← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba yace inde baki je ba ba ruwana dake ba zaki kara ganina ba ya mike ze tafi ta rikeshi tace to zanje Yace yauwa ko kefa bana so ki zama me riko a ranki kinji tace to yace tashi mu shiga ciki in shirya ni zan ma kaiku Ta mike suka shiga ciki goggo rabi tace zarah kenan hukuma seda lallashi ko goggo dije tace ba lallashi zaneta zan rinka yi tace idan muka je can kema dukana zaki rinka yi irin nasu mommy tace eh mana tayi alamun kuka tace to bama se naje ba Suka yi daria goggo dije tace wasa nake ya za ayi na bigi yar daddy da aunty aunty tace yar mommy kuma da sauri tace bade yar mommy ba suka de yi daria Goggo dije tace ba dukanki da zanyi amma idan kika yi laifi zan bigeki tace bama zanyi laifin ba ba duka a can Kamal ya fito yace to mu tafi na shirya aunty ta mike tace to jirani in fito ta shiga ciki ta fito ta mika ma goggo dije leda tace gashi ba yawa akwai atamfa biyu se kiba ma hajia safiya daya sauran kuma turaruka ne da sabulai tace kai hajia halima harda dawainiya haka to an gode tace ba komai ta mika mata dubu biyar tace kwa kara na mota tace kai dawainiyar tayi yawa tace haba ai ba komi Ke kuma zarah idan tafiyan ya yuwu banda rashin ji kinji ko da yake ai gaki ga goggo dije ba zance komi ba idan na tashi zaki ga sako Kuma zamu rinka gaisawa tunda na amshi number din goggo dije kuma ga kamal ma zaki rinka ganinshi duk da ya kusa gamawa suka yi sallama suka tafi suna isa gidan amma suka shiga Amma tace sannunku da zuwa suka gaisa amma tace keko zarah ba magana goggo dije tace ai sena maketa mara kunya zaki gaidata ko kuwa ta gaisheta baffa ya shigo shima dan dole ta gaidashi Amma tace haba zarah me yayi zafi kullum kina ranmu baffa yace bare ni da ban ganin matana a kusa tace ni ba matarka bace me zanyi dakai Bayan ka rabani da mamana yace tofa abin babba ne shiyasa ashe kike fushi amma tace haba takwarata ki mana hakuri ba zamu kara ba tace ai amma banda ke baffa yace au duk fushin dani ake to kiyi hakuri har gida ina nan zuwa biko tace ai zaria zan tafi yace haba Goggo dije tace ai na amsheta yace na tafi da ita amma ta washe baki tace kai alhamdulillah abu yayi kyau baffa yace aikuwa kuma aita hakuri goggo dije tace ai ya zama dole bari mu tafi zamu biya gidan ahmad mu gaisa shima baffa yace to ai kin kyauta mun gode sun isa gidan ahmad yaji dadi sosai aunty falmata ji take kamar ta goya zarah da zasu tafi tace zarah bari in hada maki kayan shafa ko goggo dije tunda zata koma zaria se a rinka kawo mana ita hutu tace to ba matsala Suka mata sallama kamal ya daukesu ya maidasu gida [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD ya masu sallama ya wuce suna shiga cikin mommy tace ai na zaci ba zaku dawo gidan ba daga can kun wuce goggo dije tayi murmushi tace haba hafsa me ze hanamu dawowa gidan nan Nida gidan danuwana ita da gidan ubanta ai duk inda muka je dole nan zamu dawo mtsww mommy taja tsaki ta wucewarta goggo dije ta shige daki Hajia safiya tace kun dawo lalle kunyi nisan kiwo tace kede bari ai munsha yawo to ya kuka sameta lafiya lau tana gaidaki sosai ta bada sako ma na kawo maki tace kai na gode wannan mata akwai kirki ai ba karamin rashin dace bashir yayi ba saboda samun mace irinta a zamanin nan se an tona goggo dije tace kede bari ai har yanzu ina bakin cikin rabuwansu saboda tasan darajar mutane Anyi biki an kare lafia an kai amarya gidan mijinta se muce Allah ya bada zaman lafia kowa nata hada hadan tafiya gida goggo dije tace ma hajia safiya ni se jibi zan dawo saboda tafiya da zarah hajia safiya tace to nide yau gida zan kwana insha Allahu dan Allah dije banda fada ki samu ku rabu lafia Goggo dije tace ba abinda ze faru zan samu nakai zuciyata nesa Daddy ya shigo yace har kun gama shiryawa tace eh mun gama tsaf yace na zaci zaki dan kwana mana biyu tace a'a yau gida zan tafi gara de nesa nesa yace to ga mota nan tazo da zata maidaku ta jashi gefe tace dan Allah bashir ka dena wasa da addu'a Kada ka bari neman kudi ya fiye maka komi fa yace insha Allahu zan kokari inga na Kara akan wanda nake yi tace kuma ka rinka kula da halin da zarah take ciki saboda Allah ze tambayeka kiwon da ya baka akan 'ya' yanka ya ka tarbiyatar dasu Be kamata ace yarinya tun tana karama take cikin matsi na matar uba ba kuma kana cikin gidan ka kasa magana Yace ayi hakuri zan gyara tace to kade yima kanka fada ni zan wuce ya mika mata kudi yace gashi kya danyi hidimarki tace to na gode Allah ya kara budi ya ci gaba da kareka daga sharrin me sharri yace ameen ta fito duk wanda ze tafi ya shiga mota suka dauki hanya goggo dije ta dawo cikin gida suna zaune da zarah zarah tace har na kosa mu tafi goggo dije tace ai zamu tafi jira nake gidan ya dawo daidai na hada maki kayanki tace ai duk kowa ya tafi Muje kawai a hada kayan ta mike suka shiga dakin ta jawo katuwar jakan zarah ta fara fito da kayanta tana zubawa a cikin jakar zarah tace dama mi tafiyarmu yanzu goggo dije tace ai zamu tafin ne zarah tace duk a tsorace nake Salma ta shigo daukan wasu tarkacenta dan ta koma dakin khadija can zata rinka kwana ta tarar suna hada kaya ba tare da tace komi ba ta fita bata zame ko ina ba se dakin mommy [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD salam na shiga tace mommy zo kiga abin mamaki tace meya faru tace goggo dije na gani tana ta hada ma zarah kaya da alamu tafiya zata yi da ita Mommy tace tafiya fa kika ce to da izinin wa zata tafi da ita ta fito fuu se dakin su zarah ta shiga tace dije me kike haka ta dago da kanta ta kalleta shekeke tace me idanunki ya gane miki tace kina nufin tafiya zaki yi da ita tace eh tafiya zanyi da ita tace da izinin wa tace dako izinin wa inba mahaifinta ba ai kin san shi keda wannan ikon na barina na tafi da ita Mommy tayi shewa tace ai wannan umurnina ne dan haka ba inda zarah zata kuma ki rubuta ki aje tace to ko zanga yanda za ayi ke har kin isa dawa kike takama tace da karfin ikona da isata nake takama goggo dije tace jar uban nan hafsa har yanzu baki gama sanin wacece ni ba Naga kina son shiga gonata mommy tace gonarki na nawa kuma kuma zaki ga abinda zanyi Ta fita bata zame ko ina ba se dakin daddy tana shiga ta fasa mashi kuka yace hafsa lafia Tace akan me zaka ce dije ta tafi da zarah saboda ni na kasa riketa ko kuwa me kake nufi yace haba hafsa ya zance kin kasa riketa Ta nuna tana so in bata ya zan hanata tace a gaskiyar magana ba inda zarah zata karatunta fa me zata samu a can wane tarbiyane dije zata bata da kai ba zaka iya bata ba ko kama manta yanzu zarah tana shirin karatun sauka tafa shiga ajin sauka seka bada ita gara gaskia ka canza shawara kawai se a rabata da yanuwanta ni ban yarda ba goggo dije ta shigo tace ai magana an riga an gamata ba zaki dawo da hannun agogo baya ba da kike cewa wane tarbiya zan bata ai ke naga kina bata tarbiya na zalunci kuma zarah kamar ta bar gidan nan ne daddy yace wai miye haka kuke yi goggo dije tace yaya ka barni da ita Yace yanzu abinda za ayi dije ki tafi ni da kaina zan kawo maki zarah har gida tace haba yaya idan barci kake gara ka farka ya za ayi mun gama magana dakai kuma ka dawo kace kuma in tafi matar nan taka ba tsoron Allah a tare da ita fa ya kamata ka farka daga barcin da kake Ka dubi bakar UKUBA da diyarka take ciki mommy tace kome zaki ce sede kice amma zarah ba zata bar gidan nan ba goggo dije tace keko kina so ki gama da duniya lafia kuwa kin raba gaba 1 'ya da mahaifi kin raba yarinya da mahaifiyarta ba kunya ba tsoron Allah yanzu kuma kina so ki raba soyayyarta da mahaifinta ke wace irin uwa ce da bata san ta haifa ba ba tasan wa zata mutu ta barma nata ba tun wurin kiji tsoron Allah kije ki hake abinda kika birne muguwa azzuluma la'anan........bata karasa ba taji saukan mari a kuncinta yace akan me zaki zauna kina aibata matata a gabana zarah ce deko to na fasa baki ta rike kuncinta tace yaya ni ka mara kaci sa'a kai yayana ne kuma nasan ba a cikin hayyacinka kake ba ta riga ta wanke ta jika ta baka ke kuma ta nuna mommy tace kina takama da boka muna takama da Allah ki jira na wani lokaci kadan kada kiyi tunanin zan kyaleki kici gaba da sakewa a gidan nan kada ki manta bani da miji ba zaman kowa nake ba to zan dawo da zama gidan nan ki daura dammaran yaki dani Mommy ta buga shewa tare da tafa hannu tace dije ai sede kiyi hakuri dan na gaba yayi gaba ta juya wurin daddy taga ya dafe kai ya rasa me ke mashi dadi a zuciya tace yaya kenan ai tashin hankali kadan ka gani yanzu zan barma gidanka amma ina nan
Chapter 14 · 0% Book details