← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 24

Sashe 24

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zarah ji yake kamar ya dauketa ya gudu da ita abokinshi nasir yace haba abokina ai se idon ya fadi wannan irin kallo haka yayi murmushi yace sweety maza basa shiga wannan rufi da ake dan bana so kimin nisa husna tace aikuwa sede kayi hakuri yace nima a rufe ni mu shiga kawai siyama ta fito tace ku shigo za a fara cikin marairaicewa yaya deen yace yanzu tafiya zakuyi da ita ban gama ganinta ba itama siyama ta kwaikwayeshi tace za a kai maka ita gida suka shige ciki suka kara gyarata tun wurin fitowa da ita ake fesa mata hadin turaruka har ta isa wurin zamanta gida ya cika da yanuwa da abokan arziki Zarah kanta tasan yan maiduguri na wurin ji take har Turare ya fara hawa kanta malamai suka fara wa'azi zarah ta fara kuka ganin irin yanda ake kawo hadisai da ayoyi na aure da hakkin dake kanta na mijinta da azabar wanda baya daraja mijinshi daga karshe akace mahaifiyar amarya tazo ta bata shawarwari aunty da kanta tasa mommy ta fita ta bata shawara a matsayin uwa data riketa seda mommy tayi kuka taba zarah shawarwari dede gwargwado wurin ya dau kabbara bayan an gama aka raba abinda za a raba da wani littafi da aka buga na yanda mace zata ma mijinta ba tare da tabi boka ko mallam ba da addu'o'i a ciki Akayi aka gama washegari aka hada gagarumin party wanda aka gayyato makada da mawaka wurine da ya halacci manyan mutane masu fada aji tsayawa fadin tsaruwar wurin ma bata lokaci ne kai abinde se wanda ya gani ga amarya da ango da suka hakimce sunsha kyau kamar wadanda suka fito daga jinsin larabawa idan nace zan tsaya fada maku kyan da sukayi se charjina ya kare wanda de be halacci bikin nan ba an barshi a baya haka aka sha shagali aka tashi nan ma ansha rabon kaya jakunkuna memo riga robobi dade sauransu duk da tambarin hotonsu a jiki Washegari aka shaida daurin auran zarah da yaya deen wurin daurin auran hatta fararen Fata ba a barsu a baya ba An gama yinin biki an kai amarya gidanta dake yanmajalisu ba karamin keruwa yayi ba a ranar da aka kaita kowa ya watse akabar amarya da angonta [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD zarah tunda aka kaita take kuka har yaya deen ya shigo yayi maganar duniya amma taki denawa se kuka take yace zarah tashi kiyi alwala muyi nafila ta tashi ta dauro alwala shima yayi sukayi nafila ya kama kanta yayi addu'o'i sannan ya tambayeta akan addini zarah duk ta fada mashi yaji dadi ya gode ma Allah daya bashi mace saliha me ilimi Bayan sun gama ya sata tayi wanka shima yayi yayi shirin barci yazo yaga ta maida kayan data cire yace haba zarah ai se ki kasa barci dakyar ya samu ta canza kaya kayan daya shigo dashi taki ci sede ta kwanta haka cikin dare yaya deen yace be san wannan ba zarah taci gaba da kuka tana cewa yaya deen bana so jin haka naja kofa na rufe masu na hau kan kujera na kwanta ina jiran su fito nan barci ya daukeni hayaniyarsu ya farkar dani kai ashe safiya tayi na Kara binsu dan ganin me ze wakana na fada dakin na tadda zarah kuka kawai take yaya deen yace zarah tashi ki kara wanka kiji dadin jikinki da kanshi ya kaita toilet ya mata wanka tare da daura mata alwala ya fito da ita ya gama shiryata ya shimfida mata dsdduma tayi sallah nan ta kuma kwanciya barci ya dauketa ya shigo da kayan breakfast ya tadda tayi barci ya tadata yace bari idan kika sha seki kwanta dakyar ya samu tasha tea kafin kace me zazzabi ya rufeta ya rasa inda zesa kanshi ya dauketa ya kaita asibiti nan doctor ya rubuta mata magunguna ya siyo mata suka koma gida nan ta kwanta a kasa yace tashi kisha maganin ko tace se da tuwo zanci yace tuwo kuma ina zan samo tuwo Bako yanda zeyi haka ya fita samo tuwon da zata sha magani seda ya samo Haka zarah suka ci gaba da zamansu cikin so da kauna gwanin sha'awa Watanta biyu da aure akasha bikin husna Bayan shekara daya zarah ta santalo yaranta biyu yan mata ranar suna aka rada masu suna halima (afnan) se dayar aminatu (afra) zama ne naso da kauna ake a cikin gidan gwanin sha'awa Bayan shekara uku tafe take a mota zuwa dauko Yara daga school bashir (afan) ne a bayan mota se kiriniya yake tace afan ba zaka natsu ba se na zaneka yace se kin kaini wurin amma sannan zan daina kiriniya tace to Ka natsu zan kaika yace da gaske tace eh a ranar basu dawo gida ba seda akaje gidan amma Yaya deen ya kalli zarah yace wai yaushe za a haifamin babana ne tace wadannan sun isa yace a'a ban yarda ba se an haifi babana gaskia Alhamdulillah zarah hankali ya kwanta tayi kyau abinta ka kalleta dole ka kara kallonta saboda kwanciyar hankali ya zauna mata kullum cikin farin ciki take idan ta juya ta ga yaranta tare da abin kaunarta yaya deen ga mommy yanzu ji take kamar ta hadiyeta dan so domin kafin yaranta su mata zarah ta mata Allah ya bar kauna ya hadamu da masu sonmu na gaskia ameen ALHAMDULILLAH MASHA ALLAHU LA QUWWATA ILLAH BILLAH Ina bawa duk wanda wannan novel be yi mata ba ko taga abinda ya faru a ciki hakuri kuma kofa a bude take ga duk wani wanda ze bani shawara ina maraba dashi kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafe min ya yafe mana gaba 1 ya sbd dan adam ajizi kuma tara yake be cika goma Allah ya kara mana son annabi (saw).

SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
84064a4fa33e42349b3dfe21e21592ea
Chapter 24 · 0% Book details