Sashe 10
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zarah tsohon yayi yace ban gane ba ta gyara zama tace ai tafiyanka halima tazo har cikin gidan nan taci min mutunci wai tazo daukar diyarta ta gaji da ganin wadda ba uwarta ba tana rikonta shiyasa tazo daukarta ba yanda banyi ba kada ta tafi da ita amma seda ta tafi da ita yanzu inaso ka tashi kaje ka dawo da ita dan seta zauna ta rayu a gidan nan yanzu kuwa zanje na dawo da ita tace ai tare ma zamu suka ma gidan halima dirar mikiya ta shiga zarah na ganinta ta mike da sauri ta boye bayan yaya deen shiko harda kara boyeta aunty tace wa ya baki izinin shigo min gida cikin murmushin mugunta tace wanda yake baki izinin shigo min gida shi ya bani damar shigo miki gidanki daddy ya fito yace lafia tace ina fa lafia azzalumar mata ta shigo mana gida ya juya ya kalleta yace baiwar Allah daga ina tace gidansu zarah tare da babanta muke ya fita ya shigo da shi bayan duk sun zauna daddy yace nazo tafiya da zarah sbd halima taje har gida ta dauko ta ba tare da wani dalili ba halima tace bata fada maka dalilin da yasa muka daukota zuwa mukayi muka tarar tana dukanta se kace ta samu babban mutum mommy tace daga gyara sata tayi na hukuntaka ai temakonta nayi halima ta mike tace temako wane temako a haka ake temako temakonki na banza ta fita ta shigo da zarah ta daga jikinta tace jibi yanda kika fasa mata jiki haka ake hukunci ko ake so a gyara mutum dan haka ba wanda ya isa ya rabani da ita mommy tace aiko se kin bada ita tace ashe ko za a samu matsala daddy ya kamata ya zaunar da ita yace ba naso kina hayaniya baki ga ba lafia ne dake ba yace yanzu ka bari in komi ya lafa da kaina zan kawota yace be san wannan ba abu yaki ci har seda daddy ya kira amma yace su zo yanzu ba a jima ba se gasu ita da baffa yaya yusuf da yaya ahmad duk aka maida mgn halima tace dan haka ba zata kara zama wurinku ba zan mommy tace sata fa tayi se ace ba za a hukuntata ba halima tace ai idan tayi ke kika sata sbd kina mata da yunwa wane dan adam ne zeyi rayuwa da yunwa [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 halima ta dage se fada take baffa ya bita da kallo can ya nisa yace halima yaushe kika zama haka tarbiyar dana baki kenan ko bokon daya ratsaki rashin kunya ya saki har ina wuri ba zaki yi shiru ba tace baffa kayi hakuri idona ya riga ya rufe sbd cutarwan tayi yawa yaya ahmad yace baffa kasan dole tayi fada in ba haka ba wannan shedaniyar ba zata saduda ba kawai su bata diyarta tunda basu suka sha wuyar nakudarta ba baffa ya nuna yaya ahmad yace tun wurin ka min shiru tun kafin na koreka a gidan nan dan me aka so mu shigo ciki ai dan a san yanda za a bullo ma al'amarin ahmad ya kara tamke fuskanshi kamar wanda be taba daria ba baffa yace alh kana sane da wahalar da zarah ke ci a cikin gidanka ka kasa daukar mataki itama fa haihuwanta akayi tana da gata ba daga sama ta fado ba idan muka baka yarinyar nan ka tafi da ita muka ga komi be canza ba ni da kaina zanzo na dauketa saboda ba zamu sa ido muga ana azabtar da ita ba duka shekarunta nawa halima ta rufe ido tace bafa zan bada ita ba baffa idan kuma har aka matsa sena bada ita to dole in shigar da kotu a ciki sbd inada hakkin da Zan rike diyata daddy yace halima ki tsaya muyi magana a hankali bana so kina tada hankalinki ya juya ga amma yaceamma kinki cewa komi tunda kika shigo tace to me zance yaya yusuf ya gyara zama yace baffa maganar gaskia a barma auta diyarta ta reneta ta bata tarbiya saboda bata samun kulan da zata samu tarbiya a gidan da take mommy tace to me kake nufi da ba zata samu tarbiya ba ahmad ya kalleta da idanunshi daya kada yayi ja yace ina tarbiyar take ke har wani tarbiya gareki da zaki ba ta tsorata dashi ta kalli daddy tace kayi shiru kaki magana gashi har ana sheranta maka da gidanka ba tarbiya kuma duk kayi shiru ba zaka yi magana ba gara kasan abin yi har wani gindaya ma sharudda ake aiko kamar yana jira tayi magana ya fara yace ya zama dole a bani diyata idan kunga na fita gidan nan to tare da zarah ne halima tace aiko ba zaka tafi da ita ba sede duk abinda ze faru ya faru daddy yace wai ke halima me kika taka ne tace abinda ka taka kai da makirar matarka azzalumai kawai daddy yace halima dole ki bani ita mommy tace dolenta abu yaki ci gaba 1 wuri ya kacame baffa ya daka tsawa yace kowa yamin shiru ya dubi halima yace auta ki bani hankalinki nan ina so ki bashi zarah ya tafi da ita daddy yace kuma kada ta kara zuwa min gida tunda tashin hankali take nema in ba haka ba zan wulakantata baffa yace ba dakai nake ba ka saurara min halima kiyi hakuri ki bashi ta fashe da kuka tace baffa idan kaga ana ba mutum hakuri an cuceshi ni ba zan bada diyata ba shiyasa nasa aka bar gidan da ita baffa yace ma daddy kira min kamal dan nasan suna tare ya kawota yanzun nan halima tace wai ya kuke so nayi ne amma kiyi magana kema fa uwa ce ta kara fashewa da kuka yusuf ya mike yace banga amfanina a wurin nan ba ahmad ya mike shima yace hada dani ya nuna mommy da daddy yace kuma ina mai tabbatar maku idan har wani abu ya samu halima sena dauki tsatstsauran mataki suka sa kai suka fita [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 kamal ya shigo da zarah ta tafi wurin halima ta makalkaleta tace aunty kada ki bari su tafi dani gidansu halima ta kara fashewa da kuka tace akan me ba zaku barni in rayu da diyata ba ta kalli mommy tace meyasa dole se kinga an rabani da wadda nake so jinina wadda zata tausaya min a duk halin da nake ciki kinko son radadin da uwa take ji idan aka rabata da danta kema fa kin haihu kin san zafin da fa yanzu idan aka ce za a rabaki da wani dan da kika haifa ya zaki ji a cikin zuciyarki baffa meyasa ka kasa tausaya min a matsayina na diyar cikinka baka tausaya min ba ya za ayi wani ya tausaya min amma tace auta kiyi hakuri kisa ma zuciyarki salama tace amma kema hakuri zaki bani kinfa haihu kin san soyayyar uwa akan danta meyasa kuka cika cemin inyi hakuri dan abin be faru a kanku ba shiyasa baku san dacin da nake ji ba ta girgiza kanta tace tabbas baku san dacin da nake ji ba tunda ba a kanku ya faru ba a kaina ya faru dole ni kadai zan dandani dacin da nake ji me na maki mena tsare maki da ba zaki kyaleni hakanan ba kina ji kina gani ki raba da da mahaifi ribar me zaki samu baffa yace haba halima yaushe kika saba da yarinyar nan haka tace baffa banyi sabo da ita ba amma dole akwai soyayyarta a cikin zuciyata a matsayina na mahaifiyarta baffa ba rashin kunya nake ba gaskiyar abinda ke raina nake fada kuma ko sun tafi da ita sena je na daukota na canza garin da Zan zauna da ita na rayu da ita ta samu kulawan da uwa kawai zata iya yima danta bare su kara yunkurin zuwa daukanta baffa ya fusata yace haka kika ce ko to na datse dangantakar dake tsakaninki da zarah baki ba ita idan kullum zasu rinka diban naman jikinta suna dafawa yarshi ce idan kika kuskura kika bi zarah to ban yafe maki ba kuma bani bake sede ki canza iyaye da sauri ta dago ta kalleshi amma da daddy suka dauki salati amma tace hukuncin nan yayi tsauri da yawa yace hakan yamin daidai tofa an tabo bafullatani rai ya baci ya mike yaje amsar zarah ta riketa gam baffa na ja tana ja tana kuka ita kanta zarah kukan take can ya fisgeta ya mika ma mommy ta kalli halima ta saki shu'umin murmushi baffa yace kuna iya tafiya kafin daddy ya riko halima ganin zata fadi ina har ta sulale kasa sumammiya salatin da yaran gidan suka ji da karfi suka shigo dakin da gudu harda su goggo rabi kamal ya saki kara yace daddy mutanan nan zasu kashe mana ita ba yanda basu yi ba ganin ta farfado amma ina abu yaci tura amma duk kawaici irin nata da dauriya a ranar ta kasa ita kuka wadanda dake gidan suma kuka daddy yace kamal fito da mota da sauri ya dauki key ya fita daddy ya sureta suka bi bayanshi ya sata a mota suna isa aka amsheta emergency gaba 1 ana kan halima kokari ake aga ta farfado amma kukanta har ya fara fitowa daddy ke dauriyan bata hakuri shiko kamal ya ma kasa magana [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 3 daddy yace Amma kiyi hakuri mude fatanmu muga ta farfado amma tace baban kamal na shiga rudani akan me baban halima zan yanke irin hukuncin nan yasan halin da mahaifiyarta zata shiga da ita kanta yarinyar tsakanin fa da da mahaifi se Allah ba wanda ya isa ya rabasu meyasa baze yi tunanin azabtar da yarinyar nan take fuskanta ba daga wurin shedaniyar matar babanta haba duk wani me imani inde ya cika musulmi dole ne ya tausaya mata ribar me zata samu dan ta wahalar da kankanuwar yarinya me ta tsare mata da har shi baban halima ze yanke danyen hukuncin nan ai beyi dede ba gaskia daddy yace Amma kiyi hakuri