← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

saurayi baze nuna maki ba fatana ki saki jikinki [9/28, 9:44 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD tade dukar da kanta taki magana yace kira siyama muyi sallama zan wuce ta shiga ciki siyama tace har ya tafi ne tace yade ce kizo kuyi sallama ta mike suka koma tace har zaka wuce yace eh tace to mun gode ya kira driver dinshi ya shigo da katuwar jaka yace to gashi zarah tace a'a ka barshi bece komi ba ya mike ya mika ma siyama kudi ta noke yace ai ni na bagi gashi ta amsa tayi godiya ya tafi siyama ce ta dauki jakan suka shiga ciki siyama ta bude turaruka ne masu kamshi da tsada se kayan shafa siyama tace be san matar tashi yar kauye bace bata son kwalliya turaren de nasan wannan ana sonshi zarah ta harareta tace ni kinga ma abinda ya kawoni ban fada maki ba saboda tashin hankalin da nazo na taddaki Tace fada min tace aure zanyi nida yaya hisham rana daya zarah tace haba tace da gaske dama kina da wanda kike so baki fada min ba tace a'a duka ma fa cikin satin nan muka hadu dan abokin abba ne sunanshi mubarak zarah tace na tayaki murna kawata shi kuma yaya hisham ba tace diyar kanwar mommy ce zarah tayi shiru Siyama tace to ni zan tafi ai na maki wuni zarah tace ki dau abinda kike so a ciki siyama ta dau Turare biyu da wasu kayan shafan sannan ta mika ma zarah kudin tace gashi nasan zaki so kiyi amfani da kudi tace a'a siyama haka siyama ta aje mata ta fita ta rakata tana dawowa ta dauki kayan ta boye dan ba amfani zata yi dasu ba Haka zarah taci gaba da rayuwa cikin damuwa gashi ta hana su hadu da yaya deen kwata kwata shi kanshi ya rasa yanda zanyi da rayuwarshi Ga bikin salma yazo se shirye shirye ake ranar da su goggo dije tazo taga yanda duk zarah ta rame tace zarah meke damunki ciwo kika yi tace a'a daddy ne ya badani aure ga tsoho Goggo dije tace tsoho kuma eh tsoho duk ta fada mata yanda akayi tace share hawayenki ba wanda ya isa ya aura maki wanda baki so sha kuruminki kici gaba da hidimanki yanzu tashi ki shirya ba party zaku ba tace eh to tashi ki shirya abinki taje ta shirya tayi kyau sosai yanda kasan itace amarya fitowanta duk wanda ke wurin seda ya juyo ya kalleta zarah bade kyau ba sun isa wurin party din da aka kawatashi siyama ta kirata tana dauka tace haba kawata inata jiranki tace gani a wurin fito ta fita taje wurinta suna tsaye suna magana ganin yaya deen tayi UKUBA Na EASHA MD zarah na ganin yaya deen ya kama mata hannunta kafin siyama tayi wani yunkuri har ya sata a mota ya figi motor yayi waje tace yaya deen ina zaka kaini ko kallonta beyi ba yaci gaba da tafiya suka isa wani hadadden gida ya saki horn me gadi ya bude ya shiga yana fitowa ya bude inda take ya kamota ya shiga da ita ciki ta fara kuka tace yaya deen meyasa zaka kawoni nan Ya dago ya kalleta da idonshi da yayi ja yace zarah kalleni da kyau da haka nake dibi yanda na koma akan sonki na rame har gadon asibiti na kwanta saboda ke ya nunata na kasa tsayawa na kalli wata mace face ke ke na tsaya jira naki aure tun kina cikin zanin goyo nake kaunarki amma da abinda zaki saka min kenan ki kara kallona kin taba ganina a haka Na kasance cikin farin ciki a da tunda na furta ina sonki na shiga damuwa Inada aibu ne da bakya sona kika tsaneni me kike tunanin rayuwata a nan gaba yaya zanyi da rayuwata bayan idan banyi rayuwa dake ba Zarah inaso kiji abinda nake ji a zuciyata ko zaki gasgata maganata zarah meyasa ba zaki soni ba inaso kiyi farinciki da walwala zan maidake kamar sarauniya a fadin duniyar nan ya dafe kanshi zarah ta kara sakin wani kukan yace ya isa ya isa me kike kuka akwai abinda ze dameki ne in na mutu kin wahalar dani ki fita a cikin raina inaso na manta dake zarah nayi tunanin kinzo duniya ne saboda ni ina jin kamar..............
Chapter 20 · 0% Book details