Sashe 12
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata leda ta amsa ya tafi suma suka wuce siyama tace tun da aka fito break nake nemanki amma ban ganki ba suka shiga class suka zauna Zarah ta bude ledan ta saki murmushi tace kai yaya deen ya kyauta kamar yasan mu biyu ne ya siyo komi biyu siyama itama dariyan tayi kowa ya dau nashi suna ci suna fira gwanin sha'awa husna ta shigo ta kallesu ta saki tsaki tace banzaye siyama tace banzaye kuma ta mike zata bigi husna zarah ta riketa dan tasan siyama ba hakuri Tace siyama kiyi hakuri kada kiyi fada da ita in ba haka ba ni zaki ja mawa a gida ta koma ta zauna tace saboda ke na kyaleta tace meyasa kika koma kika zauna kinji tsoro kenan zarah tace kada ki kulata kawa tace ai na kyaleta Husna ta kalli zarah tace ina bakin ciki naga kina cikin walwala ina bakin cikin inga wani ya rabu dake dan haka dole se kin rabu da siyama zarah kallonta kawai tayi ba tare da tace mata komi ba sede tayi murmushi ta samu wuri ta zauna siyama tace waike zarah meyasa kike zama wannan ta rinka juyaki tace to ya zanyi idan nayi magana se kiga mommy ta fara dukana ta fara hawaye siyama tace kawata kiyi hakuri tace dama ya zanyi [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 siyama tace to ke meyasa ba zaki koma wurin mamanki ba tace baki ga bata damu dani ba shiyasa ma bana tunanin naje gidan itama baki ga sede tazo nan ta ganni ba Kuma kinga duka yaran data haifa duk fa ban taba zuwa sunansu ba sede naji sunansu ko in tazo dasu kinga wadda ta haifa hauwa'u jidda seta haifi twince muhsin da muhsina kinga ba wani shakuwa a tsakanina dasu a matsayina na yayarsu sede fa in nan suka zo na gansu kinga ma da yake yanzu sun shiga school yaushe rabon dana gansu siyama tace to ki koma wurinta tana sonki fa zarah tace kona koma se daddy yazo ya daukeni da mommy ta zugashi shiyasa kullum yaya deen sede yayita bani hakuri Komawarsu gida husna na zaune tare da mommy tace mommy yanzu zarah ta samu kawa baki ga yanda take wulakantani ba yanda kika san ba gidanmu daya ba ta zauna taci gaba da yima zarah fanfo mommy tace kira min ita ta shigo ta kirata Ta zo ta duka tace mommy gani tace matso nan ta matsa ta murda mata kunne ta saki ihu tace wato ke nan har kin girma kin san kanki kin san ki wulakanta yaruwarki kuma ina so tun wuri ki rabu da yarinyar da akace kina tare da ita zarah tace to mommy itama fa tana da kawayen ta kara murde mata kunnen tace au in saki abu kice min ai itama tana dasu to banga damar cewa ta rabu dasu ba ke nake so ki rabu da ita da sauri zarah tace to burinta taga ta sakar mata kunnen ta saketa tare da rankwashi tashi ki bani wuri ta mike ta fashe da kuka mommy tace au kuka kike zo nan ta fara gogen hawayen tace a'a tace dan kinga ban bigeki ba to yanzu zan bigeki kiyi me dalilin tace a'a mommy kiyi hakuri wuce ni ki ban wuri ta shiga daki taci gaba da kuka Ga bikin khadija yazo gida ya cika da yanuwa zarah ko taji dadi ji take kamar gidan yayi ta zama a haka saboda ta samu ta sake idon mommy be kanta sena hidima ta nuna murnarta a fili na ganin khadija za tayi aure ta huta da zalincinta da sata aiki komi zarah miko min zarah dauko min tade kasa boyewa da ta shiga kitchen gaje tace zarah kwana biyu naga kina cikin walwala tace inna gaje ba dole nayi murna ba aunty Khadija zata yi aure na huta wahalana ze fara raguwa saboda aunty Khadija da kike ganinta muguwa ce kafin gaje tayi magana khadija tace sannu munafuka wato har murna kike zan bar gidan ko to ai tafiyar da zanyi ba wai na tafi bane gaba 1 zanzo gidan kuma idan naso a bani ke za a bani in tafi dake zarah tayi tsuru tsuru ta kalli gaje tace ke kuma da yake babban banza ce yarinya karama ta kawo maki gulma amma kin zauna kina saurare wama yasan iya lokacin da kuka dauka kuna gulmace gulmacenku ita de gaje ba tace komi ba khadija ta fito da zarah tace nice muguwa ko zarah cikin tsoro tace a'a ta samu silifas ta kama zarah ta matseta a cinya ta samu bakinta taita duka da silifas din zarah na kuka goggo dije tazo wucewa tace haba takwara me ta maki kike hukunci irin haka yee Tace ki barni da ita wai ni zata zauna tana murnar zan bar gidan nan goggo dije tace shine abin duka to ai dole ta tayaki murnar aure ko khadija tace haba goggo dije haka ake taya mutum murna har taje tana gulmana tana kirana da muguwa goggo dije tace in banda abinki duka nawa zarah take da zaki zauna kina bata ranki a kanta tace wai ya za ayi kice duka nawa take shekaranta fa 11 shine za a kirata yarinya kima dena sata tana daukan kanta yarinya goggo dije tace owo rashin kunyar naki har yazo kaina khadija to dan tace miki muguwa ai dan kina mata muguntar yasa ta fada maki haka haba wannan wane irin rayuwace tun tana karamanta wadda bata wuce goyo ba kuke azabtar da ita yanzu kuma ba zaku bari ta huta ba kunbi kun takura mata ko ita ance maku ba haihuwarta akayi ba koda kike ganin auranki za ayi baki wuce yanzu in zaneki ba khadija ta hau kunkune goggo dije ta kai mata duka tace kin sani bana daukar raini khadija ta fasa ihu mommy data fito ta karaso da sauri tace lafia mutane suka yo wurin Goggo dije tace ni da ita ne dukanta nayi mommy tace duka kuma wane irin duka tace dukan da kika sani ta riko zarah dake kuka ta daga fuskanta tace jibi fuskan yarinya yanda yayi ja ta samu yarinya ta hau zuba mata silifas a fuska ita in aka mata zata ji dadi da Zan mata magana ta nemi ta min rashin kunya ni tsararta ne khadija tace mommy zagina fa tayi shine har goggo dije zata bigeni mommy na juyowa zarah bata ankara ba taji saukan mari ta gigice ta saki kara goggo dije bata tsaya bata lokaci ba ta dauke mommy fa mari tace baki da adalci hafsa kin goyi bayan yarki akan yar rikonki mommy ta rike kuncinta tace ni kika mara tace na mareki zata riko goggo dije hajia mairo ta riketa tace miye haka dambe kuke so kuyi ko me da girmanku da komi goggo dije tace hajia ki barta tazo akan wane dalili zasu matsa ma yarinya Hajia mero tace dije ya isa mommy tace wllh ba zan yarda da cin mutunci ba ai dama kun dade bakwa kaunata shiyasa nima bana kaunarku me za ayi da dangin miji irinku goggo dije tace me aka maki na rashin kauna kiri kiri kin rabamu da danuwanmu duk baki gani ba ko da yake laifi tudu ne taka naka ka hango na wani ai kinde ji kunya ace kishin mahaifiyar yarinya ya dawo kanta me zaki dauka a jikin karamar yarinya Mommy zata yi magana hajia mero ta hanata magana tace ya zaki min haka bayan kina jin maganganun da take fada min goggo dije tace ai kin sanni banda hakuri shiyasa ban cika so a shiga gonata ba hajia mero tace haba dije wai baki ga so nake maganar ta mutu ba kuma gaku duk kun tsaya kuna kallo kusa baki mana taci gaba dan Allah ku bar maganar nan mu samu a gama bikin nan lafia ai abin kunya ne ana hidimar biki ace ana tashin hankali duk wanda ya shigo se yasan abinda ke faruwa ai wannan tsari beyi ba da girmanku ta tasa mommy ta kaita dakinta ta dawo ta kira dije tace dan Allah dije ya wuce kada ki kara tada maganar tace ba zan tada ba inde bata tada ba kinde sanni in aka shiga gonata bani da hakuri tace hakane to amma kiyi hakuri ayi biki a tashi lafia tace shikenan ya wuce ta fita goggo dije tace ai dama jiranta nake makirar mata azzaluma [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 anci gaba da hidiman biki sede wasu ba cikin jin dadinshi suke ba anata shirin tafiya party kowa nata shiri harda iyaye mother's day ranar aka shirya Wanda kowa yaci kwalliya ya fito zarah tana kusa da goggo dije tace bari nima in shirya goggo dije tace kije ina duk abinda suke maki ko ance kije inda suke ke kyaje ki zamanki muyi zamanmu a gida nima kinga ba inda zani tace to goggo dije se in zauna bansa kayana ba harfa anko anyi min goggo dije tace yanzu dauki kayanki kisa kiyi kwalliyanki a gida ba zan hanaki ba amma maganar kice zaki wurin da suke ban yarda ba hajia safiya itace yayar su daddy se daddy sannan goggo dije se autansu kawu sunusi su hudu iyayensu suka haifa se yanuwa da suke tare dasu shi kanshi mahaifin daddy su biyu ne shida kanwarshi inna hafsi tana nan da ranta Hajia safiya tace haba dije ya zaki hanata zuwa wurin yanuwanta tunda hidiman biki ake ita se a barta gida kowa ya tafi goggo dije tace ai zaman gidan yafi mata sauki akan can saboda ba kyaleta zasuyi ta huta ba hajia safiya tace amma de kin san tafiya zamu yi mu barta a gidan ko goggo dije tayi daria tace ai yaya safiya ba zan bar zarah a gidan nan ba abinda zami ma mahaifiyar zarah mu faranta mata rai shine mu faranta ma zarah ko kin manta zaman halima a gidan nan ne wane kaunarmu ne bata yi ba Hajia safiya tace ai ba zan manta ba goggo dije tace to kinga dole idan muka ga wani nata cikin mawuyacin hali dole se inda karfinmu ya kare bare kuma