Sashe 2
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sa'a ba a koya min raina manya ba dase na rama ya fita yabar baffa a nan shima ya fita cikin kunan ran abinda bashir ya mashi ya isa asibiti duk ya kwashe yanda sukayi da alh bashir halima cikin kuka ta fada jikin Amma ta saki kuka tace yanzu Amma ya zanyi baffa yace kada ki damu Allah ya bamu kudin da zamu kula da ita ba zata taba maraicin mahaifi ba halima cikin kuka tace ai baffa ba shi bane matsalan lokacin da zata tashi ta nemi mahaifinta kaga yanda ya shegantata kowa ma ze shegantata baffa yayi dogon ajiyar zuciya ba wanda ya kara cewa komi a dakin da yamma sega kamal ya shigo shida abokinshi ya gaida Amma ya gaida halimatu yace aunty nazo kara ganin matana tayi dariya tace ai gata nan tana jiranka ya dauketa Amma tace haba yaro gani sabuwar jini me zakayi da wannan yarinyar ai gara ka bar ma tsoho ita se a bar ma alh ita cikin daria yace habade ai wannan itace sabon jini gata kyakykyawa cikin daria Amma tace aiko baka san kyau ba yaro yace to nide ita nake so a haka babanshi ya shigo yace to kamaludden dama kana nana lalle ana son baby din nan suka gaisa yace ya jikin tace yayi sauki ya kalli kamal yace wato baby tasa kana magana halima tace tofa ashe sirikin nawa miskili ne yayi murmushi daddy yace mijin naki yazo ne tace a'a yace to ba a fada mashi bane tace an fada mashi beda lokacinmu ne kuma yana zargin yarinyar ba tashi bane daddy yace kamar ya? tace haka yake nufi, yace to ya maganar auranki? tace ai ya sakeni , yace insha Allahu na maki alkawari zan rike maki ita kamar ni na haifeta, ya juya ya kalli Amma, yace amma inaso ki fada ma baffa ina so ya bani izinin neman halima na aura, saboda yanzu shekaran matana uku da rasuwa, wurin haihuwa har yanzu ban kara aure ba, yarana hudu kamal ne na farko, Amma tace to zan fada mashi, naji me zece, satinta daya a asibitin,, aka sallameni, [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 0 yarinya taci sunan Amma fatima wanda suka lakaba mata zarah anan gidan aka yi suna baffa da kanshi ya siya raguna manya guda hudu anyi suna na duk wani me gata ze samu baban kamal da kanshi ya bugo mata calender da manyan jakunkuna wanda hotonta ke kai ansha shagalin suna sosai halima na zaune ita da Amma zarah na hannun Amma baffa ya shigo suka mashi sannu da zuwa ya amsa ya samu wuri ya zauna halima ta tashi ta dauko mashi ruwa mai sanyi da kunun aya ta aje a gabanshi ta koma ta dauko mashi abinci ta zuba mashi ya amsa yace yauwa auta sannu Allah yashi maki albarka ta amsa da Amin bayan ya gama cin abinci yace auta tace na'am baffa yace ina son magana dake ta maida hankalinta gareshi yace kan wannan bawan Allah ne baban kamal ni hankalina ya kwanta dashi amma ba zan shiga hakkinki ba idan har kinga kina son zama dashi falillahil hamdu kanta duke a kasa tace baffa kaga fa zarah karama ce yace ai dama ze daga kafa har zuwa ki yayeta amma fa bance ki aureshi dole ba tace to haka suka ci gaba da kwanciyar hankali ita da zarah suna zaune kamal ya shigo amma tace kamal ne yace eh Amma tace to ya babanka da kannenka yace suna lafia Amma tace to madalla yasa hannu yace Amma bani matana tace gata dama duk tasa na gaji yayi murmushi ya zauna ya gaida halima tace daga ina yace daga gida kuna lafia ko yace lafia lau nan ya gama firanshi sannan ya tafi alh aliyu yazo ya aika kiranta ta fito ta sameshi suka gaisa yace ina diyar tawa tace tana cikin gida tace ka shigo ciki ta bude masu sitting room ya samu wuri ya zauna ta fita ta kawo mashi juice ta tsiyaya mashi ya amsa yace na gode bayan yan mintuna yace to halima me kika yanke nide na fada maki sunana kuma ni dan garin bauchi ne aiki ya ajeni a nan na comapany na dake nan garin kaduna kuma yarana hudu kamal khadija aliyu muna kiranshi haidar se auta da taci sunan mahaifiyarta aminatu muna kiranta da minal kinji takaitaccen tarihina me kika gani zaki aureni tace to zan gani amma inada karamar yarinya da bazan iya aure a yanzu ba [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 0 alh aliyu yace halima dama ba za ayi yanzu ba se zarah tayi wayau tace zande yi shawara yace to Allah yasa shawarar taki ya zamto anyi amanna dani tade yi murmushi yace kina da sha'awan ci gaba da karatu ne dan a tsarina inaso inga mace ta samu ilimin boko sosai in aka cire na addini sbd ta wuce raini a gun koma waye ta nisa tace abinda ke raina kenan ina da burin inga na samu ilimin boko se gashi ina gama secondary sch aka aurar dani yace to insha Allahu na maki alkawarin cika maki burinki na samun ilimin boko insha Allahu zan neman maki tace haba dawainiyar ma da ka mana ya isa haka base na Kara daura maka wani nauyin ba dama na riga na fada ma baffa inaso na koma makaranta yace halima kada ki damu ni nasa kaina ai mun riga mun zama daya yace ni zan wuce tace to na gode ya tafi ta shiga gida suna zaune amma tace wa auta ya kike ciki ne da maganar baban kamal halima tace nifa amma bana son in kara wani aure amma tace to haka kike so so kita zama tace eh tace ai kin san abinda baze taba yuwuwa bane miko min wayata gashi nan ta mika mata ta danna number din babban danta yusuf dake abuja can yake aiki dama yaranta uku yusuf ahmad se auta halima yana dauka suka gaisa tace na kawo maka karan auta ka mata nasiha tunda kasan yanda ahmad keda zafi son da yake ma auta yana ganin taci wuya yaki samin hannu goyon bayanta yake yace bani ita ta mika ma halima yace haba auta kiyi hakuri ki auri mutumin nan sbd beda wani mugun hali zaki ji dadin zama dashi tunda beda mata bare kice zaki sha wahala kinga ke kadai garemu mace ba zamu so mu ganki a gida ba tace hakane yace to kiyi tunani akai zamuyi magana suka yi sallama tace haba amma meyasa zaki fada mashi tace na fada din yaya ahmad ya shigo yace auta lafiya na ganki haka amma tace sbd an mata fadan aure yaya ahmad ya bata rai yace Amma a kyaleta mana zuwa wani lokaci cikin fushi amma tace ba za a kyaleta ba ku tashi ku bani wuri tun kafin in saba maku suka mike da sauri suka bar wurin [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 0 halima ta gama ajema baffa komi a gabanshi ta juya zata tafi yace dawo ina son yin magana dake ta dawo ta samu wuri ta zauna yace auta ke kuwa ba zaki tausaya ma kanki ba kiyi auranki ki gode ma Allah mana na ni'imar daya baki daga fitowanki fa Allah ya baki miji amma zaki butulce mashi mata nawa ke kuka da idanunsu akan Allah ya basu miji amma basu samu ba kuma basu fasa rokon Allah din ya basu ba ko so kike damar da kika samu ya kubce maki Amma tace fada mata de in damar ya kufce ai se mu zauna ga kuguna ga nata muna jira tsawo tunda haka kike so ko dan yaran nan nashi da suke sonki suke son yarinyar nan taki ai ai kya tausaya masu baffa yace aikuwa suna nan biye da ita to tun wuri ki zauna kima kanki fada tun kafin wani ya maki Amma tace ai zawarcin ke bata sha'awa ko dan ki shusa ma wannan tsohon mijin naki haushi yaga kin samu miji da wuri ai kyayi auran baffa yace a'a komi bawa zeyi yayi dan Allah ba dan wani abu ba cikin damuwa tace baffa naji na dauki shawaranka sede tunanin zarah nake bata yi wayau ba yace dan wannan kada ki damu ai dama renonta yafi a wurin mahaifiyarki komi ita ke mata kafin a ganta tare dake a ganta da mamanki dan haka ba abin damuwa bane tace to shikenan yace tashi ki tafi Allah ya maki albarka ta miye ta shiga dakinta ta kira alh aliyu suka gaisa shiru ya dauki lokaci ba wanda yace komi can yace halima ya akayi tace dama ta kuma shiru yace dama me fada min inji tace na amince muyi aure yace da gaske kike tace eh yace kai na gode ma Allah kuma Allah ya shige mana gaba tace Amin sannan inaso kamin alfarma yarinyata ta cika shekara 2 yace haba halima yayi yawa zande bari tayi shekara 1 yanzu zan samu inga kin fara karatu tunda gashi an fara saida jamb form se a siya kinga kafin bikin kin fara karatun tace to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi yace Amin [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 0 tana zaune tana canza ma zarah kaya kamal ya shigo tare da kannenshi yazo ya dauki zarah suka gaidata halima tace minal harda ke akazo zo nan ta daurata akan cinyarta tace ya gida lfy lau ya makaranta yau ba aje ba tace naje ajinki nawa tace nursery 2 tace iye ashe yarinyana ta zama yan mata kefa khadija tace primary 6 tace ashe de yan matan nawa sun girma haidar fa yace primary 5 tace to Allah ya taimaka minal tace to aunty baki tambayi yaya kamal ba tace hakane kuma khadija tace ai shi babba ne jss3 yake yace ma ya kusa gamawa ko yaya yace eh tayi daria minal tace aunty ina son yarinyan nan zaki bani tace eh na baki ta buga tsalle tana murna tace na samu kanwa nima na zama babba tace yaya kamal bani kanwata yace to sarkin surutu ya daura mata akan cinyarta yace