Sashe 13
Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yarinyar nan diyar dan uwanmu ne duk da halin ko in kula da yake nuna mana dole shi jininmu ba zamu taba canza shi ba Hajia safiya tace hakane amma dije ina so ki rinka zama me hakuri goggo dije tace ai raini ne ba naso shiyasa kuke daukana mara hakuri suna ta fira daddy ya iso gidan zarah na palour da sauri ta tashi ta shige dakin dasu goggo dije suke Goggo dije tace ke lafia ta zauna tace muryan daddy naji tace to shine kike gudunshi se kace ba mahaifinki bayan yayi wanka yaci abinci Ya zauna yana hutawa goggo dije ta shigo shiga palour dinshi da sallama ya amsa mata suka gaisa yace kun iso hidima kenan tace aikuwa tun shekaran jiya yace to sannunku Allah ya bar zumunci tace ameen itama yaya safiya na can daki yace a to muje can suka koma can dakin suka gaisa suka dasa firan zumunci zarah ta shigo dakin hajia safiya tace ina kuma kika je tace ina dakin su inna gaje Daddy yace ke me ya hanaki bin yanuwanki da sauri ta duka dan bata lura yana dakin ba ta gaidashi yace ya akayi baki je ba tayi shiru goggo dije tace ni na hanata saboda naga idan har tana kusa dasu ko ruwa gagaranta sha yake shiyasa na hanata zuwa Taci gaba da magana tace wai ko yaya bashir kana addu'a kuwa ko kudi kawai kasa a gaba yace ina yi dede gwargwado hajia safiya tace ai ba a zama dagewa zaka yi yanzu jibi yaushe rabonka da zaria ka kai fa shekara uku sunan kana da yanuwa a can harda kanwar mahaifinka fa uwa daya uba daya tun tana magana har tasa ma ido koda kake gani ba iyayenmu sun rasu ai akwai yanuwanka kazo a gaisa ma ai arziki ne ko da yake ba laifinka bane na wannan hatsabibiyar matar taka ce da se taga ta rabaka da duk wani naka kuma ai ita tana zuwa zaria ko tunda tana son yanuwanta sa'a ma muka ci ta aika mana da bikin Yace dan Allah kuyi hakuri kude ku ci gaba da tayani addu'a tace muna maka kuma ba zamu fasa ba yace to na gode Goggo dije tace zarah jeki wurin su gaje ko muna magana ta tashi ta fita Goggo dije taci gaba tace ai seda muka kwashi yan kallo da matarka yace subhanallahi garin yaya tace a kan zarah mana kana zaune ana gasa yarinya a cikin gida tun tana tatsitsiyarta ya kamata fa ka dauki mataki ka zama namiji a cikin gidanka ba mace ta rinka juyaka ba hajia safiya tace gaskia yace ni kaina ba a son raina haka ke faruwa ba bade yanda zanyi ne ko nayi yunkurin inyi magana sena kasa saboda tana nuna min tarbiya take bata goggo dije tace a tarbiya kam gashi nan tana bata yaya idan ba zaka damu ba ka bani zarah na tafi da ita yace to ai kuma karatunta tace zaria ai akwai makarantu masu kyau da za a sata ai ba abinda ze gagara iyaka ka biya mata tana can ita kanta zata fi sakewa a can tayi karatun yace to shikenan bari a gama hidiman bikin ko se ku tafi amma kuma da zanso idan ta gama jss1 dinta zefi tunda sun kusa fara exams kuma promotion exam da kun tafi seta fara jss2 ko ya kika gani tace ai can din duk 1 ne yace to shikenan bari a gama bikin ko tace to na gode yayana yayi murmushi yace ai ke dije bame iya maki se ni hajia safiya tace ai shiyasa nayi shiru saboda in kuna tare mantawa kuke da wanda ke kusa daku dan ku ba a sanin cikinku suka kwashe da daria tace to duk naji komi nide fatana Allah ya tayaki rikonta ya baku hakurin zama da junanku dan rikon dan wani seka jure suka amsa da ameen a tare [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA na EASHA MD 3 ranar daurin aure gida ya cika makil da yan biki se hidima ake zarah ta gama shiryawa tsaf tayi kyau abinta bare dama wurin kyau ba daga baya ba ta fito goggo dije tace kai zarana kinyi kyau farar mace alkyabbar mata mommy ta juyo ta kalleta ta buga tsaki goggo dije tace diyata ta kaina a ganki a kyale sede a buga a barki mommy tace wai ke dije me kike nufi ne tace kamar ya fa nida diyata kuma ban isa tayi kyau na yabeta saboda kina wurin tace ai naga abin naki ne da isgilanci hajia safiya ta fito tace haba dije wai ke kin girma amma har yanzu ba zaki canza halinki ba tayi daria tace me kuma nayi gaskia ce fa dole a fada mommy ta kalli hajia mero tace yanzu sede ina kallo wannan matar taita fada min magana idan fa na barta hawan jini ze iya kamani Hajia mero tace ai se kinso hawan jinin ze kamaki Tunda da tayi magana ta ambaci sunanki goggo dije tace fada mata de mommy tace to da dawa take in ba dani ba na rantse da Allah zan dauki mataki yanzu Hajia mero tace idan kin dauka ke zaki ji kunya tunda jama'a de ke kika tarasu gara ki daure ki rabu da kowa lafia Ke kuma dije dan Allah komi ya wuce tunda tun jiya akayi tace to ni yanzu me nace in ba jirana take ba ni yanzu ma zan bar mata gidan se taji dadin yin bikinta zarah taso muje bala ya shigo tace yauwa bala zo ka kaini wani unguwa Mommy tace amma ai kinga hidima ake dole da aiken da ake mashi tace wannan kuma ba damuwata bane bala muje mommy tace aiko ba inda zashi saboda aikenshi zanyi hajia mero tace bashi aiken idan ya sauketa inda zata se ya wuce miki aiken mommy hakanan ba yanda zata yi ta yarda bayan sun shiga motar tace bala gidan maman zarah zamu Yace to suna tafe yace amma goggo dije naji dadi da zaki kaita ta gaisa da mamanta tace aikuwa yarinya ta zauna se bakar wahala take ci bala yace ai matar nan nake fada maki ba Allah a tare da ita ko kadan ki duba kiga hajia halima mace me hakuri da kawaici amma seda taja mata sharrin da ta bar gidan nan Tace ai bala ka barni da ita nice maganinta kuma ina nan watarana seta zauna da kishiyar da zata addabeta cikin gidan nan Lokaci nake jira bala yace ai shine daidai makirar mata kawai a haka har suka isa gidan suna shiga duk suna palour da gudu suka rugo tararta aunty ta fito tace lafia ihun me ake goggo rabi tace babbar bakuwa mukayi ta washe baki tace aa goggo dije ce ashe zamu kara haduwa Tace aikuwa bismillah zauna tasa baba jummai ta kawo mata kayan makulashe zarah tace ina yaya deen naga ban ganshi ba minal tace yana dakinshi Da sauri ta tashi ta shiga dakinshi cikin murna yace wa nake gani kamar zarah tace nice mana yaya deen ke dawa kika zo waya kawoki da saninsu kika zo Tace nida kanwar daddy ne haka ta zauna sunata fira goggo rabi ta shigo ta kamo zarah tace tashi muje haka ake yi seka riketa kai kadai muma muna son ganinta ai yayi daria shima ya mike suka dawo palour aunty kanta ta kasa boye murnanta tace zarah kin shigo kin ma kowa magana amma banda ni laifi na maki kike fushi dani ta fara hawaye tace bake bace kin dena zuwa wurina Tace Allah sarki ba kin zuwa nayi ba aiki ne ya boyeni tace to amma ai baki sona tace ya za ayi naki sonki goggo dije tace gaskia baki kyauta ba ai diyarki ce ya zaki saketa aikinki ya fita mahimmanci ne koda ace kina jin haushin babanta ita ai ke kika haifeta tace bama haka bane tace to banji dadin sakinta da kika yi ba tunda ai kin san halin hafsa aunty tace saboda zarah har nan suka zo suka ci min mutunci kin san halinta tace nima zuwana din nan seda mukayi da ita duk akan zarah gaba daya ta riga ta mallake yaya ne se yanda tayi dashi tunda ko rabuwanku dashi ba yanda bamuyi ba ya dawo dake amma yaki wanda sanadin haka fa hajia saude ta cire hannunta a kanshi kinde san yanda take sonshi amma yanzu ko maganarshi bata yi a matsayinta na kanwar mahaifinmu ai dole muji maganarta aunty tace gaskia be kyauta ba amma sede hakuri goggo dije tace idan kuma ka ritsashi sede yace be san me ke faruwa ba aunty tace addu'a kawai za aita tayashi kawai goggo rabi tace shine kawai Allah yasa a dace kawai amma irin matan nan idan Allah ya hadaka dasu to shine kawai ze kawo maka dauki a ciki aunty tace hakane [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: UKUBA Na EASHA MD tace shine kuka baro gidan bikin goggo dije tace ai mu da gida se dare yau yawo zamu sha har gidan ahmad se munje da wurin amma zarah ta zunburo baki tace ni gidan uncle ahmad kawai zani ba zanje gidan amma ba goggo dije ta mata dakuwa tace kinga naki akan me zaki ce ba zaki gidan amma ba wani abu ta maki tace bata min komi ba baffa ne bana so ya ganni tunda shi ya rabani da mamana suka dauki salati Aunty tace waya fada maki haka kada in kara jin kin fadi haka goggo dije tace ai se in tashi in bibbigeta a wurin gidan amma ne se kinje kin gaidasu ta tashi ta fara kuka ta fita kamal ya bita yace haba zarah miye na kuka Yanzu fa kin girma duk wanda yaga kina kuka ze maki daria ne haba zarah Tace ai ni gidan amma ne bana son zuwa yace to me suka maki gidan da kike zaune ba gashi suna azabtar dake ba ya kika yi dasu haba Su amma kakanninki ne dole suna sonki dande ba yanda zasu yi ne kuma ai basu raba ki da aunty ba dan haka ki dena fadin haka kinji tace eh naji amma fa ba zani