Sashe 16
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wuce mommy ta kalleta tace yanzu husna haka zaku zauna ba zaku ma kanku komi ba haka zakuyi aure baku iya komi ba baga girkin ba baga tsaftar wuri ba ta zunbura baki ta tashi ta bar wurin zarah na gama gyaran dakin ta wuce kitchen ta tadda har gaje ta fara aiki tasa hannu suka ci gaba aikin tace ai inna gaje na manta inata sauri in rigaki shiga kitchen macaroni soup yau naso muyi tace kash gashi na riga na daura tace ba damuwa se kuma gobe in Allah ya kaimu suka gama ta shiga tayi wanka taje ta samu mommy tace mommy zanje saloon tace ba inda zaki tace mommy ki temaka min bana jin dadin kaina tayi banza da ita yaya mansir dake zaune yace mommy ki barta taje Hakanan ta hakura ta barta tace saura ki dade ta shiga ta daura jallabiya akan kayanta ta fito tayi kyau abinta tace mommy sena dawo Yaya mansir yace mommy ya kamata ki kyaleta hakanan tunda wahala de a gidan nan ai ta wahala duk wanda yasan zarah a gidan nan tace to naji ubana Zarah na fita ta samu bala tace zamu fita tana shiga tace gidan su siyama zaka kaini yace to ya mika unguwansu suna isa tace da la'asar kazo ka daukeni yace to ya tafi ta shiga siyama na ganinta ta tashi ta rungumeta suka shiga ciki ta gaida mommyn siyama suka shige dakinta suka hau fira siyama tace baki ce ina yaya hisham ba yana nan shifa da gaske yake har cewa yayi sena kaishi gidanku nace wai ai gidan nan baze samu zuwa ba dan zarah cike take da matsala a gidansu Zarah tace haba siyama duka nawa nake dama zan fara tsayawa da samari ai har yanzu ban isa aure ba Siyama tace ai naga alama se ga muryanshi siyama tace kinga dan halak UKUBA Na EASHA MD yaya hisham ya shigo ya taddasu ya ware idanu yace zarah tace yaya hisham barka da aiki yace yauwa kin boye tace ina nan siyama ta mike tace sorry kawata muna ta surutu ban kawo maki komi ba ta fita yabi zarah da idanu ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da hannunta yace zarah da gaske nake yi idan kika gama secondary school se ayi maganar aure Ko ina kike so kiyi karatu zan tsaya maki da zarar munyi aure ko ya kika gani kinyi shiru haba my baby tace yaya hisham to me zance yace idan kin amince ki fada min ki dena jin kunyata idan ban maki ba tell me kada ki boye min komai ta dago suka hada ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta yace kin amince kenan ta rufe idonta siyama ta shigo yace ni bari in fita zan dan shiga na kwanta kafin la'asar in ta tashi tafiya kimin magana se in maidata tace ai za a zo daukana yace nide a fada min ya fita siyama tace ya to kawata yayana ya samu shiga ko tace siyama ni maganar soyayya baya gabana kuma ina jin kunyar in fada mashi saboda ni karatu nake so nayi tace baki ganshi bane yayana dan boko ne bana shakka a kanshi ko nawa ne ze kashe miki tace baki ga duk gidanmu se sun fara karatu suke aure ba kinga yanzu ma salma ta fara danma ta samu miji da wuri kinga an kusa auran nifa kunya ma nake ji inga na fara tsayawa da samari duka nawa nake yarinya ce fa ni mtsww ta danja karamin tsaki tace har yana wani cemin baby se kace wata yarinya siyama ta kwashe da dariya tace yanzu fa kika gama cewa baki isa aure ba au kuka zaki min haba baby kada kiyi kuka ta kai mata duka ta kauce tana daria zarah tace ni tashi ki gyara min gashina dan cema mommy tace nayi saloon zani ta mike da sauri tace banga ta zama ba dan bana so a taba auntyna kuma kawata zarah tace kede kika sani ta wanke mata kai ta dauko hand dryer ta busar da kan ta gyara mata shi yayi kyau tace wow matar yaya kinyi kyau yanzu abu daya ya rage ki bari na tsantsara maki make up dan yau so nake ki zama kamar amarya kina da kyau amma bakya son kwalliya ko dan kinga ko baki ba kina kyau murmushi kawai tayi siyama tace yau fa sena maki ta kara murmushi sannan tace yanzu idan kika min mommy ta ganni tace saloon din kenan tasha ba can naje din ba tace haba ba zata gane ba ai akwai saloon din da suke make up se kice a can aka maki zarah ba yanda zata yi dole ta tsaya aka mata [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD siyama na gama mata ta kalleta tace aljannar duniya wai sharhabila cancadi makadi kawata kinga yanda kika yi kyau ko makiyinki ne se ya waigo ya kara kallonki dandan kallo daya yayi kadan tashi ki kalli mirrow tayi murmushi ta mike ko ita kanta seda ta birge kanta ta kara kallon kanta murmushi kawai tayi zarah tace ga dimple din nan kara maki wani sihirtaccen kyau yake tace kede siyama kina da matsala tace matsala kuma daga fadin gaskia ai zarah ko ni kin birgeni tana zaune akayi la'asar seko ga bala ya iso siyama tace aikuwa se nayi sallah zaki tafi seda ko ta jirata ta idar suka fito mommy tace zarah har kin fito tace eh mommy tace jirani na fito ta shiga ciki ta fito da leda me dauke da turaruka a ciki ta mika mata tace mommy na gode tace to zarah ki gaida gida ta fito Sega hisham ya fito ya jefeta da harara yace shine zaki tafi ba muyi sallama ba ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi yace da sede inji kin tafi ba ni nace zan maidaki ba tace ai an riga an zo daukana shiyasa yace to shikenan nan se yaushe kuma tace se kuma na Kara zuwa yace naki har gida zanzo tace base kazo ba ai nakan zo gidan nan Siyama tace ba wani yaushe kike zuwa gidan tace zanma dawo ta shige mota siyama tace se mun hadu a school sukayi sallama ta tafi tana isa gida Ta shiga mommy tace se yanzu kika ga daman dawowa tace a'a mommy da mutane da yawa shiyasa ta kauda kanta ba tare da ta kara ce mata komi ba zarah ta mike ta shiga daki ta kara daban kanta a madubi tace haka kawai duk ta bata min fuska ni wankeshi ma zanyi ta shiga toilet ta kara yin wanka ta canza kaya ta fito Kwanci tashi ba wuya gashi har su zarah sun fara ssce sun fito suna maida bayanin exams yaya deen ya iso ta kalleshi da fara'arta tace yaya deen se yau nake ganinka yace ki bari kawai zarah aiki yamin yawa ne daddy ya riga ya sakan min komi na company dinshi yanzu bama cika fita yayi ba komi sede ni yace to ya exams din tace ba laifi yace to Allah ya temaka tace Amin yace siyama ya kokari zarah ta hana mu gaisa tace aikuwa yaya deen Zarah tace yaya deen wai ya maganar aure ne na gaji da ganinka fa a haka yaci ace ka aje mata fa yace zarah akwai abinda nake jira har yanzu tace kullum yaya deen se kace akwai abinda kake jira na rasa menene wannan abu in kudi ne ka samu in gida ne ka samu ba abinda ka rasa kafa yi girman daya kamata ace kana da mata yace to yanzu na tsufa ne tace sosai kuwa yace tofa wadda kuma nake so ashe idan na furta mata se tace na mata tsufa siyama tace haba yaya deen fadar zarah ne kawai waye ze ganka yace ka tsufa ai yanzu ma ta fika tsufa yace tofa ashe ma zarah ta fini tsufan zarah ta harari siyama tace keko suka kwashe da daria yace to gudun tsufan kike tace ba dole na guji tsufa ba kaima da kayi shekaru ka tsufa kana gudun tsufan bare ni yarinya yayi daria siyama tace mude bamu ga tsufa a jikinshi ba a naki muka gani tace to ai se kuyita yi yaya deen tashi ka tafi yace au korata kike aiko idan na tafi zaki shekara baki ganni ba tace dafa wasa nake yace to naji na hakura amma zaki dan kwana biyu baki ganni ba saboda zan danyi wani tafiya se in na dawo tace har zuwa yaushe yace zande yi wata daya kacal tace wata dayan ne kacal kafin ka dawo ma mun gama exams dinmu yace haba tace da gaske yace to se in na dawo din amma banso haka ba tace nima haka Ya masu sallama yace zan wuce suka ce to a dawo lafia ya ciro kudi a aljihu ya mika mata gashi kwayi amfani dashi dan nasan siyama kike bari da wahala siyama tace haba wane wahala ai mun zama daya ta amsa suka yi godiya ya tafi zarah ta mika mata kudin tace amsa ki aje a wurinki tace kide aje tace haba dan Allah nide ki amsa siyama ta amsa ta aje masu komi de nasu tare gwanin ban sha'awa abinsu Kwanaki na gudu har sun gama exams se zaman jiran fitowarshi [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD zarah na zaune duk zaman gidan ya isheta saboda takuran mommy burinta taga ta fara karatu jira kawai take Result ya fito tunda tayi jamb dinta taci husna ce dama point dinta be kai ba tayi shiru ta lula tunani a ranta tana ko inyi auran kawai in auri yaya hisham din in huta da tsangwama na gidan mommy nima in samu yancin kaina kuma ai ba sonshi nake ba ina so na auri wanda nake so To kuma idan naci gaba da zama jiran wanda zanso zan kare a wahala kuma burina inyi karatu wani zazzafan hawaye ya gangaro mata gaje dake kanta tsaye tace zarah lafia tun dazun nake miki magana naji shiru kuma ga hawaye a idonki tace inna gaje aure nake so nayi saboda na huta da tsangwaman gidan nan Gaje