Sashe 18
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zaria ne da nima baka sanni ba yace hakane da kuma bana kasar amma ba diyar mommy bace tace eh mamanta bata gidan Tace bari in shiga ciki na gaji ta shige ciki Waye farouk farouk dane ga hajia mairo yayar mommy ya tashi cikin gata da sangarta shiyasa yake gani duk abinda yayi dede ne a wurinshi su biyu iyayenshi suka haifa daga yayarshi nafisat se se shi auta shiyasa babanshi ya dauki son duniya ya daura mashi kome yake so shi ake mashi ya yana gama secondary school ya saman mashi gurbin karatu a malesia sanadin haka idonshi ya kara budewa yanzu ya dawo ya gama karatu inda yake aiki a nan kaduna hajia maryam ta nemi alfarmar ya zauna tare da mommy kafin a mashi aure nan aka bashi daki daze zauna a nan wannan shine takaitaccen tarihin farouk [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD zarah suna zaune da siyama karatu suke yi siyama ta aje handout din dake hannunta tace zarah ina so muyi magana me mahimmanci zarah ta kalleta tace ina jinki tace magana ne kan yaya hisham zamuyi tace ki bari se anjima kin san de test garemu gobe Kinga karatu nake tace zarah duk karatun da zakiyi a yanzu kin riga kinyi shi nasan baki da wannan damuwan sede in ba zaki tsaya ki saurareni bane zarah tayi shiru ta kyaleta siyama ta fisge handout din dake hannunta zarah zata mike ta riketa tace kawa wulakanci zaki min Ba wani magana me tsawo zamuyi ba tace ina sauraranki siyama tace yaya hisham yace shifa ya shirya aure yana so ki bashi dama kuyi mgn se yaga iyayenki zarah ki temaka mun kosa yaya hisham yayi aure zarah ta saki ajiyar zuciya tace siyama me kike so na fada maki nifa ban hada karatuna da komi ba kawai ki fada mashi yayi hakuri ba yanzu zanyi aure ba Siyama ta daure tace kin nuna mini iyakata yanzu na gane bakya sonmu Tun yaushe muke binki akan maganar nan ban taba tunanin zaki ki danuwana ba zarah tace haba siyama ya zanki danuwanki in na maki haka ban maki adalci ba ko dan halaccin da kika nuna min Tace gashi kuwa kin nuna min baki kaunarshi ta dau waya ta kira yana dauka tace yaya hisham dan Allah ka rabu da zarah bata kaunarka ka nemi wata ai ba ita bace aurar mata kome yace mata tace to shikenan nan se na dawo gidan zarah tace haba siyama me yayi zafi haka Akan dan wannan abin kawai siyama tace au wannan abin ne dan wannan to a wurina babba ne saboda kin nuna ma dan uwana kiyayya kinko san kaunar da nake mashi to ba zan jure a wulakantashi ba dan haka gara muyi nesa dake Ta mike zata bar wurin zarah ta riketa tace ki tsaya ki saurareni tace zarah ba abinda zaki fada min ta fisge hannunta tayi tafiyarta zarah ta duke a wurin ta fara kuka haka ta zauna sukuku har aka tashi Ta koma kamar mara lafia tana zaune ta rafka tagumi ta rasa meke mata dadi farouk ya shigo ya zauna ya mata magana bata amsa mashi ba yace zarah na lura dake tunda nazo gidan nan bakya min magana ko wani abu na maki ta kalleshi tace niko me zaka min baka min komi ba yace Amma meyasa bakya min magana tace maganar ne bata kama ba kuma da yake ban cika zama a palour ba shiyasa ta mike zata shiga ciki ya tashi yasha gabanta yace zarah inaso muyi magana dake tace gashi kuma akwai abinda zanyi yanzu taci gaba da tafiyanta ze riketa tayi saurin ja da baya tace kada ka kuskura hannunka ya taba jikina duk maganar da zakayi ina sauraranka yace zarah dama ba wani abu bane illah tace ka bari se anjima ka fada min koma miye yanzu akwai abinda zanyi ta shige ta barshi nan wurin [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD haka zarah ta kwana cikin rashin kwanciyar hankali saboda abinda ya faru tsakaninta da siyama ta rasa ina zata sa kanta Washe gari haka ta tashi wata iri da ita ta gama shirinta tsaf suka tafi tana isa ta tafi ta samu siyama siyama ta canza fuska zarah tace ya Naga kina ta shan kamshi tayi shiru bata ce mata komai ba zarah tace haba siyama duk yanda muke dake tun muna Yara ba muyi fadan se yanzu da girmanmu zamu samu matsala Siyama ta mike tace se kiyi ni kinga tafiyata ta bar zarah nan zarah ta shiga ciki haka ta zauna har suka tashi ta tafi gida idon nan ya ciko saboda kuka kowa ya kalli zarah a cikin yana yin nan yasan tana cikin matsala tun tana bin siyama har ta hakura Ta shigo zata shiga gida ranar ta dawo da wuri ta shiga ciki mommy bata nan ta shiga dakinta ta kwara ruwa tayi alwala tayi sallah Ta dauko abinci zata ci ta tasa shi a gaba ta rafka tagumi ta kasa ci se hawaye da take yaya farouk ya shigo tace yaya farouk lafia zaka shigo min daki in wani abu kake so base ka kirani ba yayi murmushi yace ai na riga na shigo yazo daf da ita ta matsa ya riko hannunta ta fisge ta daukeshi da mari tace ina me umurtarka da kada hannunka ya kara taba jikina idan ka saba gogayya da matan banza to ni ba haka nake ba dan iska kawai Rike da fuskanshi kawai yayi yana mamakin yar karamar yarinya kamar wannan ta mareshi yace ni kika ce ma dan iska to bari in nuna maki yayi kanta gadan gadan ta fara zagaye dakin ya samu ya riketa ya wurgata kan gado ya bita tace dan Allah kada ka cutar dani idan ka cutar dani Allah baze barka ba yace ke kika nemi haka shiyasa zanyi maganinki tace dan Allah kada ka hukuntani ta wannan sigar ka temaki taga ba sarki se Allah ta fara kokarin kwatar kanta Duk tabi ta jikata karfinta ya fara karewa dawowan da zatayi ta ganshi yanda yake ta fasa kara ta sume Allah ya temaketa mommy ta dawo daji karanta ta shigo dakin ta kai mashi duka tace farouk rashin mutuncin naka har ya kawo cikin yaran gidan nan to ba zan dauki wannan iskancin ba ka riga ka aikata mata ko yace a'a mommy cikin daga murya tace to me ya kawoka dakinta gashi bata numfashi me ka mata dede lokacin daddy shima ya shigo dakin isowarshi gidan kenan yaji hayaniyar mommy [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD daddy na shiga yace lafia ya dubi zarah dake kwance yace meke damunta farouk yace matsala aka samu daddy amma be kasance ba yayi kan zarah ya dagota ya ganta a sume ya dauki ruwan data aje ya antaya mata ta farfado tace dan Allah ka temaka min Ta fashe da kuka tace daddy ya bata min rayuwa ko ya dagota yace a'a zarah Allah be bashi iko ba ta kara fashewa da kuka tace daddy kade boye min ne Ya kama mata hannu yayi palour dinshi da ita ya zaunar da ita har a lokacin kuka take bakon da suka zo da daddy me suna alh sharif yace wai meke faruwa daddy ya bashi labarin komi da yan wahalhalun data sha a gidan alh sharif ya tausaya mata matuka ya juya daga kallonta ya koma kan alh sharif yace idan ba zaka damu ba ina so ka bani auranta in aureta da sauri zarah ta dago ta kalleshi tace a'a daddy ta tashi ta fita da sauri ta bar dakin ta koma dakinta ta fashe da kuka Tace me kuma yake son shirin faruwa dani da wanne zanji yama za ayi wanda ya haifeni yace yana so ya aureni baze yuwu ba ta kara lafewa ta saki wani kukan Tana kwance ta kasa yin komai ta rasa meke damunta me zatayi taji dadi a ranta ta mike ta dauki qur'ani ta fara karantawa farouk be daddara ba ya faki idon mutane ya kara shigowa dakinta ta mike da sauri tace meya kawoka dakina kuma na tsaneka bana son ganinka yace zarah ki tsaya in fahimtar dake bana son jin komi daga gareka yace oh zarah meyasa ba zaki tsaya muyi magana ta fahimta ba ki fahimceni mana bawai na aikata haka da niyya bane tace fahimtarka na wofi ai beda amfani tsayawa fahimtar irinka azzalumi da be san darajar mace ba Allah ya isa tsakanina dakai tunda har ka zalunceni dan haka ka fitar min daga daki taga beda niyyar fita ta hankadashi waje ta maida kofar ta rufe ta duke a kasa ta saki wani irin kuka me tsuma zuciya salma ta shigo dakin tace kizo daddy na kira ta fita ta shiga dakin yace zarah meyasa kika fita tace daddy nide burina kada ka yarda na aureshi yayi murmushi yace zarah ba abinda alh sharif ze nema na hanashi UKUBA Na EASHA MD dan haka zarah kiyi hakuri kimin biyayya ki aureshi matarshi daya be taba haihuwa ba yana neman haihuwa ruwa a jallo har yanzu Allah be bashi ba kuma matsalan daga matarshi ne gashi yana so yayi auran ta hanashi saboda na sanki da addu'a shiyasa na amince da auran koda ya nema a dede lokacin aka kira mommy ta fita zarah cikin kuka tace daddy kana so inyi auran da zanje in dawo ne kana so abinda ya faru da mahaifiyata ya faru dani Yace a'a zarah tace to meyasa ka amince zaka bashi aurena daddy ka tausaya min mana inaso na auri wanda nake so a raina mommy ta dawo daddy yace kina da wanda kike so ne tace eh daddy akwai wani hisham da nake so mommy tace wanda kika rinka haduwa dashi a waje ai be taba zuwa gidan nan ba kada ka bashi ita saboda bana kirki bane shima na binciki halinshi ai alh sharif din kawai zaka bata yace to kinji ance halinshi beda kyau kinga ko alh sharif mutumin arziki ne zaki ji dadin zama dashi beda matsala ko daya daddy babba ne fa mommy tayi dariyar mugunta tace yaro yaro ne Yarinya