← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 24

Sashe 23

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

azzaluma ce ta rabani da dangina ta rabani da matata saliha me mutunci me son yanuwana ta fara rabani da dukiyata tana son kasheni jiya tazo da niyyar kasheni zarah ta temakeni mahaifiyarku bata kaunata dukiyata take kauna gashi har akan kudi zata iya kisan kai zata kashe uba ya'yanta Sadiq yace shiyasa jiya tace base na kwana a dakinka ba ita zata kwana yace tabbas dalilinta kenan ya dauko wannan tsuntsun ya nuna masu yace kunga asirin da tayi na kwanta ciwo ko tantama banayi da wannan halittar ta kwantar dani se gashi Allah ya fita sede kuyi hakuri dan a yau zan datse igiyar aurena dake kanta taje ita da Allah zata ga sakayya ta cutar da bayin Allah da yawa da basuji ba basu gani ba khadija tace daddy pls kada ka saketa zamuyi iya kokarinmu muga mun canzata ta dawo mace ta gari duk suka kaure da kuka suna rokonshi mansir yace ku kyaleta ya saketa abinda ta shuka ne dole a hukuntata dan ko nine matata ta min haka ba zan nemi shawarar kowa ba husna tace haba yaya mansir se kace ba mahaifiyarka ba ai duk lalacewan iyayenka iyayenka ne wayarshi ta hau kara ya dauka yace eh nan ne da sauri ya mike yace innalillahi kowa yace lafia yace mommy ce tayi accident tana asibiti gaba daya suka dau kuka Zarah tace ai se aje aga wane hali take ciki haka suka dunguma zuwa asibiti yanayin da mommy take ciki ba kyau Doctor ya kira mansir yaje yace kade ga yanayin jikinta kuma kaga yanda kafanta yayi dole se an yanke dayan kafanta daya lalace Mansir yace a yanke doctor yace anma auna arziki da ta rayu dan motar ance ba zakayi tunanin mutum ya fita ba yace hakane ya fita suka tareshi ya akayi Yace se an yanke kafanta daya lalace duk suka saki kuka haka ko akayi aka yanke kafanta daya mommy taci kuka kamar ranta ze fita ta dan kwana 2 a asibiti aka sallameta suka dawo gida bayan dawowansu gida daddy ya nemi kowa na gida suzo aka aka kinkimi mommy aka kaita dakinshi cikin mamaki tace ka warke yace kwarai kuwa kinso ki zaunar dani kinma so na mutu se Allah ya nuna maki baki isa ba azzaluma makira ai ga ishara nan kin fara gani abinda kika shuka ne kike girmanshi tace me nayi ya dauki wannan tsuntsu ya wurga mata da duk wasu asirai data birne da shima Allah ya bashi ikon ciresu Yace hafsa kin cuceni ba zan yafe maki ba zarah ta fita se gata ta dawo da jakan kudin da mommy ta boye ta mika ma daddy tace ga kudinka mommy ta kalleta zarah tayi murmushi tace zarah kin munafunceni ta fara hawaye goggo dije tace ai dama dan hakin daka raina shi ke tsolema ido abinda kuma ya saka daria wataran shi ze saka kuka Daddy yace kun gani ko kuke cewa kada in rabu da ita matar nan fa tayi nisa ba zata taba canzawa ba dan haka zan saketa kawai ta fara kuka zarah tace daddy ka kyaleta kada ka rabu da ita ko dan Albarkacin 'ya' yanta goggo dije tace hakane ka kyaleta yace naji amma zan kara aure goggo dije tace wannan yayi daidai na riga na zaba maka mata dama kuma ka santa ba wata bace illah jamila diyar kawu sama Yace au tana nan tace eh tunda auranta ya mutu ba tayi ba yace shikenan yanzu kiyi magana ni ko a jibi ne a daura bade tada matsala ko tace a'a zarah ta hau murna mommy tace dije yanzu da abinda zaki saka min kenan tace kin min abin arziki ne da na miki na sharri mansir yace mommy ko me aka maki ke kika ja wane fada ne bana maki daga baya amma kika ki ji yanzu wa gari ya waya ya juya wurin zarah yace zarah duk wani abu dana maki ki yafe min tace yaya mansir alkhairi daka min a baya yasa na manta duk wancan ba matsala husna na kuka ta dawo gaban zarah ta rungumeta tace zarah ki yafe mana na ari bakin sauran yan uwana Mun zalunceki zarah ta toshe mata baki tace duk ya wuce na yafe maku Dukansu duk suka roketa gafara husna tace mommy dan Allah ki roki zarah ta yafe maki harda mahaifiyarta ma kuma mommy ki zama ta gari duk ki jefar da mugayen halinki bade tace komi ba se kuka da take yi husna tace zarah ki yafe ma mommy Ina kara neman afuwarki ko zan samu sa'ida a raina gashi miji ma in samu ya gagara Tace husna na yafe maki miji kuma da yardar Allah zaki samu zarah tace daddy banji kace ka yafe ma mommy ba yace zarah ya wuce yaushene bikinki ta dukar dakai goggo dije tace sati biyu ya rage yanzu yace to se a fara nawa sannan nata yaya farouk yace daddy in ba matsala nima inaso ka bani auran husna daddy yace to kinji husna ba bata lokaci tace na amince nan daddy duk ya masu nasiha sannan kowa ya tashi ya bar dakin ranar zarah ba karamin farinciki tayi ba duk wani masoyinta seda ta kira ta fada mashi [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD ba a dau wani lokaci ba a kwana biyun aka daura auran daddy da jamila mommy kuwa ta zama kurman karfi da yaji se kuka kullum cikin kunci take Zarah ce tafe ita da husna zasu gidan aunty sun isa gidan aunty ta rasa inda zata sa zarah dan murna ta kallesu tace naji dadin yanda kuka hada kanku kishi beda amfani koda ace mazajenku zasu yi aure ko sunyi ba ruwanku da bakin kishin da ze kaiku da halaka zaman lafia yafi komi a rayuwa duka duniyar nawa take namiji ba an halicceshi dan mace daya haka ta zauna tana ta masu nasiha daddyn kamal ya shigo aunty tace kuje ku gaidashi zarah tace kunya nake ji tace tashi bana son haka kuje haka suka shiga dakin ta gaidashi yace ke miye kike jin kunyata ni ba sirikinki bane Babanki ne ni nan shima ya masu nasiha nan ma suna gamawa da gidan sukayi gidan amma taji dadin ganin zarah baki yaki rufuwa haka baffa yusuf ne ya shigo da matarshi se yaransu 4 duk se tambayarsu sunansu take yaran sun shiga ranta taja wannan taja wannan tace uncle yusuf yaushe kuka zo yace mun kwana 2 muna nan ma har bikinki tayi murmushi tace aunty safina se yau na taba ganinki tace aikuwa zarah sede naji labarinki shima nan suna gama gaidasu sukayi gidan uncle ahmad aunty falmata tace nako ji dadin zuwanki zarah ya maganar dilka da gyaran jiki dan nasa yagana tazo tun jibi saboda ta gyara min ke zarah tace nifa aunty falmata bana so tace aiko baki isa ba se anyi gara ma ki shirya husna tace kyaleta ai zama ayi ne zarah tace to mu zamu wuce tace tun yanzu tace aikuwa akwai wuraran da zamu biya har gidansu khadija duk seda sukaje daga nan suka yada zango gidan siyama tace kai kawa naji dadi da zuwan nan me ake shirya mana na biki husna tace ai tace ba wani chasu da za ayi sede ni na samu yaya deen akan maganar komi muka shirya tace yauwa yar gari bikin zarah da yaya deen ai dole mu rakashe soyayya tun yarinta ai zanyi rawan da ban taba yi ba can zan baro kuguna idan na dawo akace ina kugunki ince na baroshi bikin bikin kawa zarah suka kashe da husna zarah tace bari mu tafi gida yamma tayi sun isa gida ta fada dakin jamila ta fada kujera tace wash aunty amarya yau na gaji munsha yawo tace ai dole ki gaji kuwa tashi ki shiga ki watsa ruwa kyaji karfin jikin ki haka tayi Biki ya kankama yagana ta iso ta fara gyaran jikin zarah wadda har ta fara tsumuwa da kamshi a kwana 2 ga magunguna ana bata tana jin haushin sha se ja take karawa duk inda ta gitta kamshi ne ke fita siyama da husna sun tasata gaba siyama tace gaskia nima so nake inji ina kamshin nan aunty yagana ya za ayi ne tace kizo musa labule tace aiko zanzo zarah tace aunty yagana nayi yellow da yawa a bar dilkan nan hakanan tace a'a se nakai karshe tace kai aunty yagana husna tace kawai ki bari aci gaba se kace ke ba yar maiduguri ba Zarah duk ta kosa a gama gashi ta gama kyau iya kyau UKUBA Na EASHA MD zarah kam ba dama ga lefe an kawo tasha kaya akwati set biyu komi yaji a ciki me tsada lefe ne na gani na fada ana jibi biki aunty yagana ta daura mata lalle ranar rufi kenan anan cikin gida aka kawata wurin da decoration zarah tasha lifaya me tsada ta fito husna tace wow sister kin ganki kuwa dama ga yaya deen ya kosa ya ganki ya sani dole sena fito mashi dake tace kai husna kunyar zuwa nake tace ki daure tace to jirani ina zuwa tayi dakin mommy taga tana kuka crutches dinta baya kusa tana so ta fito gashi tana kan gado zarah ta idasa wurinta da sauri tace mommy lafia me kike so ba kowa a dakin ne tace eh zarah zarah dan Allah ki yafe min kinga yanda Allah ya maidani tace mommy kiyi hakuri na yafe maki tuntuni tace zarah hassada da kiyayya da mugunta basu da amfani nayi dana sani sosai Zarah ta fara hawaye mommy tace zarah dena kuka kada ki bata kwalliyanki zarah da kanta ta shirya mommy ta mata kwalliya ta mika mata crutches dinta suka fito tare seda taga ta aje mommy tayi hanyar fita umar yazo ya tsaidata yace zarah mun gode mu abinda muka kasa yi maki kenan tace ba komai komi ya wuce tadashi beda amfani ta wuce husna tace inata jiranki tace seda na tsaya shirya mommy ayi biki uwar amarya bata guri husna tayi shiru sannan tace zarah mun gode suka isa wurin su kamal UKUBA Na EASHA MD kamal gaba daya ya kasa kauda idonshi akan
Chapter 23 · 0% Book details