Sashe 21
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yayi shiru zarah da sauri tazo ta rungemeshi ta baya tana kuka tace yaya deen dan kai kawai aka halliceni ina cikin kunci da damuwa ka yafe min I LOVE YOU yaya deen inaso na rayu dakai har karshen rayuwata ya juyo da ita har jikinshi na rawa yace da gaske kike ba mafarki nake ba tace yaya deen da gaske nake ya kara riketa hawaye ya gangaro mashi yace meyasa kika rinka guduna tace yaya deen daddy ne yamin miji yace no zarah bana son ji tace yaya deen yanzu dede nake da na kwaci yancina yaya deen kai kadai zan aura na rayu dakai har karshen rayuwata yace zarah meyasa daddy zeyi haka [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD zarah kada ki bari daddy ya rabani dake pls saboda ba zan iya samun sauki daga soyayyar da nake maki ba idan na rasaki zan iya rasa rayuwata idan kika bari daddy ya rabani dake zuyata zata fashe kin san soyayya tana da radadi kece zaki daga tushen soyayyar nan zarah kin kasance wani bangere gagarumi a tare dani a rayuwata zan soki har abada Tace yaya deen kayi shiru zanyi iya kokarina fatana Allah ya shige mana gaba yace zarah ba zan iya yin komi ba tare dake ba kuma nayi amanna da maganarki ta lumshe idanunta wasu hawayen suka zubo mata tace yaya deen zan zauna dakai har na karshen rayuwata yace Allah yasa zarah kinga gidanki tashi mu zaga kiga idan akwai tsarin da be maki ba a canza shi duk ya koma kamar wani zautacce tace ka bari se wani zuwan na gani nide yanzu ka maidani gida ya bata rai yace inde baki tashi ba zanyi kuka kuma ba zan maidaki gida ba sede ki kwana a nan ta mike da sauri suka fara zagawa gaba daya tsarin gidan ya mata ya hadu sosai yace ya kika gani tace yayi sosai Tace mu tafi yace haka zaki fita ki koma gida kowa ya ganki haka yasan kinyi kuka idon kawai ta wanke tace mu tafi suna tafiya yace yanzu ina zan kaiki tace maidani gida kawai Yako maidata gida tana shiga taci karo da goggo dije tace har kun dawo tace a'a kaina ke ciwo ni kadai na dawo tace ayya sannu je ki kwanta ki samu ya sauka Tana shiga ta kira number din siyama tana dauka tace kawa na riga na wuce gida tace eh nima gani nan yaya deen ya daukeni ze maidani tace au wurin party din ya koma tace eh dama shi ya kawoni tace to kenan kin san komi da tafiyar da yayi dani kenan tace eh zarah amma idan na maki laifi kiyi hakuri saboda naga halin daya shiga kuma be boye min komai ba shiyasa nayi haka dan ku hadu zarah taja dogon numfashi tace shikenan se gobe idan kinzo tace gobe ba zan samu zuwa ba zarah kimin afuwa tace shikenan ba damuwa bye Washegari daurin aure ansha biki an kai amarya gidanta lafia se fatan Allah ya basu zaman lafiya da hakuri Zarah tana zaune da goggo dije tace amma de ba zaki tafi ba tace dama ba zan tafi ba saboda matsalanki yanzu ma nake so na shiga wurin yayan tashi ma muje suka shiga da sallama zarah ta samu wuri ta zauna goggo dije tace se naji labarin zaka aurar da zarah yace eh wllh tace a gaskia yaya ka janye maganar nan duka duka yarinyar nan nawa take da zaka aura mata babban mutum yace wato karana ta kawo kenan tace a'a ba maganar kara Yace zarah so kike na zaman karamin mutum tace a'a daddy ni bana sonshi ne mommy dake zaune ta rafka salati tace zarah ashe bakida kunya duka yaushe kika girma ke nan har kin san so goggo dije tace ya za ayi kuwa ba zata san so ba ai dole taji abinda take so kuma taji abinda bata so tunda an halatta mata zuciya Daddy yace gara ma kuyi hakuri dan aure ba fashi ya kira alh sharif suka gaisa yace yau muna laraba ko to na rage bikin ranar asabar za a daura aure zarah ta daura hannu a kai ta fasa ihu tace na shiga uku za a min auran dole wllh ba zan yarda ba ta tashi da gudu ta shige dakinta ta datse ba bugun da goggo dije ba tayi ba ta bude amma taki budewa kuka kawai take kamar ranta ze fita shiru shiru har dare taki budewa goggo dije ta kara zuwa tace zarah dan Allah ki bude kinga baki ci abinci ba kada kija ma kanki taki budewa har safiya gaba daya harda su gaje sunzo suna rokonta ta bude amma taki budewa har yamma tayi se fama ake da ita a ranar alh sharif ya kawo invitation card ya tadda wannan badakala gashi har ya fara tura ma abokanshi na nesa da text goggo dije ta kira aunty a waya tace kome kike ciki kizo yanzu dan zarah ta rufe kanta gashi rabonta da abinci tun safe tace gani nan zuwa ba a jima ba se ga mommy da goggo rabi nan aunty tace duk me ya kawo haka goggo dije ta fada mata komi tayi magana tace zarah bude muyi magana tace ba zan bude ba sede in mutu a haka in huta kuma ku huta alh sharif yace a balla a kofar kawai ba bata lokaci daddy ya kira su bala Aka fara kokarin balla kofan [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD ana ballawa aka bude suka shiga kamar mahaukaciya haka ta mike tsaye akan gado ta wawuri wukan da ta yanka lemo jiya da safe Tace duk wanda yayi kokarin zuwa wurina zan kashe kaina wadanda suka tsaneni sun huta da ganina a doron duniya aunty tace pls zarah kada kiyi haka kefa musulma ce goggo dije taja tsaki tace kuna tunanin ita sakarya ce da zata yanka kanta ai tun kan a haifeki muke da wayau ta tunkareta zarah ta yanka hannunta jini ya fara zuba goggo dije taja baya tace kar wanda ya matsoni aunty tace zarah kada kimin haka pls ki aje wukan mommy tace ku kyaleta mana ta kashe kanta din goggo dije ta bita da wani muguwar kallo daddy yace zarah ki bani wukan dan Allah Shima ya tunkareta ta kara yanka dayan hannunta yace subhanallahi tace ku fita bana son ganin kowa a cikinku kuma ba zan fasa yanka kaina ba se in har an janye auran nan an barni da wanda nake so daddy yace haba zarah kiyi hakuri dan Allah tace yanzu kuka san da bani hakuri aunty tace zarah dan Allah ki dena yanka jikinki tace in dena yankawa kina damuwa da yanke jikina da nake ne kin damu da rayuwata ne a matsayinki na mahaifiyata kika sakeni ina gararanba abinci da zanci a gidan ubana ya gagareni kuma kina sane da UKUBAN da nake sha a matsayin inada uwar da zata nuna min gata amma kika kasa kula dani wane bakar wahala ne bansha ba a rayuwata tun ina karama har girmana amma kinje kin rike yaran da ba naki ba da kyau amma kin banzatar da wanda kika haifa ba wanda ya tausaya min se inna gaje inna juma ba zan manta dasu ba se yaya deen da siyama wadanda suka nuna min kauna ta gaskia a gidan nan haka na rasa wanda ze kaunaceni a matsayinsu na wadanda na hada uba daya dasu shiyasa ba zan manta da yaya deen a rayuwata ba ya tausaya min ya kaunaceni a lokacin da iyayena suka kini se a lokacin aunty ta tuna da kamal ta fara nemanshi a waya [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD yana dauka tace kamal dan Allah kazo yanzu muna gidansu zarah yace meya faru ta mashi bayani da sauri ya kashe wayan ba jira komi ba ya dauki key din mota ya taho yana isowa tace kamal ka temaka ka lallaba min zarah kada ta kashe kanta ya isa wurin yace haba zarah da iliminki da wayonki ki dau wuka kina ikirarin zaki kashe kanki kinfa san hukuncin wanda ya kashe kanki kina da ilimin addini fa zarah ke ba jahila bace cikin kuka tace yaya deen gara na kashe kaina na huta saboda rayuwata bata da amfani ba ranar da zanyi farinciki yace zarah kaddaranki ne haka kowa da irin tasa kaddaran tun farko Allah ya riga ya rubuta rabon bawansa na arziki ajalinsa da duk yanda ze gudanar da rayuwa tun kafin yazo duniya kuma tsari ne da ba wanda ze iya canzashi se Allah kuma kin sani idan kika kashe kanki ya kike so nayi zarah ta duke akan gadon ta saki kuka Da sauri suka karasa dakin ya amshe wukan hannunta alh sharif yace na janye maganar auranki zarah Allah ya baki wanda zaku zauna lafia na gari ta saki ajiyan zuciya aunty ta riketa tace ji yanda duk kika jima kanki ciwo tashi muje asibiti tace ba inda zani daddy duk yaji kunyar alh sharif yace kayi hakuri kasan ka haifi dane baka haifi halinshi ba yace kada ka damu ba damuwa yace zarah ki tashi a kaiki asibiti kada ki samu matsala taki tankawa Shiko kamal dadi duk ya cika zuciyanshi mommy ta cika tayi fam alh sharif yace ka bar mamanta ta tafi da ita gidanta ta riketa yace to na amince halima ki tafi da ita zarah tace daddy ba inda zani a gidan nan zan zauna aunty tace zarah so kike kici gaba da fuskanta matsala mommy tuni ta fita a dakin su daddy ma sun fita Tace a'a aunty so nake in zauna dan se na karya alkadarin matar nan aunty tace a'a zarah nafa san halin matar nan nasan wacece ita duk yanda zaki so ki canjata she will never change tace aunty addu'a kawai nake nema dan sena temaki mahaifina ko ba komi shi ya haifeni kuma yana kokarin yaga ya kyautata min amma se ta shiga ta fita Goggo dije tace na goyi da bayan ki bar zarah a gidan ina nan nima se munga abinda ya ture ma buzu nadi tace shikenan zarah ki yafe min ba