← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wai nayi haka bane dan ko bana sonki ba ina sonki asalima kullum se nayi kuka akan halin da kike ciki bade yanda zanyi ne Tayi shiru bata ce komi ba goggo dije tace ku tafi zanyi magana da ita suka tashi suka tafi yaya deen yace zarah se na kiraki tace to suka tashi suka tafi zarah tace goggo dije ina tausayin mommy duk ranar da alkadarinta ya karye a gidan nan fatana kawai Allah ya shige mana gaba goggo dije tace ai zata raina kanta kuwa [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD tun daga ranar zarah ta dena tsoron mommy komi ta tashi yi yin kayanta take ba tare da tabi ta kan kowa ba A haka aka zo bikin siyama ta taka rawar gani a bikin kawarta aminiyarta duk a lokacin suna tare da yaya deen duk inda tasa kafa se yasa suna zaune yace zarah ya kamata fa kima daddy magana a tsaida ranar bikinmu gashi har siyama ta manta tana dakinta Tace ai muma zamuyi namu yace ko da yake aunty ma zan tunkara da maganar tace da yafi kuwa aiko haka yayi da kanta ta kira daddy ta mashi bayani yace ba damuwa kuna iya turowa a tsaida maganar Anko sa ranar biki wata uku kamal dadi kamar me a wurinshi fatanmu Allah ya kawo ranar bikin Zarah ce ta shiga dakin goggo dije tace goggo yaune fa masu saukan qur'ani zasu fara gasu nan sun zo goggo dije tace nafa shafa'a yau juma'a da sauri ta mike ta samu su gaje akan a jika shinkafa ayi waina na sadaka sede aka jika da ruwan zafi da sauri suka kama aiki mommy tace wai me za ayi zarah tace sauka mukeso ayi a gidan mommy tace aiko ba wani sauka da za ayi wai ke me kika dauki kanki tace mommy kada ki manta dan zaki ya girma kuma sauka se anyishi saboda idan akwai shedanu a gidan su fita Tazo zata mari zarah zarah ta rike hannunta tace kada ki kuskura ki bigeni dade kin buga amma yanzu na wuce husna tace waike wacece da zaki zauna kina fada ma uwarmu magana tace ni zarah da aka dade ana zaluntana a cikin gidan nan kuma bari in fada maki ba komi zesa na raga ma mommy ba se albarkacin ta haihu kuma nasan ba zaku ji dadi ba Ta tafi ta barsu nan aka fara sauka gadan gadan duk hankalin mommy ya tashi a ranar ta fita ta bar gidan Aka gama sauka akayi sadakan da za ayi Washe gari aka dawo da daddy gida ba lafia yana kwance kamar gawa zarah kuwa ba abinda take se addu'o'i na neman tsari akan matar nan ga ciwon daddy daya daga mata hankali duk yaranshi sun zagayeshi zarah sarkin kuka har ta fara kuka duk wanda ya ganshi seya tausaya mashi UKUBA Na EASHA MD kwanan daddy biyu amma har yanzu yana kwance ba magana zarah tazo zata shiga dakin daddy taji muryar mommy na cewa ai kadan ka gani a wannan ciwon yanzu abinda ya rage min in kasheka in kwashe duk wata dukiya daka mallaka dama burina na mallake dukiyarka kuma ka jira mutuwarka na dan kankanin lokaci gonar da kafi ji da ita ta hanyar zaria na riga na saidashi ka ko san miye ma abin farin cikin na saidashi naira na gugan naira miliyan hamsin kaga yanzu sauran kadarorinka suka rage nabi ta kansu mijina ga kudin har sun iso ta bude wata jaka ta kanga mashi kusa da idonshi duk zarah na kallonta ta hango daddy na hawaye itama hawaye ya zubo mata taga mommy zata fito da sauri ta bar wurin taga mommy ta nufi hanyar dakinta ta bita tana lekenta taga ta tura jakan a karkashin gado tayi murmushi ta bar wurin Ta koma dakin daddy tasa hannu tana share mashi hawaye tace daddy ka dena kuka duk naji abinda mommy tace kuma insha Allahu zan temaka maka hatta kudinka sena maido maka yayi murmushi tace yauwa daddy bari naje na dawo haka taje ta fada ma goggo dije duk hankalinta a tashe goggo dije tace miye abin yi tace ido zamu sa mata kuma gobe ki kula dashi kinga zani school exams inda na gode ma Allah gobe zamu gama insha Allahu ba zata cinma burinta ba haka zarah ta kwana duk hankalinta a tashe kuma tasa ido sosai akan daddy duk wanda ya shiga dakin se tabi bayanshi taga me ze aikata Yau ta tashi Tana so ta gyara ma daddy dakinshi saboda mommy ke gyarawa bata bari wani ya gyara mashi Tana ta aikinta ta daga carpet din dake wurin taci karo da wasu laya guda biyu ta dauko ta aje seda ta gama aikin ta dauko layan ta mashi filla filla taga harda su gashi a ciki se takadda da yake dauke da sunan daddy da aunty ta bude dayan taga nama an sokeshi da allura tace innalillahi wa inna ilaihirraji'un duniya ina zaki damu ta daukesu ta fita ta shiga dakin mommy tace mommy gashi abinda kika shuka na fara girbo maki mommy tace ke bakida hankaline a ina kika ciro tace dakin daddy tace me ya kaiki zarah tace komi ya kaini gashi na aje maki mommy ta kalleta ta kasa cewa komai tayi murmushi tace dis is the beginning muje zuwa mommy [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD haka zarah taci gaba da addu'a ba dare ba rana saukar qur'ani kuwa duk bayan kwana biyu tasa ana yi ta yawaita sadaka Dakin daddy ko can take zaman wuni mommy ta zageta tayi fadan ko a jikinta wani shigowan da mommy tayi tace zarah wai ya za ayi ki zama ke ke zama dashi bayan wani abin dole se namiji ze mashi tace eh mommy ai abinda namiji ze iya mashi nima zan iya tayi tsaki tabar dakin zarah ta fita dan taci abinci bayan ta gama ta tashi dan ta koma dakin daddy zata shiga kenan taji magana mommy tace sede kayi hakuri dan yau zan aiwatar da kisanka dan naga alama zarah ta fara min shishshigi a lamurana Zarah bata nuna taji ba ta shigo da sallama tace sannu mommy kina nan kinata jinyar daddy ai idan yaji sauki zeyi alfahari dake kuma ze baki lambar yabo Mommy ta fara share hawayen karya tace ai wannan cuta ta mahaifinku se inga kamar baze tashi ba zarah tace haba mommy ai kuka be kamaceki ba ita cuta ai ba mutuwa bace da yardar Allah daddy ze tashi zarah tace dare yayi bari naje na kwanta mommy tace nima tafiya zanyi nasan sadiq shima yanzu ze dawo kula da babanku itama ta mike suka tafi zarah na ganin ta shige daki tayi maza ta fito ta koma dakin daddy tana shiga seda taga alamun daddy yayi ajiyar zuciya tace daddy kada ka damu ina nan tare dakai can dare ya tsala mommy ta faki idon kowa yayo dakin daddy zarah naji alamun bude kofanta tayi saurin shigewa toilet Mommy ta shigo ta isa gaban daddy tace bakon lahira yau zaka tafi se munzo bayan na kasheka zan juya kan zarah itama na halakata dan bata da gado a cikin dukiyarka kaga dukiyarka se ta zamo daga ni se yarana se a fara jerani a sahun attajirai ta dauki pillow zata danne mashi hanci tace ya naga kana tsorata ai zare ran ba zafi saki jikinka tana daurawa a kanshi zarah tayi maza ta saki ruwa alamun plushing ta fito daga toilet din tace mommy kece a daran nan cikin kame kame tace eh na kasa barci ne kuma na shigo naga yana son a gyara mashi kwanciya na gyara mashi zarah tace kin kyauta ta isa kusa da daddy tace sannu daddy ba abinda ke damunka ko yade bita da kallo mommy ta tashi ta fita zarah tace muguwa zaki ga karshenki ai Washegari tun da wuri goggo dije ta shigo tace zarah ba abinda ya sameku ko tace a'a tace alhamdulillah ai mafarkai naita yi marasa kyau a kanku zarah tace ai daddy ya auna arziki har tazo kasheshi goggo dije tace lalle matar nan bata son rahamar Allah UKUBA Na EASHA MD zarah tace ai ita duniyar kawai tasa a gaba se gata ta shigo da yaranta tace yame jikin zarah tace ai jiki da sauki ta tashi ta fita taje tayi wanka ta gama shirinta tsaf ta fito Ta koma dakin daddy duk kowa ya fita ta rage ita kadai ta dibi ruwan zamzam ta tofa mashi addu'a kamar yanda ta saba ta bashi yasha ta tashi tace daddy bari in gyara ma kwanciyanka ta fara gyara mashi tace ko insa ka dan jingina da bango ya bita da kallo da kyar ta samu ta dagashi taja pillow zata daura sama ta hangi wani abu kamar tsuntsun ta dauko ta aje seda ta jinginashi da bango sannan ta dauki tsuntsun taga an daure mashi jiki tamau bakinshi ma an daure mashi ta fara warwareshi sannan ta warware bakinshi zata ciro abinda ke jikinshi kaman laya ta juyo karan mommy da sauri ta aje ta fita ta isa dakin mommy da har ya cika da mutane tace kudina da na aje a karkashin gado miliyan hamsin ku fito min da kudina mansir yace miliyan hamsin fa kika ce ina kika samesu tace nide ku fito min da kudina zan tsine maku ta zari key din mota ta fita ta bar gidan zarah tace banso kuka barta ta fita ita kadai ba saboda ba a cikin hayyacinta take ba zarah da sauri ta koma dakin daddy bata kula dashi ba ta kara daukan tsuntsun ta bude layan taga sunan daddy a ciki tayi dogon ajiyar zuciya daddy ya motsa jikinshi yace zarah Allah yayi maki albarka Da sauri ta waigo ta kalleshi ta fita da murnanta tace daddy ya fara magana da sauri kowa ya shigo dakin harda ma'aokatan gidan kowa na mashi sannu daddy yace kowa ya zauna ya kalli khadija da salma yace kuma naji dadin zuwan da kukayi gidan yau [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD ya kalli duk wanda ke dakin yace khadija kuyi hakuri mamarku muguwa ce
Chapter 22 · 0% Book details