Sashe 15
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawowa ta fita ta tadda zarah makale a kusa da dakin tana kuka Tace haba zarah me ya saki kuka share hawayenki muje ki dena kuka saboda ke zan dawo gidan nan da zama Goggo dije ta dauki jakan kayanta zarah cikin kuka tace yanzu shikenan goggo ba zamu tafi tare ba ta kara fashewa da kuka tace zarah zan rinka zuwa akai akai ina dubaki Kuma zan dawo gidan gaba daya da zama tace kinde fada min ne kawai wai meyasa take min hakane duk wani wanda taga yana sona seta rabani dashi goggo dije tace zarah kiyi hakuri ai watarana se labari zaki ga kamar ba ayi ba yanzu dauko biro na baki number dina Ai su gaje nada waya ko se ki rinka kirana muna gaisawa nima zan rinka kiranki ta amshi number dinta ta fito rakata sun kai harabar gidan daddy ya fito ya tsaidata tace me kuma zan maka yace yanzu baki ga yamma tayi ba baki bari se gobe tace a'a yace to bari bala ya maidaki tace daka barshi ya bata rai tace to naji ya kaini yace dan Allah kiyi hakuri Nasan ban kyauta ba tace me zance maka to ta fara hawaye tace yaya wannan wane irin rayuwa ce ka jefa kanka yace nide ina kara baki hakuri zan san yanda zanyi na kawo maki zarah nide addu'a dinku nake bukata ya mika mata kudi masu yawa tace a'a ka barshi saboda ka fiye min duk wani arziki daka tara yace na sani ki amsa haka de ta amsa ya juya ya kalli zarah da har a lokacin kuka take sede ya girgiza kai kawai ya kira bala suna magana goggo dije ta ciro kudi ta mika mata tace kya rinka amfani dashi tace to na gode daddy yace ki taho ku tafi har gaban mota ta rakata tun kafin ya tada motan ta bar wurin da gudu tayi hanyar garden ta zauna ta fara shashshekar kuka me ban tausayi tace mommy me na maki kike min haka ta kara rushewa da kuka [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD mommy ta zo har garden din tace wato nan kika zo kina kuka Dukanki akai ko me aka maki tace bakomai to tashi ki wuce cikin gida Ta mike ta wuce ba tare da tace komi ba ta koma daki tayi zamanta dan gaba daya gidan ya isheta bata son gidan haka ta kwanta burinta taga gari ya waye ta bar gidan Washegari ko da wuri ta tashi tayi shirin makaranta bata tsaya bi ta kansu ba dan tasan ba zasu ba nan ta tuna da kudin da goggo dije ta bata ta duba taga dubu biyar nan ta zari dari biyar ta fito Ta duka ta gaida mommy tace zan wuce school taga bata da niyyar tanka mata tayi hanyar fita dan ko bi ta kan breakfast bata yi ba Sun fito break siyama ta dubeta tace zarah yau naga kamar kina cikin damuwa hala mommy tace ai kin San se ita daddy yaba goggo na ta tafi dani amma seda tasan yanda tayi ta hanani siyama tace kai wannan mata kiyi hakuri A haka zarah taci gaba da komi nata har suka fara exams suka gama lafia Akayi hutu tare da basu result dama ita ke zuwa 1st position tayi sallama da kawarta siyama suka rabu Sun isa gida gaba daya husna cikin takaici take ta shiga daki ba tare da ta kula kowa ba lesson teacher yazo yace kowa ya kawo mashi result dinshi suka kai zarah ta mika mashi Yace kai masha Allah zarah ki gode ma Allah ya amshi na husna yace husna ya akayi haka kije ki kwaso ma kanki na biyun karshe gaba daya kin maida kanki jaka ta zunbura baki Yace kinga yanzu gashi zarah har saukan alqur'ani zata yi gashi se matsowa yake nan na dage daga bokon har na addini ina kokari akan koya maku amma baki maida hankali Zarah ki gode ma Allah dan ya baki kwakwalwa husna ta fisge result dinta tayi cikin gida ta fada kan mommy ta fara kuka tace ke kuma lafia tace wannan uncle din ne se faman gaya min magana yake akan zarah tazo na daya har yana cemin jaka mommy tace haka yace tace eh tace to zanyi maganin abin zarah na shigowa tace ke zo nan tazo ta duka tace gani tace kada in kara ganin kin fita lesson a gidan nan tace mommy saboda saukana ina tilawa a wurinshi Tace to nade hana zuwan wanda aka koya maki a makaranta ya isa haka ba tace komi ba ta mike ta shiga daki Haka taci gaba da karatunta ba tare da ta samu matsalan komi ba da suke fatan ta samu da taga haka bata barin wuri se taga ta iya ko in bata gane ba ta samu wani ya koya mata se taga ta iya Kwanci tashi ba wuya a dade ana yi se gaskia hassada kuma game rabo taki gashi har ta gama hadawa suna shirin walimar sauka ta samu ta kira goggo dije a waya ta fada mata walimar saukansu tace zaki zo de ko inba haka ba ba abinda za a min kuma saura sati daya tace to ina nan zuwa gobe ko jibi taji dadi sosai Haka ko akayi se gata tazo bata tsaya bata lokaci ba ta kira daddy a waya ta mashi bayanin komai yace to ba matsala yanzu zansa a kawo maku komi da kuke bukata tace ka bada kudin tace to sede ka bari se ana gobe saukan yace ai ranar asabar ne ko tace eh yace to ranar alhamis zan dawo se a siyo komi tace to Allah ya dawo dakai lafia ta kashe wayan Ana ko jibi sauka daddy ya dawo bayan ya huta Washegari suka fita da bala da goggo dije haka suka yo siyayya sosai ga kaji masu yawa ga katon ra go da za a yanka aka shigo da komi goggo dije tace to gaje ku fito aikin nayi ne mommy tabi daddy daki tace yanzu ka nuna min iyakata akan zarah yace me kuma nayi dije ta nemeni akan komi na zarah ke baki nemeni ba tace to ai jira nake ka dawo sannan muyi magana yace to nayi laifi kiyi hakuri ta fita ya kira salma yace kira min zarah da husna ta kirasu ya dauko kaya ya mika ma kowa kala biyu Yace ke kuma zarah ga naki harda na bikin saukanki na Kara maki suka yi godiya yace kuje ku gwada kuga ze muku ko tunda lokaci ya kure kafin a dinka maku shiyasa na siyo dinkakke suka mashi godiya suka fita goggo dije taje ta samu mommy a daki [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD bayan ta sameta tace naga an kawo komi banga kinyi magana ba tace ya za ayi nayi magana tunda an nuna min iyakata akan zarah an nuna bani na haifeta ba goggo dije tace ki dena fadin haka koda nazo bada tashin hankali nazo ba yanzu de kiyi hakuri ki shiga kan maganar nan hajia Amina ta shigo goggo dije ta fita hajia Amina tace hidiman me kuke tace zarah ke sauka amma kinga be sani kan hidimanta ba duk ta fada mata yanda akayi Tace laifinki ne baki iya cin arziki ba kina nuna karara kishinki a kanta ne shiyasa yanzu ki tashi ki saki jikinki ki shiga hidimanta haka ta lallabata salma suka shigo da kaya a hannunsu suka nuna mata daddy ne ya siyo mana tace to kun gode zarah ma nata yafi namu yawa saboda wai ita zata yi sauka mommy tace kin gani ko Tace kibi komi a hankali kada ki tada hankalinki da kanta hajia Amina ta kira kawayensu tana fada masu gobe akwai waliman sauka gidan hajia hafsa tace to rashi mu fita suka je wurin hidiman goggo dije tace kin fito tace eh Kamal da khadija suka shigo gidan su bala suka biyosu da kaya a hannu mommy ta fito daga dakin daddy suka gaisa yace sako muka kawo zarah ta fito da sauri ta rungume khadija nan aka bude su jakukkuna memo biro littafi da suka buga mata se snacks dangin su cake da doughnut mommy tace an gode sosai dama yanzu na mashi maganar snacks se a sauke drinks kawai goggo dije tace aikuwa sannunku kamal Allah ya bar zumunci ya mika ma mommy wata leda yace dinki ne aunty tace aba zarah da husna tace to an gode Hajia Amina ta bude ledan ta mika ma kowa nashi kala biyu yace to zamu koma goggo dije tace ku tsaya ta shiga ta fada ma daddy ya fito ya washe baki yace kai munfa gode ya ciro kudi ya mika masu kamal yace a'a daddy goggo dije tace aiko se kun amsa da kanta ta amsa ta mika ma khadija zarah har gaban mota ta rakasu suka fita Washegari ba abinda ba a tanada ba da walima dama da yamma za ayi a gida kowa ya hallara zarah ta fito tare da siyama ta hangi yan school dinsu tace kai siyama ya haka tace ni da kaina na gaiyacesu dan nasan ba zaki fada ma kowa ba tayi murmushi taje duk suka gaisa dasu anyi walima an kare lafia inda duk wanda ya kawo ma zarah gift ya mika mata tayi godiya anyi an gama kowa ya tafi gida zarah kuwa farin cikin da take ciki baya misaltuwa [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD kwanaki sunja shekaru sun tafi har zarah ta manta ta hada haddarta yanzu gashi har zarah na ss3 girma ya gama bayyana kyau iya kyau akwaishi yanda kasan ita tayi kanta ga kira me kyau Allah ya bata diri iya diri tana dashi komi son barka tana zaune a palour tana karatu mommy ta fito tace ya maganar gyaran dakina ko so kike yau ya zauna a haka Tace a'a mommy yanzu na gama gyara dakina na ban dade da zama ba tace kina iya tashi kije ki gyara min husna dake kallo tace nima ga dakinmu can a hautsine juma duk yau bata gyara mana ba Zarah tace kuma kenan da ake gyara maku ta