah tayi kokarin tayi shiru amma ta kasa mommy tace ba zaki hadiyeshi ba sena karkaryaki a wurin ta saki kukan gaba 1 haka mommy ta jata ta fita da ita waje tace idan kin gama kukan kya dawo dede lokacin ruwa ya sauko ta biyo mommy da sauri ta hankadata ta fadi ta maida kofa ta rufe ruwa ake sosai haka yake ta jikata wani tsawa aka saki daya firgitata ta kwasa da gudu tayi sashin su juma ta tura taji a rufe ta tuna suna sashin mommy suna aiki wani tsawa aka saki ta saki kara tayi hanyar waje ta shige dakin megadi bala ya riketa yace zarah lafia tace mommy ce ta amshe min kayan wasa tabama husna kuma ta koroni waje wai dan nayi kuka mallam musa yace kai wannan mata ba tada imani anya bala tana son rahamar Allah kuwa bala yace anya kuwa zauna a gama ruwa ki tafi [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 ruwa na daukewa mallam musa yace to yi sauri ki koma gida ki canza kaya kafin sanyi ya shige ki ta ruga da gudu bala yace gaskia ina jin tausayin yarinyar nan sosai mallam musa yace hada dani ai matar nan ba zata ga annabi ba kaga fa inba 'ya' yanta da yanuwanta ba wanda yake zama nata da take so kai ka zama makiyinta jibi yanda maman zarah taci wuya a gidan nan seda ta bar gidan hankalinta ya kwanta bala yace kai de Allah ya karemu daga sharrin irin matan nan haka ta hau buga kofan sadik yazo ya bude mata ya rankwasheta yace se kin balla ma mutane kofa kike bugashi haka ta dafe wurin ya shige ta bishi ta shiga dakinsu ta cire kayan tasa wani ta zauna a ciki hawaye kawai ke zuba a idonta tana tunanin aunty dasu yaya deen ana sallan magriba mommy ta shigo dakin tace me kike a daki munafuka au har yanzu kukan kike aiko yanzu zan kara wurgaki waje magen dake shigowa gidan ya cinyeki kinga mun huta tace a'a mommy na dena kinga na goge hawayen tace karma kiyi shirun kici gaba zaki tashi kiyi sallah ko kuwa ko da yake ruwanki ma in baki yi ba kuma kayan da kika cire a jike wa ze shanya maki tace nice ta fita a dakin da sauri zarah ta dauki kayan tabi bayanta tayi tayi ta shanya ta kasa se tsalle take sega juma ta fito tace juma ki shanya min na kasa ta amsa ta shanya mata tace na gode ta shige ciki tayi alwala tayi sallah ta dauko littafinta ta dawo palour zaman jiran lesson teacher dinsu harta zauna ta mike ta shiga kitchen ta duba taga ba abinci ta dawo ta duka tace mommy yunwa nake ji tace au da kin san kina jin yunwa kika je daki kika zauna to babu saura nasu mansir ya rage dan haka tashi ki bani wuri kije can waje ki jira malamin naku yazo dan ba so nake in bude idona in ganki a kusa dani ba ta tashi da sauri ta fita ta wuce sashin su juma juma tace zarah ya akayi gaje ta kamota tace yunwa nake ji gaje tace baki ci abinci ba tace eh tasa mata tace yi sauri kici kafin hajia ta fito nemanki taga kina nan da sauri ta amsa ta fara ci juma tace yanzu fa yarinyar nan fa shekaranta 3 a gidan nan amma ba abinda ya sauya gaje tace haka fa tana shekara 2 aka maidota gidan nan in kika hada shekaranta 5 ta cinye juma tace ya isheki ta daga mata kai ta mika mata ruwa ta amsa tasha tace to tashi kiyi sauri ki tafi ta mike ta tafi da sauri ta isa inda ake masu lesson ta ganshi ya iso yana jiransu ta gaidashi yace yaushe kika dawo tace yau yace to bari in fara maki kafin su fito yana mata suka iso duk suka gaidashi husna tace uncle ka fara yimin yace baki ga an kusa gama mata tace nide kamin yace kai husna rigima yaci gaba da yima zarah seda ya gama yace ta matso ta tashi tace bana so bebi ta kanta ba ya fara ma sauran ta fada jikin mommy ta hau kuka tana fada mata kinga uncle seda ya fara ma zarah lesson da yake tana waya se bata kulata ba har barci ya dauketa a nan uncle abakar ya kalli zarah yace tashi ki tafi ki kwanta kada ki manta kiyi isha'i an kira tace to tana shiga daki tayi alwala tayi sallah ta dauki kayan barci tasa da kanta dan dabi an gidan aunty ne se an sa kayan komin kankantar yaro haka gidansu ma tun bata iya sa kaya da kanta ba har ta iya tana gamawa ta haye gadonta bata dade ba barci ya dauketa safiya nayi da zazzabi ta tashi bayan ta gaida mommy ta amsa tace miye kika kafeni da ido tace banda lafia magani za a bani tace bandashi bace min a gabana ta tashi ta koma tasa uniform suka wuce makaranta duk tana jin jikinta ba dadi ta rasa yanda zatayi haka suka isa [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 ta zauna a aji se kuka take kamar ranta ze fita mallam ya shigo yana karatu amma hankalinta baya wurin kuka take sosai tana kiran aunty mallam ya iso wurin ya buga bulala akan desk ta dago da sauri ya duko da kanshi kusa da ita yace zarah meke damunki ya tabata yaji jikinta zafi yace subhanallahi zarah baki da lafia ne tace eh yace kinsha magani eh nasha yace sannu