Sashe 7
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
malaman na gaida zarah sun wakiltamu zuwa gaidata halima tace mun gode suka ce zarah ya jikin naki tayi murmushi malama sadiya taja mata kumatu tace baki magana halima tace ai jiki ya warware malama suwaiba ta gyara zama tace wai ko maman zarah meze hana ki dauki yarinyarki tunda ba rasa abinda zaki kula da ita kikayi ba halima ta canza fuska tace wllh malama nima abinda naso nayi kenan sede ba yanda zanyi babanta ya matsa se an bashi mahaifina yasa ni dole seda na bada gashi kuma an kasa mata rikon kirki malama sadiya tace ai tada hankalin kowa zaki yi se kin amshi diyarki yarinya duk tabi ta lalace tace abinda naso nayi kenan se a dankwafar dani amma abin yana damuna amma wataran hakan ne ze faru nan de suka gama maganarsu suka masu sallama suka tafi amma tace auta naji duk abinda kuka tattauna nade yi shiru ne amma ina me shawartanki da kibi komi a hankali tade dukar da kanta kasa ba tare da tace komi ba sega kamal ya shigo ya gaida amma halima tace ba yau monday ba meya hanaka zuwa school bayan na baroku kuna shiri yace zarah nake tunanin jikinta ko naje ba abinda zan iya yi tace to baga zaran ta warke ba amma tace yako je amaryarshi ba lafia yayi murmushi aunty tace to duk su khadija sun tafi ko yace eh mommy ta shigo ita da bala ta gaida amma yame jiki aunty tace jiki alhamdulillah kafin ta koma ruwa bala shima ya gaidata amma tace ya yara tace yara lafia lau duk sun tafi makaranta ba wanda na baro kwance amma tace ai haka akeso ta tashi tace mun tafi Allah ya karo sauki tace ameen amma tace ke kiji mata se kace ance mata wani ana so wani nata ya kwanta aunty tace ai ni ban dauketa me hankali ba zarah tace aunty amma ba zan koma wurin mommy ba ko saboda bana son gidan yauwa aunty wai ya akayi kika san ruwa na shiga naji kince ma mommy kafin in koma ruwa aunty tace a'a ban sani ba dama ruwa kika shiga tace eh mommy ta koroni waje ana ruwa kuma ta rufe dakinta kamal ya shigo yace azzalumar matar nan ta tafi amma tace eh dama saboda ita ka fita yace aikuwa sbd bana son ganinta dan zan iya dukanta zarah tace yaya deen dama baka fita ba ka rama min ai ba zan koma ba aunty dan Allah kada ki maidani ta kalli aunty taga tana hawaye ta fara share mata tace aunty me ya saki kuka sbd nace kada ki maidani to kada ki kaini gidanki yaya deen ka daukeni ka kaini wuri me nisa inda kowa baze ganni ba yauwa amma dama kince maiduguri nada nisa a kaini can kinga mommy ba zata ganni ba dasu yaya mansir masu dukana tace aunty har yanzu kukan kike harda ke amma itama seta fashe da kuka kamal ya mike ya fita sbd baze iya jurewa ba doctor ya shigo ya dubata yace jiki yayi sauki yau se gida yayi rubucenshi ya sallamesu seda suka fara kai amma gida sannan suka wuce zarah tace yaya deen bade gidan mommy zaka kaini ba yace a'a zarah ta hau murna suna isa gidan kowa da murna suka tareta minal tace zarah kinzo kenan ba zaki kara tafiya ba ko tace eh mana khadija tace aunty har munji dadi da kika dawo amma da baki wuni gidan ba dadi tace gashi ai na dawo goggo rabi ta fito tace an sallamoku tace eh goggo rabi taja zarah tace muje na maki wanka taje ta mata suka dawo ta shiryata goggo rabi tace kinde daukota kenan ko tace a'a zade ta kara samun sauki seta tafitafi kinga saura sati 1 jirginmu ya tashi tace base ki barta wurina ba tade yi murmushi goggo rabi tace yanzu ba gashi kin rike mana yara da gaskia ba kowa ya budi baki se sam barka da godia gareki ai ba muda abinda zamu saka maki se godiya da addu'a a gareki amma kin bar taki a wulakance murmushi ta kara yi [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 zarah ko ta saki jikinta se wasa take har bata so taji an mata maganar su mommy ranar da zata koma daddy da kanshi yazo daukanta duk ta cika gida da ihunta daddyn kamal ya kirata taje yace zarah baki son komawa tace eh daddy kada ka bari na koma duka gidan mugunta suke min su inna gaje ne kawai suke sona dasu bala amma su mommy da yaranta basu sona har barina da yunwa ake ace abinci ya kare in tafi school banyi breakfast ba tana fada tana hawaye daddy yace zarah ba zan kara bari wani yaci zalinki ba kinga bana zama a gida tace tunda baka zama a gida ka barni a nan yace kiyi hakuri zan rinka baki kulawa share hawayenki kinji ta goge daddy ya gyara zama yace to alh bashir kaga ya kamata ka rinka jan yarinyar nan a jikinka yace insha Allahu daddy yace zarah ga kayan makaranta ki rinka tafiya dashi ta kalla taga bobo caprisonne da biscuit tace daddy ba zanje dashi gida ba sbd idan naje dashi ba za a rinka bani ba kwacewa zatayi kaga ma duka kayan wasan da ka siya min duka ta amshe taba husna daddy yace ka gani ko Allah ka gyara tsarin gidanka tun kafin nan gaba ya gagareka aunty tace tun yaushe ya gagareshi haka zarah na kuka ya tafi da ita aunty tace ki dena kuka dana dawo makka zanzo na daukeki itama ta wuce daki tana hawaye goggo rabi ta bita tace haba auntyn Yara kiyi hakuri kada kisa damuwa a ranki kizo wata cuta ta shigeki gara ki amshi yarinyarki ko mu sbd sabo da ita mun shiga damuwa ga yara can ma kuka suke ganin kinayi dan Allah kiyi shiru tace goggo rabi ya zanyi tace kawai ki amshi diyarki tace bari mu dawo makka inga yanda za ayi suna isa gida cikin tsoro da sauri ta shiga dakin dan karta hadu da kowa kafin ta ida shiga dakin mommy tace waye da sauri ta C dawo da baya ta duka ta gaidata taki amsawa taci gaba ta daka mata tsawa tace dole sena amsa tashi ki bani waje da sauri ta mike ta bar wurin daddy ko ya kasa ma mommy magana se yayi yunkurin mata mgn seya kasa haka zarah taci gaba da fuskantar tsangwama da UKUBA daddy ya fita ze koma abuja da sauri zarah ta fita ta sameshi yace zarah ya akayi tace daddy har yanzu daddy da dasu aunty Khadija basu dena min abinda suke ba ko baka ma mommy maganar ba ya shafa kanta cikin tausayawa yace zarah nayi amma idan na dawo zan kara masu mgn kinga yanzu yamma tayi ban tafi da wuri ba tace to har ya shiga mota ta kara tsaidashi yace ya akayi kuma zarah tace daddy bafa a bani abinci idan zanje school wataran m bana ci nake tafiya yaya deen ke kawo min kuma ya tafi makka shima ya dau yan naira hamsin na dubu daya ya bata yace ki boye ki rinka kashe hamsin ko dari tace na gode ta shiga gida shi kuma ya tafi tasa kudin cikin jakanta a haka ta samu in anyi break take siyan wani abin malama suwaiba ta kirata tace zarah naga kina kashe kudi bade na wani kika dauka ba ko ta girgiza kai tace a'a daddy na ya bani zarah kudi ya kare ta koma gidan jiya haka take zama taci kuka idonta gaba 1 ya jagwale sbd kuka gashi ya hadu da ciwo kuma be samu kula ba tana zaune a jikin bishiya tana kuka malama suwaiba tazo ta sameta tace zarah me kike a nan har an koma class ke kadai ba kowa tace anty yunwa nake ji tun jiya da rana dana ci ban kara ci ba da kanta ta fita wurin me tea ta hado mata mai kauri da kwai da indomie ta kawo mata taci sosai sannan suka koma class wata sabuwa komawarta class ido yace be san da rubutu ba ya rufe ruf [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA AMD 2 malama halima tace zarah me kike baki rubutu tace aunty bana gani hawaye ya gangaro mata oh zarah zarah dena kuka idan kina kuka zeci gaba da maki ciwo duk takaici ya isheta a zuciyarta tace wato mamanta taki daukan shawara tun zarah na kukan a hankali har ta fara da karfi malama suwaiba ta dauketa ta kaita sick bey bayan sun dawo tace zarah gobe kada kizo tace aunty nafi so nazo sbd gidan ba dadi malama suwaiba ba tace mata komai ba haka ta daura kanta a kan desk ta hau barci bata tashi ba seda aka tashesu suka wuce gida suna isa husna tace mommy yau zarah ba abinda tayi a class se barci take kuma daka dawo break ma bata dawo class da wuri ba seda aka dade mommy ta harari zarah tace ina abinda ya dameni data yi karatu da kar tayi ba asarata bace asararta ne tashi kije ki cire kaya husna ta mike mommy tace kefa tashi a gabana kinzo kin kafeni da ido ta mike tabar wurin sukuku khadija ta shigo ta fada kujera tace wash mommy na gaji tace kin dawo nayi tunanin zaki kwana a zaria tace ai iyakata ma cikin makarantar mommy tace kin gama komi ko tace na gama yanzu next week zan koma can na fara daukan lecture tace to Allah ya taimaka tace Amin zarah ta fito ta zauna khadija tace ke zubo min abinci ta mike da sauri ta zubo mata sauran daya rage a flask din tana tafe tana kallon su husna nacin abinci bata ankara ba taci tuntube da kafan mommy ta fadi abincin ya zube har seda ya zuba a jikin khadija khadija na tashi ta dauketa da mari ta fasa wani uban kara sbd marin ya shigeta sosai mommy tace munafuka da gangan ta zubar jawo min ita ta fara ja baya tana kuka tace wllh mommy