← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 24

Sashe 3

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kada ki yarda ta khadija tace bayan duk ka riketa ka hanamu ganinta kana mana rowanta minal tace ni ba zan maki rowa ba zoki ganta Amma ta karaso dakin suka gaidata halima tace Amma kin dawo tace eh yaran naki yau gaba 1 suka zo tace aikuwa tace shine baki basu komi ba tace fira muketa yi amma da kanta ta kawo masu komi kamal yace aunty dan Allah so muke ki auri daddy dinmu saboda mu samu muma uwa a kusa damu muka dai ne a gidan se masu aiki su ke kula damu se yayar daddy itama in ta dan zauna damu seta koma bauchi halima tace shi ya turo ku kenan kace mashi yayi hakuri banda burin aure yanzu kamal ya duko yace a'a wllh temaka mana zaki yi mu kadai muke rayuwa a gidanmu ya fara kuka yace muna so kizo gidanmu sbd inaji a raina zaki kula damu kamar ke kika haifemu suma sauran ganin kamal na kuka suma suka fara minal ta mike taje gabanshi ta fara share mashi hawaye tace yaya waya bugeku ku tashi mu tafi itama ta fara kuka halima taji tausayinsu ya kamata a zuciyanta tace Yara kanana se wayau tace kuzo ku dena kuka shikenan zan aureshi yace da gaske ta daga mashi kanta suka hau murna amma cikin itama hawayen tace kin tabbata tayi murmushi tace Amma kema kukan kike tace kaji yarinya kema nasan kinyi kukan yanda kike da saurin kuka nan yaran suka ci gaba da hidimarsu amma tace kinga har sun saki jikinsu driver ya dawo daukansu ta hada masu kayan ciyeciye suka tafi [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 1 kwanci tashi ba wuya halima tuni ta fara karatunta wanda har taci shekara da doriya akai inda suka fara shirye shiryen bikinsu a lokacin alh bashir ya shigo da maganar ba wanda ya isa yaje mashi da diya agolanci halima na fada maki ki bani diyata ba yanda za ayi in bar diyata a gidan wani katon banza cikin fada tace aiko ya wuce katon banza sbd ya mata abinda kai ka kasa yi mata dan haka ko duniya zata tashi ba wanda ya isa ya rabani da yarinyata yace aiko baki isa ba dole ne ki bani ita sbd ta samu tarbiya a gidan ubanta ba gidan wani gardi ba ta kalleshi a shekeke tace a wane gidan za a bata tarbiya bade a gidanka ba gidanka har tarbiyane a ciki ka fada min tambayarka nake wai yaushe ma ta zama diyarka in ka manta in tuna maka cewa kayi bata daga cikin sahun yaranka a yaushe ta zama diyar taka ka manta a yawon banza naje na samota kaga kenan baka da akala da ita diyata ce ni kadai mtss taja zaki ta tafi ta barshi a nan yace lalle yarinya yaushe tayi baki haka yaja mota ya tafi ta shiga gida da sauri Amma tace ke lafia tace Amma ba lafia to me ya faru ina sakona ta maka mata tace wai alh bashir ne yazo wai a bashi diyarshi Amma tace tirkashi wata sabuwa shida yace ba yarinyarshi bane halima tace kema kya fada tace to Allah ya kawoshi gidan nan zeko ji magana wllh bema da kunya halima tace aikuwa inama take tace ta ciki tana barci dawowanshi suka hade da baffa baffa yace naji duk abinda kace ai ba diyarka bace ba dolenka bace mune ta zaman ma dole dan haka tun wuri ka bace min daga kofar gida yace ni nasan diyata ce tunda Allah be yini matsiyaci ba ba zan bar yarinyata ta rayu a wani gida ba baffa yayi daria yace idan kace yarinyarka ne kana bani daria wai ka manta ranar dana je gidanka ne a gabana ba kunya kace diyata na yawon banza mazinaciya ce diyar data haifa ba taka bace ko wahalan da halima tasha a gidanka duk ina sane nade sa maka idanu ne da kuma yarinyar tasan darajar sirrin gidan mijinta bata taba fada mana da bakinta ba sede muji a wurin wadanda suka gani shine kakeso mu baka yarinya karama ku dakusheta tunda kuriciyarta yace baffa wanda ya faru ya faru sharrin shedan ne baffa yace na gode ma Allah da ka gane yarinyarka ce dan haka bani da lokacinka ya shige gida ya barshi nan [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 1 abu yaki ci yaki cinyewa alh bashir yaki hakura se zarya yake akan se an bashi zarah zuwan safe daban na rana na dare daban baffa ya kira halima taje yace zauna da kyau auta gamu ga yayyenki auta abinda nake so dake inaso ki dauki yarinyar nan kiba babanta halima da sauri ta dago ta kalleshi tace baffa ba zan iya badawa ba ai ba diyarshi bace yaya ahmed yace haba baffa ya za ayi a dauki karamar yarinya da ba tasan ciwon kanta ba a rabata da mamanta kome zeyi sede yayi ba za a bashi ita ba baffa yace duk ku rufe min bakinku a wurin ai rufin asirinmu shine ta zauna a wurin mahaifinta sbd ta wuce gori a idon jama'a ko kun manta bakin fentin daya shafa mata ita da mahaifiyarta ai abin mu gode ma Allah ne tunda har yazo da kanshi ya nuna diyarshi ce tunda har yayi nadama gara a bashi din ta zauna a gidan ubanta halima cikin kuka tace baffa na fasa auran nafi so na zauna da yarinyata baffa yace ashe dama baki da kunya ban sani ba aure ya zama dole ba zaki maidani karamin mutum ba tace wllh baffa ba wani nadama da yayi cutar da ita zasuyi yaya yusuf yace auta tashi ki shiga ciki [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 1 tana zaune a tsakar gida tayi kashi a wando haka ta wurgota tsakar gida ta barta kuda na binta se kuka take kamar ranta ze fita khadija ta fito da bulala a hannunta ta fara tsula mata tace yi mana shiru kin cika mana gida da kuka shegiya me bakin hali irin na uwarta taja tsaki ta tafi ta barta a nan khadija itace diyarsu ta farko me shekara 15 se zainab mansir sadiq umar salma se autarta husna itace tsarar khadija asalin alh bashir da mommy yan zaria ne aiki ya ajeshi kaduna haka tasa hannunta a baki tana tsota har barci ya dauketa a nan tsakar gida ga rana gaje ta shigo me aikinsu tace to lafia zarah kike kwance a nan ta dauketa tayi sashin da suke zaune a can ta shiga toilet ta wanke mata kashin ta mata wanka ta dauko abinci ta fara bata da sauri ta rinka amsa tana ci da taga bata bata da wuri ba tasa hannu da kanta ta diba juma ta kalli gaje tace anya kuwa akwai rikon arziki a tare da hajia kuwa nide na tausaya ma zarah gaje tace nima wllh dan wuyar da zata ci a gidan nan sede Allah ya kawo mata agaji baki nan ai mamanta take zaune gidan nan ba karamin kaskanci tasha ba taci wahala juma tace kai wannan mata ba digon imani a tare da ita haka mommy ta banko dakin tace uban wa ya baku izinin daukarta ku shigo da ita gaje tace ayi hakuri hajia tace duk wanda na Kara ganin ya temaka mata dede yake da barin aiki a gidan nan ta finciko zarah tana kuka ta fita da ita ta direta a kasa ta dauko wasu kayan da pampers ta fara sa mata tana kuka ta kai mata duka a baki tace yimin shiru shegiya bade an kawoki gidan nan ba se inga yanda zaki ji dadi a cikinta ta gama sa mata ta dawo da ita palour aka dankwafar da ita a kasa ta rakube a wuri guda se ajiyar zuciya take husna tana zaune a kan cinyar mamanta ga goran bobo a hannunta dasu chocolate zarah ta bita da kallo mommy ta mata dakuwa ta daka mata tsawan data gigitata kinbi se kallon mutane kike da idanunki kamar na mujiya kwadayayya ta dukar da kanta kasa zainab ta kwashe da daria tace jibeta se kace munafuka karamar yarinya da ita mommy tace to da miye ita an tsota a wurin muguwar uwa mansir ya tashi ya kai mata rankwashi ta fara kuka aka sata tayi shiru dole oh duniya ina zaki damu yanzu me yarinyar nan ta sani Allah kai mana katangar karfe daga sharrin masu sharri [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 1 tana daki taci kuka idanunta duk ya kumbura tana waya da alh aliyu yace kiyi hakuri zan nemi baffa da maganar ki dena kuka bana son kukan kome kenan anjima zan kiraki baffa ya shigo ya sameta kwance da plate din abinci yace auta tashi kici abinci mana kan wannan abin zaki bata ranki har kiki cin abinci mamanki tace tun dazun take fama dake kici abinci har ta gaji tayi fushi dake tashi kici kinji se muyi magana ta mike zaune ta amsa taci kadan yace kara kinji autana tace ya isheni ya amsa ya aje a kasa ya mika mata ruwa tasha yace auta kiyi hakuri da hukuncin dana yanke alh aliyu ma ya min magana a kai kin san idan na yanke abu na riga na yanke ina mai kara baki hakuri a matsayina na mahaifinki ki bar zarah ta koma hannun babanta shine mafi alkhairi kiyi hakuri ni babba ne na fiki hankali nasan abinda ke baki sani ba dan haka kede duk a inda kike ki rinka bin diyarki da addu'a tace to shikenan baffa yace yauwa auta Allah ya maki albarka ya mike ya fita ta saki kuka Amma tace ya kukayi da ita yace ta yarda Amma tace naso a barta ta rayu da diyarta baffa yace ni kaina halima ta bani tausayi ba yanda zamuyi ne se hakuri ita ma Allah ya bata hakuri da juriya ameen tace ai ni matsalata ahmad kasan halinshi yace ki barni dashi fitinanne an shiga hidiman biki a yau aka daura aure kuma a ranar ta tare kuka ko ba a magana ganin ta bar zarah ya zatayi da hukuncin Allah Amma ta riga ta
Chapter 3 · 0% Book details