← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kinji ai an kusa tashi ki dena kuka kinji ta daga mashi kai kafin kace me jikinta ya fara rawa se rawar sanyi take ana tashi da kanshi ya rikota ya sata a mota sauran yanuwanta na shigowa ta zame jikinta ta zauna a kasa tsakani kujera suna isa gida da sauri ta shiga daki ta haye gado ta jawo blanket ta rufa jikinta rawan sanyi take sosai take girgiza kowa na palour amma banda ita mommy ce ta leko dakin taga yanda take ta kada kanta ta fita ba tare da tayi tunanin ta kawo mata agaji ba haka ta kwana cikin zazzabi sosai tana tashi da asuba taji jikin nata da sauki tayi shirin makaranta da sauri dan kar suce ta bata masu lokaci ta fito ta taddasu a zaune suna breakfast ta duka ta gaida mommy sannan ta juya ta gaida sauran zainab tace ai na zata ba zaki tashi ba ta mike ta shiga kitchen da sauri juma ta dauki tea ta mika mata ta bata bread tace yi sauri kisha da sauri ta amsa tana tura bread din tana hadawa da tea ta shanye ta dauko roban ice cream tasa mata a school bag tace dankali ne in kinje makaranta se kici tace to ta fita ta isa wurin motan da zata kaisu suka fito suka tafi ana yin break ta fita ta samu jikin bishiyan data saba zama ta zauna ta fara cin dankali da kwai ta hango yaya deen ta washe baki shima ya hau mata daria ya iso ya zauna se daria take ya mike yace bari in tafi tunda ba zaki min magana ba ta rukoshi tace a'a ya koma ya zauna tace jiya ban ganka ba yace kiyi hakuri test nayi a school har aka dawo break muna class yace ya kike cin dankalin duk ya huce meyasa ba a sa maki a flask ba tace ai juma ta bani a boye nima bana jin dadinshi idan ya huce to bana so na zauna da yunwa bece komi ba ya dauko leda ya ciro mata meatpie ya mika mata ya bude mata exotic ya mika mata tayi murmushi tace nama fasa cin dankalin yayi murmushi seda ta gama ci sannan yasa ta koma class sannan ya tafi kafin kace me zazzabi ya rufeta anty tazo kanta ta tsaya duk hankalinta ya tashi taje class din su mansir ta amshi number din mommy ta kirata tana dauka tace zarah bata da lafia sosai kisa a zo a dauketa tace ni yanzu bana gida sede in an tashi tace haba hajia tana jin jiki fa tace ai zaki iya kula da ita ta kashe wayan malama suwaiba ta rike waya cikin mamakin mugunta na matar nan ta juya ta koma class ta dauki zarah ta wuce da ita sick bey nan take aka mata allura aka bata magani malama sadiya ta shigo tace na leka class dinki naji haniya naga bakya ciki tace kede bari patient na kawo tana jin jiki na kira matar babanta tana fada min ba za a zo daukanta ba malama sadiya tace ai ni naga kunci da UKUBA da yarinyar nan tasha nida nayi teaching dinta tun daga nursery 1 har nursery 2 ke yanzu kika fara gani tace aiko duk sanda Allah ya hanani da mamanta zan bata shawara ta dauki yarinyarta tace to Allah yasa taji kowa ya wuce class dinshi ana tashi malama suwaiba da kanta ta daukota ta kaita mota suka tafi suna isa gida duk a lokacin barci take duk suka fita suka barta bala ya shiga ciki ya kira juma ta dauketa ta daukota ta kaita har daki ta kwantar da ita haka ta wuni tana barci da yake ranar alhamis ne washegari kuwa bata je school ba yaya deen yaje kamar yanda ya saba yaga be ganta ba ya isa class dinta ya tambayeta ina zarah tace aiko yau bata zo ba ba tada lafia yace meke damunta tace zazzabi da mura to kai ya kuke da ita yace babana take aure tace to dan Allah daka koma ka fada mata kome take ciki taje taga diyarta yace yanzu kuwa ya mata sallama ya tafi ya koma gida ya fada ma aunty tace to bari a sauko masallaci se muje yace haba aunty da sauran lokaci mu tafi yanzu tace kade bari anjiman yana dawowa yace aunty taso mu tafi tace se anyi la'asar yace haba aunty anfa ce tana jin jiki tace to ya zanyi babanka ya sani aiki ya koma ya zauna ya dafe kai la'asar nayi suka tafi suna shiga gidan ta dira a palour daddy suka gaisa tace nazo ganin zarah ance ba tada lafia kafin wani yayi magana husna tace tana daki muje in kaiki suka fita suna shiga dakin ta saki salati kamal da sauri ya isa wurinta yana jijjigata [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 aunty ta karasa wurinta hawaye ya zubo mata tace yanzu yarinya karama aka bari da ciwo ta fita da sauri ta fada dakin tace kiwon da Allah ya baka kenan ka kasa kula dashi ace yarinya na ciwo gata can kwance tayi amai a gado har ya kai ga ta isa hanyar bayi ta fadi nan ba tare da tasan inda kanta yake ba kada fa ka manta Allah seya tambayeka ya ka tarbiyanta da 'ya' yanka wane wace irin rayuwa ce yace nifa bana garin yanzu ban dade da isowa ba tace amma ai ga duka yaranka nan a tare dakai meyasa ita baka tambayeta ai itama hakkinka ce ita ba yarinyarka bace sbd ba idon uwarta a ciki se a saketa sakaka ai su sauran gasu nan sbd akwai idon uwarsu ai kana tare dasu mommy tace wai ke me kika taka da zaki shigo gidan mutane kina...aunty ta dakatar da ita da hannu tace ba dake nake ba ki dakata min banzo kanki ba kuma wllh alh kaji tsoron Allah domin seya tambayeka yace ai se ki tsaya ki saurareni tace ba abinda zaka fada min zata ci gaba da magana kamal yace yanzu fa ba lokacin cacar baki bane mafita ya kamata mu nema aunty ta kara komawa dakin kamal da kanshi ya dauketa suka fita ya sata a mota suka shiga yaja motar aka wuce da ita asibiti suna isa suka amsheta da hanzari akaci gaba da dubata nan take aka dibi jininta ba tare da bata lokaci ba aka sa mata drip har a lokacin halima kuka take kamal da kanshi ya kira daddy ya fada mashi suna asibiti sannan ya kira amma ya fada mata ba a jima ba se gata ita da ahmad aunty tace amma har kunzo tace eh ta isa gaban gadon ta tabata tace sannu takwara barci ma take ahmad yace ke kuma me ya saki kuka da girmanki ba zaki dena shagwaba ba tace yaya ahmad ba dole nayi kuka ba kaga halin da naje na tadda zarah kamar matatta haka zata ci gaba da rayuwa a gidan can kuma muna kallo hakurina ya fara karewa zan dauki mataki amma tace hakurin zaki kara da kauda kai tace amma kauda kai kuma ina ganin ana cuta kuma cutar diyar dana haifa da cikina amma tace to kiyi hakuri zamu ga yanda za a bulloma lamarin baffa ya shigo ta gaidashi yace ashe matana bata ji dadi ba amma tace aiko ga kishiyata nan kwance yace duk ta rame aikuwa da dare daddy yazo tare da kamal suka dawo da sauran yaran da abinci da sauran kayan ciye ciyen da mara lafia ze bukata da suka tashi tafiya amma tace ki tashi ki bisu ni se in kwana a nan tace a'a amma ki tafi gida tace haba ina nan ina zan barki a nan keda ba cikakken lafia ne dake ba wannan laulayi da kike fama dashi ina zan barki tashi kibi mijinki dole ta tafi ba dan ranta yaso ba washegari da sassafe ta iso asibitin ta tadda zarah ta tashi ta gaida amma ta wuce gadon ta riketa tace zarana sannu ta kwanto jikin aunty ta saki ajiyan zuciya ta kara matseta a jikinta hawaye ya sauko mata amma ta bisu da ido cikin tausayawa dede lokacin daddyn zarah ya kira wayan halima taki dauka amma tace bakiji ana kiranki ba ba zaki dauka ba tace baban zarah ne shiyasa ba zan dauka ba ya kara kira bata da niyyar dauka har ya katse yade kara kira amma tace dauka tun kafin na saba maki ta dauka tace ai na zata ba zaka nemeta ba yace habahaba ai ya zama dole na nemeta nan ko mommy ne ta bashi izinin kira da zuwan yace kuna ina yanzu tace muna ni'ima hospital yace to bakwa bukatan komi tace a'a mun wadatu da komi ta kashe wayan ta koma kan zarah tace me kike so tace ice cream tace kina mura ba zaki sha ba ta dago idonta tace zarah harda ciwon ido kuma tace eh kuma yana min zafi aunty ina yaya deen tace yana nan zuwa daddy ya shigo da sauri zarah ta sunkuyar da kai seda ya gaida amma sannan ya taho wurin zarah ya mata ya jiki yace me kike so tace bakomai yace kode mamanki ta hanaki tace a'a ya mike yace ze wuce amma ta bishi suka tsaya tace baban zarah dan Allah ka kula da yarinyar nan saboda kar ta saka a jerin wanda basa kaunarka sbd yaro rikone dashi yace Amma insha Allahu zan kiyaye ni kaina bana so haka na faruwa tace kuma ka rika dagewa da addu'a yace insha Allahu sukayi sallama ta koma ciki halima ta dauko kudi tace kinga ya aje kudi ai ya dawo ya dauka amma tace ai hakkinshine ya bada dan haka kada ki maida kinji na fada maki [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 haka akaci gaba da kula da zarah jikinta kam alhamdulillah ta samu sauki ranar litinin sega malama suwaiba tazo dubata itada malama sadiya bayan sun gaisa tace malaman zarah ce halima tace Allah sarki ya aiki tace alhmdllh ya fama da Yara sukace aiko gashi nan muna ta yi amma tace ai kuna kokari tace wllh kuwa duk
Chapter 6 · 0% Book details