← Book details Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 24

Sashe 1

Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data *UKUBA* EASHA MD zaki bar min gida yau din nan bana son ganinki, na tsaneki halima tace amma alhaji ai ka bari se gobe in tafi ko tunda dare yayi, ga tsohon ciki, ya zanyi ya kalleta cikin bacin rai, yace miye amfaninki da har zan bari ki kwana a cikin gidana, kamar yanda abincinki da ruwanki ya kare a cikin gidan nan, haka kwananki ya kare a ciki dan haka tashi ki fita, halima tace amma. alhaji....shissh ya daga mata hannu alamun baya son jin komi daga gareta, da kanshi ya dagaka, ya fita da ita tana hawaye, hajia maryam da aka fi sani da mommy ta daga hannu sama, tana mai gode ma Allah tace kai Allah mun gode maka daka rabamu da kaya, a gayas umma ta gaida asha haka ta fita cikin daren nan kusan 11 na dare, ta tunkari titi, tana tafiya gashi ba motan hayan da zata ce ta shiga ya kaita unguwan da take, haka tana tafiya tana hawaye, bata ankara ba, ta fadi a kasa, ga nakuda ya taho mata gadan gadan, haka ta duke a kasan nan, tana murkusu ya Allah kaine abin godiya, kai ka daura min jarabawan nan, Allah ka kawo min agajinka, wani mai mota ya faka motarshi, subhanallahi! hajia lafia? sannu tashi muje asibiti, da kyar ta yunkura da temakonshi ta shiga motan, yaja yayi asibiti da ita , isar su asibiti, aka amsheta da gaggawa, sbd ta fita hayyacinta, bata san wanda ke kanta ba, [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: nakuda ya dauketa, tsawon lokaci, wanda ya kaita har safiya, halima tana abu daya, bata haihu ba, duk tabi ta galabaita, bata san wanda ke kanta ba, doctor ya fito yana neman wanda ya kawota, wata nurse da suke tare, tace mashi ai be riga ya iso ba, yace to in ya iso kice ina son magana dashi, tace ok sis, ya wuce, ba a jima ba, se gashi ya iso asibitin, nurse ta fada mashi sakon doctor, yace to ba damuwa, ya shiga office dinshi, ya sameshi, suka gaisa, yace dama abinda yasa nasa kazo, sakamakon nakudar da matarka ta dade tana yi, ya zama dole a mata operation, saboda ba zata iya haihuwa da wuri ba, muna bukatan sa hannunka, dan gaskia za a iya rasa rayukansu, daga ita har baby din dake cikinta yace to ba damuwa, haka yasa hannu, aka shiga da ita thearter room, se fatan Allah ya fito da halimatu lafiya, ita da baby din dake cikinta, [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: bayan gama mata operation, aka fito da ita, dakin da zata huta, baby kuma aka shiryata, aka miko ma bawan Allah daya temaka mata, yace har kun fito? tace eh insha Allahu zata farka itama nan bada jimawa ba, yace to shikenan, sannunku, yace: tunda Allah yasa an gama mata operation a sa'a, zanje in dawo zuwa anjima, ga baby din se ki kula da ita, ta amsheta, shi kuma ya tafi, zuwa yamma halima ta farka, doctor ya shiga ya kara dubata, aka hadata da baby dinta, bayan sallan magriba, se gashi ya shigo ya sameta, kwance ga baby don't a kwance kusa da ita, yasa hannunshi ya dauketa, ya samu kujera, ya zauna, yace mata sannu ya jikin naki? tace da sauki, yace ai alhadulillah aikin yayi kyau, dan gashi kin samu sosai, sunana alhaji aliyu, dana kawoki nan, tace na gode, Allah yasaka da alkhairi, ya mike ya aje baby din, da kanshi ya hada mata tea, ya mika mata, ta amsa tace na gode, ya kara daukan baby din, yace yarinyar nan ta birgeni sosai, ta shiga raina, ina jinta sosai a raina, halima tayi murmushi, tace na gode. bata ankara ba, hawaye ya zubo mata, yace subhanallahi! baiwar Allah lafiya kuwa? tace bakomai, yace a'a akwai saboda hakanan zaki hau kuka? ta kara cewa bakomai, yace to shikenan, ba zan takura maki sai kin fada min ba, yauwa ina ne gidanku? saboda a fada masu su san halin da kike ciki, tace ina unguwan dosa ne, ta mishi kwatancen gidansu, yace to insha Allahu zan samu naje zuwa gobe, ko yanzu idan na fita, tace to na gode sosai, yace kada ki damu, bari in samu in tafi ana kiran isha'i, daga can zan wuce gida, se gobe na Kara zuwa, tace Allah ya kaimu, bayan fitan shi, ta kalli baby dinta, hawaye ya kara sauka a fuskanta, tace Allah ka raya min ita, ka tsare min ita daga duk wani sharrin halitta, [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: bayan gama mata operation, aka fito da ita, dakin da zata huta, baby kuma aka shiryata, aka miko ma bawan Allah daya temaka mata, yace har kun fito? tace eh insha Allahu zata farka itama nan bada jimawa ba, yace to shikenan, sannunku, yace: tunda Allah yasa an gama mata operation a sa'a, zanje in dawo zuwa anjima, ga baby din se ki kula da ita, ta amsheta, shi kuma ya tafi, zuwa yamma halima ta farka, doctor ya shiga ya kara dubata, aka hadata da baby dinta, bayan sallan magriba, se gashi ya shigo ya sameta, kwance ga baby don't a kwance kusa da ita, yasa hannunshi ya dauketa, ya samu kujera, ya zauna, yace mata sannu ya jikin naki? tace da sauki, yace ai alhadulillah aikin yayi kyau, dan gashi kin samu sosai, sunana alhaji aliyu, dana kawoki nan, tace na gode, Allah yasaka da alkhairi, ya mike ya aje baby din, da kanshi ya hada mata tea, ya mika mata, ta amsa tace na gode, ya kara daukan baby din, yace yarinyar nan ta birgeni sosai, ta shiga raina, ina jinta sosai a raina, halima tayi murmushi, tace na gode. bata ankara ba, hawaye ya zubo mata, yace subhanallahi! baiwar Allah lafiya kuwa? tace bakomai, yace a'a akwai saboda hakanan zaki hau kuka? ta kara cewa bakomai, yace to shikenan, ba zan takura maki sai kin fada min ba, yauwa ina ne gidanku? saboda a fada masu su san halin da kike ciki, tace ina unguwan dosa ne, ta mishi kwatancen gidansu, yace to insha Allahu zan samu naje zuwa gobe, ko yanzu idan na fita, tace to na gode sosai, yace kada ki damu, bari in samu in tafi ana kiran isha'i, daga can zan wuce gida, se gobe na Kara zuwa, tace Allah ya kaimu, bayan fitan shi, ta kalli baby dinta, hawaye ya kara sauka a fuskanta, tace Allah ka raya min ita, ka tsare min ita daga duk wani sharrin halitta, [9/28, 9:41 PM] Ayshat madu: washegari sega alh aliyu ya shigo dakin shida babban yaronshi me suna kamaluddeen da halima take ciki a lokacin idonta biyu ta gaidashi kamal shima ya gaidata suka mata ya jiki alh aliyu ya dauki baby din yace babyna kina lafiya kamal yace daddy bani ita na ganta ya amsheta ya kara rungumeta yace wow daddy baby din nan tana da kyau ina sonta wallahi ta shiga raina mamanta ina kamu tayi murmushi tace zan baka daddy yayi dariya yace kamaluddeen kenan harda rantsuwa yace daddy ai da gaske nake ne daddy yace to ai gashi mamanta ta baka yace to daddy kaine sheda idan aka hanani ya kalleta yace ai bama zata hanaka ba zata cika alkawari ma halima ta kara murmushi daddy yace to jiya na samu naje gidan naku na fada masu halin da kike ciki na masu kwatancen inda kike tace to na gode daddy yayi murmushi yace bakomai wato kema kinyi ta Yara kenan yace kamal hada mata tea din ya mike ya hada mata tare da ferfesun kayan ciki ya mika mata ta amsa tace ba abinda zanci gaba da maka se godia na gode yace ki dena gode min saboda dan adam daraja ne dashi in yanzu na temakeki nan gaba na san temakon da zaki min ko wani nawa tace hakane yace to kada ki damu da duk wani abu dana maki ya mike yace to kamal tashi mu tafi ni zan wuce office ne tace to a dawo lafiya Allah ya temaka cikin jin dadi yace Amin kamal ya mike yana ta kara kallon babyn daddy yace tofa kamal mikata mu tafi mana yace ai daddy bana son rabuwa da ita ne halima tayi murmushi tace ai zanci gaba da kulan maka da ita ya mika mata yana ci gaba da kallonta suka mata sallama kamal yace ina nan dawowa tayi murmushi tace to seka dawo suka fita fitansu ba dadewa iyayenta suka shigo mahaifiyarta tazo kusa da ita ta rikota tace halima ya akayi wanda yazo ya fada mana kina asibiti yace 11 na dare ya ganki meya faru dake ina mijin naki halima tace ya sakeni hajia zainab wadda suke cema Amma tace ya sakeki akan me halima tace akan yana zargina da ina zina alh mansir wanda suke kiranshi da baffa yace zina kuma tace eh Batangas ahmad yace aiko kotu zata rabamu dashi dan baze yuwu aimaki sharrin zina ba Baffa yace a'a abin bezo da haka ba ka bari abi komi a hankali yaya ahmad yace akan me wai baffa ya za ayi a rinka takamu sede kace muyi hakuri yace hakurin shi zanci gaba da baku ka bari zan nemeshi inji komai A ranar baffa yaje ya samu mijin halima suka shiga palour suka gaisa yace bashir meke faruwa ne ka saki halima naga maganar bata waya bane nace bari nazo naji ko lafiya meya hadaku alh bashir yace eh to abinda ya hadani da ita shine ina zarginta da bin maza baffa yace subhanallahi zargi ma ashe kake baka kamata tana aikatawa ba yace ai tana ma aikatawa shiyasa naga zamana da ita beda amfani me za ayi da mazinaciya baffa yace kai bashir cikin daga murya ka iya bakinka naga alama giyar kudi na dibarka bana son raini ni inada kyakykyawan zata akan yarinyata nasan tarbiyan dana bata kabi duniya a hankali kuma diyarka na nan data haifa maka yace baffa wace diya kuma diyarta de dan bata cikin sahun tsarkakan yarana baffa cikin zafin rai ya daukeshi da mari yace me kake nufi da haka alh bashir ya dafe kuncinshi yace abinda kaji na fada shi nake nufi kaci
Chapter 1 · 0% Book details