← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace to zarah kin samu mijin ne tace eh na samu mijin shiyasa nake so nayi auran na huta karaf a kunne mommy tace me kike cewa Zarah ta sunkuyar da kanta kasa tace tambayarki nake zaki bani amsa ko se na saba maki tace mommy aure zanyi ta saki salati tace duniya tazo karshe ke nan har kin san aure to inama kika hadu da mijin gashi bamu sanshi ba tunda be taba zuwa gidan nan ba tace eh mun hadu dashi a waje tace ban gane ba kina nufin a waje kike haduwa dashi shikenan ai ya gama dake Kin riga kin sakan mashi jikinki a titi Allah ya wadaranki zarah to bari kiji in fada maki ba auran da za a maki se anyi na salma ke ko husna da kike gani kanku daya da ita se anyi nata za ayi naki inma zaki cire son wani aure a ranki gara ki cire dan auran ma se naga dama zaki yi ta wuce ta barta nan zarah tace ta Allah ba taki ba ta mike ta shige dakinta Result na fitowa ba tare da bata lokaci ba ta fara cuku cukun fara neman gurbin karatu a ABU husna kuma poly nan hassada ya darsu a ranta tace ita bata yarda ba mommy tace yanzu ya kike so ayi tace sede muje school tare Daddy na dawowa haka ta shiga ta hau kuka tana ita bata so ta rabu da yaruwarta sede suje school tare daddy yace kira min zarah ta fita ta kirata suka shigo a tare yace zarah husna tace dole sede kuje school daya bata so ku rabu zarah tayi shiru a zuciyarta tace me kuma husna take nufi tabbas akwai wani abu a ranta [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD daddy yace zarah kinyi shiru baki ce komi ba tace daddy nafa riga na gama komi har admission kuma an bani course din da nake so medicine se kuma in fasa zuwa tun yaushe nake burin samun wannan ranar daddy yace zarah na sani husna ta kara fashewa da kuka daddy yace kiyi hakuri mommy tace wai yama za a tsaya ana lallabaki to ba zaki zaria ba saboda yarintarku tayi yawa ba zan bari kuyi nisa dani ba ina nan tare daku a gida kuje ku dawo in kwana daku zarah tace amma mommy naga salma har sokoto take karatu ni kuwa zaria ne kuma duk akwai dangi a can da Zan iya zama a wurinsu Mommy tace to ba zaki ba wato har kinyi girman da zaki fada min magana tace ni ba magana na fada maki ba ai.......mommy ta tsaidata tace yimin shiru yaruwarki na kuka ta nuna soyayyarta a kanki amma kin kasa tausaya mata daddy yace zarah kiyi hakuri da abinda nayi miki amma kimin alfarmar nan zarah ta share hawayenta tace daddy na yarda na hakura da ABU din Allah yasa haka shine yafi zama alkhairi yace ameen zarah Allah ya maki albarka tace ameen yace zaki iya tafiya ta mike ta fita tana share hawaye Husna na biye da ita ta kwashe da daria zarah ta kalleta husna tace kina tunanin zan barki ne ki tafi ki fini matsayi zarah tace husna dama nasan akwai wani abu a ranki hakanan ba zaki ce kina so mu zauna tare ba na barki da Allah seya saka min saboda baki taba min abinda raina ya baci sosai irin yau ba husna ta kara kwashewa da daria tace ai dama bacin ranki nake so shiyasa nayi haka au wai ko kin fara tunanin zan soki ne to in haka kike tunani ki cireshi a ranki saboda kullum kina sama dani a ko ina shiyasa ba zan taba sonki ba zarah tace wannan kuma ke ya dama na riga na barku da Allah husna ta kara fashewa da daria tace banza Zarah ta shige dakinta ta fada gado ta fashe da kuka tace mommy me na maku ku kyaleni hakanan UKUBA da tsanar ya isa haka daddy ya shigo ya taddata ya zauna kusa da ita ya dafata ta kwanto a jikinshi ta kara fashewa da kuka daddy yace kukan ya isa haka tace daddy kaima baka sona ne kamar yanda yan gidan basa sona yace zarah ina sonki ba yanda zanyi ne tace daddy meyasa kake sakaci da addu'a Addu'a fa kariya ce sosai muna rainata muna wasa da ita ya zaka zauna mace na juyaka kuma kaine a sama da ita ita ya kamata tama biyayya amma se ya zamto kai ke mata yace zarah addu'a dinku nake bukata matar nan ta wuce tunaninki tace kaima daddy seka dage yanzu ina ji ina ganin ka tauye min hakkina yace kiyi hakuri ta lumshe idonta wasu hawayen suka sauko daddy yace tashi muje ki rakani haka ta shirya suka fita da yake mommy itama sun fita yanzu a mota ma in banda kuka ba abinda take yi haka suka isa poly ya samu abokinshi suka gama magana yace ai ba matsala insha Allahu daga nan zuwa monday zata samu wannan ba matsala yace amma banji dadin abinda kayi mata ba yace nima ba a son raina haka ya faru ba ba yanda zanyi ne yace ai kana sakaci da addu'a ba dan haka ba ita din banza har ta isa gaskia ka dage da addu'a ka ware ma kanka lokaci na ganawa da ubangijinka kuma ina jiye maka hakkin yarinyar nan daddy ya kasa cewa komi Haka suka gama komi suka fito zarah har a lokacin tana hawaye ya juyo ya kalleta yace ina kike so in kaiki ta nisa tace gidansu kawata siyama yace nasha zaki ce wurin mamanki ta juya bata ce mashi komi ba yace ina ne gidan ta mashi kwatance har suka isa gidan Tana shiga gidan ta tadda siyama ta fada jikinta ta fashe da kuka siyama ta dagota tace zarah lafia taci gaba da kuka siyama tace wai miye pls ki fada min itama ta fashe da kuka ta daga zarah ta zaunar da ita ta fara kwala ma mamanta kira da karfi tana kuka mommy ta fito tace lafia kike min irin kiran nan siyama ta gansu suna kuka tace meya faru ta riko zarah tace zarah meya faru ta kwanta kan cinyar mommy tace mommy ba mun riga mun samu admission da siyama ba tace eh to shine su mommy seda suka san yanda suka hanani yanzu daddy poly ya samanmin saboda nan husna ta samu shine ta nuna bata son mu rabu Mommy cikin tausayawa tace kiyi hakuri komi me wucewa ne siyama tace mommy nima na fasa zuwa nan zarah tace a'a siyama kije mommy kisa baki kada ta fasa zuwa tace idan har ba inda zaki ba sede na fasa karatun zarah tace gaskia banji dadi ba idan kika yi haka Mommy tace zarah ba abinda zance tunda soyayyar da kuke ma juna daga Allah ne tace kuma ai abba zeyi fada mommy tace wai yanda abba be son bacin ran siyama siyama tace bari ma ki gani ta kirashi a waya ya dauka yace yar baba ya akayi ta kwashe komi ta fada mashi yace nan ya maki yanzu tace eh zanma samu daddyn siyama ya saman min yace to shikenan Allah ya temaka tace ameen na gode abba ta kashe wayan tace to kin yarda ba matsala ko zarah tace kinji dadi nima da Zan samu haka Nagode da kaunar da kike nuna min tace to ai kema kina sona tayi murmushi ta mike tace bari in tafi na bar daddy a waje tare suka fita Tace ina yaya hisham tace ya fita ko ya samu gurbi a zuciyar ne tace nade tambayeki ne siyama tace kede fadi gaskia bari mu Fata shiri a haka suka isa inda daddy yake siyama ta gaidashi zarah tace daddy tare muka samu ABU da ita itama tace ta fasa zuwa inda zani zata yace a'a siyama ki tafi kada ki damu tace ai abbana ya riga ya yarda yanzu ka saman min anan yayi waya da abokinshi ya kara neman alfarma yace ba damuwa ta hada komi nata yayi mashi godiya da zasu tafi ya mika ma zarah kudi taki karba ya matsa mata seda ta amsa ta amsa ta mashi godiya suka tafi daddy yace saura wurin mamanki tace ba zani ba gida zamu koma akwai abinda zanyi bece mata komi ba ya dauki hanyar gida [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD zarah sun fara karatunsu cikin kwanciyar hankali ba tare da ta samu matsala ba tuni ta canza akala zuwa mass comm mommy kuwa tana nan ba tare da ta canza hali ba zarah tuni da saba da lamarin mommy yanzu baya damunta abinda tasa gaba kawai take yi Suna tafe da zarah zuwa capteria siyama tace ga mutumiyarki can Ita de ba abinda ya dameta da karatu kawaye da fasion kawai tasa a gaba zarah tace ai nan gaba tayi karatun ita de ta sani Siyama tace da kin rinka mata fada tace fada fa kika ce ta ya zan mata fada kina ganin fa abinda suke min taya zan mata maganar da ze kara tunzurata siyama tace to wai ba zasu saduda hakanan ba zarah tace sude sani ni yanzu bata kansu nake ba Siyama tace ai kema kina bani haushi tace to me na maki tace saboda yanda kika manta da aunty mahaifiyarki ce fa zarah tayi murmushi tace siyama kenan ban manta da aunty ba ai ita ta manta dani wake kula dani in ba ke da yaya deen ba itama ina sane da ita siyama tayi murmushi tace shikenan Haka suka ci gaba da rayuwa komi yazo ya wuce ta dawo daga school sun shiga palour suka tadda bako husna ta washe baki tace la yaya farouk kaine a gidanmu yace aikuwa husna kece kika girma haka tace kai yaya farouk Yace hakane mana tace ai kaima ka kara girma malesia ta amsheka yace ko tace sosai kuwa zarah ta wuce ciki ya bita da kallo yace ya wannan fa tace yar nan gidan ce Yace ya akayi ban santa ba tace haba yaushe rabonka da gidan nan ai ba zaka santa ba muma dan muna zuwa
Chapter 17 · 0% Book details