Sashe 11
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin bacin rai ya yanke hukuncin nan tace bacin rai dan rai ya baci se hankali ya gushe yaushe ze yuwu ka raba da da mahaifi gara ma ya dawo cikin hankalinshi yasan kuskuren daya tafka ya duba yaga halin da yasa yarinyar nan a ciki be tunanin idan har zarah ta san shi ya rabata da mahaifiyarta wane irin kallo zata mashi wane irin mutum zata daukeshi daddy yace hakane amma ina me kara baki hakuri kada kisa ma ranki damuwa insha Allahu komi zezo da sauki ta nisa tace Allah yasa yace Amin bayan doctor ya fito ya dubi daddy yace ranka ya dade muje office zamuyi magana yabi bayanshi bayan sun zauna yace alhamdulillah mun samu ta farfado a gaskiyan magana tana cikin damuwa ya mata yawa ya kamata ku rinka kwantar mata da hankali in ba haka ba zata iya kamuwa da ciwon zuciya a sakamakon damuwan dake addabarta ga ciki a tare da ita dan haka dole ta samu kulawa dan ta samu kwanciyar hankali a cikin zuciyarta yace insha Allahu za a kiyaye doctor yace to Allah ya bata lfy daddy ya mika mashi hannu tare da fadin ameen ya fita ya tadda amma tsaye se zagaye take ta kasa zaune ta kasa tsaye tana ganinshi tace ya ake ciki yace Amma an samu ta farfado mata bayanin da doctor ya mashi tace innalillahi wa inna ilaihirraji'un kaga abinda nake gudu ko daddy yace Amma insha Allahu ba komai kada ki damu ai komi yazo da sauki yace muje dakin da take ciki ya kira kamal yazo yace kana can ka takure se tunani kake ai addu'armu take bukata Allah ya bata lafia suka isa dakin tana barci amma ta isa kusa da ita ta riketa tace auta Allah ya baki lfy daddy yace ameen amma ya kamata kije ki huta ko tace a'a ina nan wayanshi ya hau ringing ya dauka daga can bangaren baffa yace yaya me jikin ta farfado ko yace eh baffa yace to gamu nan zuwa ba a jima ba se gasu sun shigo cikin dakin can ta farka ta fara baffa ka dawo min da diyata kada ka rabani da ita ka temaka min tana kokarin mikewa amma ta riketa tace amma ki roka min baffa kada ya rabani da ita idan aka rabani da ita ba a min adalci ba baffa ya matso kusa da ita ya rike mata hannu tace baffa kaine a kusa dani yace eh nine auta tace baffa meyasa ka kasa tausaya min yace waya fada miki bana tausayinki tace ba gashi ka rabani da zarah ba yace a'a ban rabaki da ita ba tace da gaske kake baffa yace kwarai kuwa auta nayi miki hakane dan in samu ki basu ita amma har cikin raina ba haka yake ba ki ga yarki a duk lokacin da kika so amma bana so kije gidansu dan kinga matarshi ba imani a tare da ita zata iya cutar dake ta daga mashi kai tana murna gaba 1 dakin sunji dadi daddy hankalinshi ya kwanta ganin hankalin matarshi ya kwanta ta sake [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 kwananta daya aka sallameta ta koma gida duk da haka tana cikin damuwan halin da zarah zata shiga tana zaune tare da daddy yace halima me ze hana ki fara aiki akan zaman nan da zaki rinka yi kinga koda damuwar bata fita gaba 1 ba zaki samu ya ragu tace idan na rinka zuwa su kuma yaran fa se inta barinsu gida su kadai se jummai yace na riga na yanke shawaran goggo rabi ba zata koma ba ta dawo nan kenan halima ta washe baki tace da gaske kake yace eh tace amma naji dadi sbd ina jin dadin zama da ita yace to zaki fara zuwa na baki dama ki zabi inda ya maki a cikin company ki zauna tayi murmushi yace da gaske nake halima sbd kin min halaccin da ba ko wace mace zata iya yinshi ba ba ganin idonki ba ko a bayan idonki ina fada kuma zanci gaba da fada fatana ki dauwama cikin farin ciki da walwala shine fatana halima itako zarah tun komawarta mommy ta kara salon ci gaba da gasa ta ba tare da tsoron Allah ba a tare da ita wanda gashi har shekaru sunja ba tare da ta canza hali ba kwata kwata ba alamun tuna mutuwa a tare da ita duniyar ce a tare da ita se fatan Allah ya tsaremu daga fadawa irin halin nan nata gashi har zasu jss1 zarah taso zuwa boarding har daddy ya yarda amma mommy ta kekashe kasa tace bata san wannan ba dole tana ji tana gani ta hakura tayi kukan har ta hakura tunda ba yanda zatayi dole sede hakurin shine takobin mumini watarana sede labari komi me wucewa ne inde da rayuwa se kaga ya wuce tana zaune sadiq yace ke indomie zanci tashi ki da fa min tana mikewa khadija tace idan kin gama nashi ki dafa min zarah tace to in dafa maku a tare mana tace nawa nake so ni kadai ta fita ta gama ta kawo mashi ta gama nata ta kawo mashi umar na kalla yace ya birgeni nima dafa min tace nafa gaji yace ni kike fada ma haka tashi tun kafin in bigeki haka ta gama ta kawo mashi mansir na shigowa yace wow yau bikin cin indomie ake ina nawa sadiq yace sede kasa a dafa ma haka shima yasa ta dafa mashi wurin zuba ruwan zafi a tukunya ta kwara shi a kafanta ta fasa ihu da gudu mansir ya shiga kitchen din yace lafia tace ruwan zafi ya zubar min a kafa yace garin ya tace nima ban sani ba ya kamo mata hannu ya fito da ita mommy dake zaune tace to kai kuma lafia naga ka rikota se kace makaho da dan jagora yace mommy konewa tayi ta bisu da harara ba tare da tace komai ba ya wuce da ita dakinsu da kanshi ya hau fifita mata radadi ya dameta se kuka take shiko se faman sannu yake mata yace kinga ma be tashi ba shima zuwa anjima zaki ji ya dena zafin mommy ta shigo tace gimbiya ya maganar aikena mansir yace haba mommy baki ga ta kone ba ta sanadinmu yanzu ina zata iya zuwa ai dole mu tausaya mata tace anki a tausaya mata din ta fita ta banko kofar zarah tace yaya mansir dan Allah kada ka fita in ba haka ba ba zata kyaleni ba kuma kafan na min zafi sosai yace kada ki damu ba inda zani yace bari naje palour ki dena kuka kinji ta taga mashi kai yasa kai ya fita tana zaune tayi shiru ita kadai kamal yazo ya sameta tace yaya deen yaushe kazo yace tun friday nazo tace shine ban ganka ba yace dawowan yamma nayi kuma kinga se a nan zan ganki tace kana zaria ta boyeka yace karatu ne tace haba yaya deen ko da da kake karatun nafi ganinka har kana service fa ina ganinka sosai yace kimin hakuri zan gyara kinga yau ma zan koma tace to ina aunty yace tana nan tama ce na gaisheki tace anya kuwa ta fara kuka yace oh zarah why are you crying don't cry clean ur eyes da kanshi ya hau goge mata yace zarah meke damunki tace aunty bata sona bata damu dani ba ba ban san me na mata ba ko dan taga tana da wasu yaran bata damu dani ba yace haba zarah waya fada maki aunty bata sonki aunty na sonki fiye da yanda kike tunani ba zaki gane ba se nan gaba ta kara fashewa da kuka tace nafi son aunty akan son da take min idonshi ya kada duk ta bashi tausayi yace bana son kukan nan naki tace na dena yace yauwa tace yan zuyanzu ma nana fara samun saukinsu aunty Khadija 2 weeks ya rage bikinta kaga na huta yaya mansir suna school matsalata yanzu mommy salma da husna yace suma wataran zasu dena [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD tace amma yaya deen kace ma aunty ta rinka kula da ni ba taita sakina ba yace kede zarah kina ganin aunty bata sonki tana sonki Yanzu aiki ne ya boyeta bata zama a gida amma kullum da tunaninki nake kwana take tashi Tana sonki fiye da yanda kike tunanin kullum cikin damuwa take a kanki tasha tasa abinci zata ci ta aje tana tunanin a wane hali kike ciki se munyi da gaske take samu taci Hawaye ya kara zubo mata tace infa baka nan bame kula dani se uncle ahmad da aunty falmata nake gani suma ba kullum ba kaga fa ko bikinsu da akayi banje ba seda na gansu tare yake fada min ita ya aura har ta haihu ma duk banje ba kuma sunan suna yan uwana danma Allah ya hadani da friend me sona komi tana min dan ma ina dan kaucewa banso na cika shige mata ace ina kwadayi shiyasa ma nake nesa da ita kuma tana sona sosai yaya Yaya deen yace ba nace in kika yi hakuri ba komi ze wuce ba ya ciro wani dan akwati ya mika mata yace gashi na amso maki glass din Ta amsa da murnanta tace kai yaya deen na gode kaga yanzu ma dana shiga class dashi zanyi amfani shi zan sa ta kara kallon glass din tana murna yace yaya akayi tace yaya deen ya birgeni sosai yafi na wurina kyau yace shima wancan yana da kyau siyama kawarta tazo tace haba kawata ina kika shiga ina ta nemanki zarah tayi murmushi tace gani nan tare da yaya deen ne tace la shine yaya deen din naki tace eh ta gaidashi ya amsa yace to a rinka fa karatu banda wasa kunji ko tace to yace ni zan wuce tace to yaya deen se yaushe zaka dawo yace sede nan da sati 2 zan dawo ta bata rai yace haba kanwata to na fasa ba zan kai haka ba tace inma ka kai haka ka dawo ba zan maka magana ba yace zanma dawo yayi masu sallama tare da mika