← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 51

Sashe 50

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wani kalar likiti na turai da gargajiya an nuna qwarewa amma abu yaci tura gashi alamunta na sake 6aci ranar da akai uku aranar gabaki dayansu suka tattara suka nufi Georgia..shi,ammy da jakadiya data samu 'yancin rayuwarta itama sai sauran 'ya'yan da kowace takoma inda take aka bar sabon sultan dan gabatarda mulkinsa cikin aminci.

Suna sauka kai tsaye motar asibiti tazo daukarsu aka wuce asibiti dasu cikin tashin hankalinda yafi na farko sbd saki jikinta daya farayi.

Matsayinsa a babbar asibitin garin yasa ana isa da ita dukkanin likitocin dake nan suka taru aka fara qoqarin gano matsalar cikin gaggawa cikin tashin hankali da mamakin yanayin matsalarta sbd basu taba cin karo da irin hakanba.

Ammy daqyar ta iya zama gida saidai gabaki 'daya hankalinta da damuwarta na asibitin gabaki daya cikin kwana ukun ta rame tayi wani irin sanyi ko doguwar magana bata iyawa.

Har gari ya waye likitoci na kanta duk wata dabararsu da qwarewarsu sun nuna dan ganin ta farfado saidai Sam bata farfado ba saidai fatarta data fara komawa daidai sbd jinin da aka saka mata kusan leda biyu hakan yasa suke sakaran idan fatar ta gama komawa daidai ta farka.

Daqyar yake iya hadiye yawun bakinsa sbd tsananin bushewar bakinsa da maqoshinsa,

Duk wata nutsuwarsa da tunaninsa sungama barin jikinsa idanuwansa tuni suka qanqance ko gani bayayi sosai da idonsa dukkanin abokanan aikinsa sun tausayawa halinda yake ciki shiyasa suma gabaki daya hankalinsu tashe yake da ganin ta farfado 'din.

Khaleefa aranarda suka wuce aranar yasauka Ethiopia ya tararda abinda ke faruwa kasa kwana yayi duk da rashin lafiyarsa washe gari yabi jirgin asuba sbd yasan aminin nasa na tsananin buqatarsa.

Har yamma bata farkaba khaleefa ma saukarsa garin alhaji babaye yakirasa sbd news din dasuka gani gameda abinda yake faruwa a qasar nan yaqara yasanardasu abinda yake faruwa nan hankalinsu yayi matuqar tashi suka fara shirye shiryen tahowa cikin gaggawa.

Qarfe goma na dare ta bude idanuwanta dasukai wani irin shigewa sukai nauyi da ja.

Atake dukkanin likitoci suka sake hawa kanta cikin gaggawa da nuna qwarewa tareda fatar samun nasarar sanin matsalarta.

Kasa miqewa yayi sbd saki ga gabobin jikinsa sukayi sbd fargabar abinda za'a fada masa saidai khaleefa ne ya dafasa yana jinjina masa kai alamar qwarin gwiwa ganin halinda yake ciki.

Wasu sabbin dogayen hours suka 'diba suna qoqarin gano matsalar wadda suka gano daga qarshe wadda tayi mummunan 'daga hankalinsu haka suka ringa fitowa jiki amatuqar mace zuciyoyinsu ba dadi sbd dukkanin hotunansu da test test dinsu sun tabbatar musu da abu 'daya.

Dr Edward ne yafito qarshe yana zare glasses dinsa yakalli maheer da khaleefa yace,

Can we talk in my office pls..

Tashi tsaye maheer yayi tareda kallon qofar dakin da take yakalli Dr Edward din yana rintse idanuwansa da abinda za'a fada masa yace,

Just tell me dr Edward I c........

Dafasa Dr Edward yayi cikin tsananin tausayi ganin daqyar yake iya bude bakinsa yayi magana cikin sanyin murya yace,

I'm really sorry Dr m.a shams matarka ta rasa gangar jikinta bazata taba gara aikiba ma'ana tanada rai tana gani tana numfashi tanaji saidai bazata iya motsa jikintaba ko kadan bare magana har abada.

Wani mugun jirine ya dibesa khaleefa da Dr Edward sukai saurin nufarsa zasu taresa ta rigasu taresa cikin kulawa da tausayawa.

Khaleefa ne yakalleta cikin mamaki Dr Edward kuwa jinjina mata kai yayi alamar ta kula da maheer din yana buqatarta fiyeda koyaushe.

Shikuwa idanuwansa na ganinta baisan sanda ya sake fadawa jikinta yana qoqarin tsaida hawayensa saidai Sam basu tsaiduba saida suka zubo ya sake qanqameta yana cewa,

Suhailat please pray for me wlh zuciyata zafi takeyi I just can't live without her sbd wannan ma baida banbanci da mutuwa agareta.

Murmushin tausayinsa tasaki cikin sanyin murya tace,

Insha Allah zata warke
Nayi maka alqawarin zamowa majingini agareka duk lokacinda kake buqatata wannan alqawarin yananan haryanxu kuma nayi alqawarin cika makashi har qarshen rayuwata kuma zan tayaka jinyarta harta ji sauki sbd sonka shine qaddarata maheer abdulshams..

'Dagowa yayi kalleta da idanuwansa itama hawayen takeyi tana murmushi ahankali yaji wata irin soyayyarta mai tsafta tashiga zuciyarsa akaro na farko cikin wata irin rawar murya yace,

I love you suhailat sbd kece hasken rayuwata dakike tallafoni koyaushe.

Wasu hawayene suka gangaro mata ta rintse ido tana kwabar zuciyarta dake neman shegala da kamansa datasan ta samesune sbd nuna qaunarta ga rumanah saidai matuqar qaunarta ga rumanah zata jawo masa soyayyar mijinta to tabbas ta shirya samun soyayyar mijinta ta hakan.

Duk yanda ya 'daga hankalin likitocin asibitin akan abinda sukace dole ya dangana yadauki qaddara sbd result din dayane.

Ko ammy saidata kwana ta yini tana kukan halinda rumanar ke ciki da Wanda yashiga sbd gabaki daya ya birkice musu ko abinci sai ammyn tayi kuka yake iya shan abu mai ruwa ga suhailat data zamo batada wata hidima saita kula da dukkaninsu sbd sundawo gida.

Idan yazo ya zauna kusada ita haka zai riqe hannunta cikin nasa ya qura mata ido
Itadai hawayene kawai ke iya gangarowa ta gefen idonta musamman idan ammy tasata gaba tana kuka kokuma shi idan yazo ya zauna yasaka gaba ya qura mata ido tana iya hango mawuyacin halinda yake ciki.

Ranarda su hajiya yakurah suka iso aranar kuka yadawo sabo ganin halinda 'yarsu dasuke 'dokin gani take ciki...

Ko alhaji babaye dake dattijo saida ya zubarda hawayen baqin ciki da farin ciki.

Akwance take itama amma hawayene keta bin gefen fuskarta suna zuba Wanda hakan yaqara bawa kowa tausayi.

Duk da akwai Carolina sosai suhailat ke wahala sbd lalurar rumanah din.

Kusan satinsu alhaji babaye biyu kafin shi ya koma yabar haj yakurah dataqi dawowa tana jiran isowar mijinta dazasu tafi tareda rumanah sbd gwada nasu na addinin.

Satin alhaji babaye daya da tafiya alhaji mukhtar mijin haj yakurah ya iso kallo 'daya yayi mata yagano lalurarta Allah takeson akomawa sbd lalurace ta iska nan take suka yanke shawarar tafiya da ita maheer kai tsaye ya nuna rashin amincewarsa
Saidai ammy dataga yana mutuwar tsaye kullum sbd lalacewa da rayuwarsa ke nemanyi dan ko aiki bai taba fitaba koyaushe yana gida ga suhailat data zamto abar tausayi gurin qoqarin kulawa dashi da rumanah duk ta rame tausayinta da qaunarta yasa kai tsaye ta zaunar dashi cikin nutsuwa ta fahimtar dashi kuskuren dayake jefa rayuwarsa da iyalinsa ciki dan haka yabar rumanah aje da ita ya tsaya ya gyara mu'amalarsa da rayuwar aurensa da suhailat.

Sosai jikinsa yayi sanyi kuma yasan matuqar yanason gyara rayuwar iyalansa ta inganta saiya boye soyayyar rumanah kwata kwata dan haka zai danne Zuciyarsa yafara daga yanzu.

Da haka ya amince aka tafida rumanah din amma hardashi suka tafi saidaya kwana biyu yadawo dan qoqarta gyara mu'amalarsa da suhailat.

Koda yadawo su ammy da jakadiya tareda abeel sun komawarsu Libya dan haka gidan dagashi sai suhailat sbd su amah ma suna Mali tabarosu dama itakadai tazo.

Aranar daya dawo lafiyayyan tarba tayi masa cikeda Dari darin yanda zai dawo yayi rayuwa a inda babu rumanah.

Ganin yanda take kama kanta dashi duk sai yaji ya muzanta ya tattaro jarumtarsa ya danne abinda ke ransa ya riqo hannunta ahankali tareda jawota jikinsa yana kallon fuskarta dake kallonsa yasaki qayataccen murmushi yajata suka zauna bakin gadon dakinta daya shigo yasameta hartayi shirin bacci zata kwanta.

Kallonsa takeyi tanason gano damuwarsa saidai takasa ganin komai sai murmushin dayake sakar mata
Wani irin sanyi da farin ciki taji na shigarta ahankali kenan kalamansa daga zuciyarsa suka fito lokacinda yafada matasu.

Rungumesa tayi da sauri tana sakin hawayen farin ciki ta murmushin jin dadi.

Dagota yayi tareda zare mata riga yana murmushi yace,

Banyi wankaba so yau kece zakiyi wannan aiki.

Noqewa taso yi tana murmushi yayi saurin riqeta yana kallon cikin idonta ya girgiza mata kai ahankali yace,

Don't make that mistake again suhailat.

Kallonsa tayi tareda jinjina kai takama hannunsa ta nufi hanyar toilet dinta dashi suka shige.

Aranar wata irin rayuwa suka gudanar data mantarda suhailat dukkanin damuwarta ta dah inda sukai alqawarin dora sabuwar rayuwar aure ta fahimta,soyayya qauna da aminci atsakanin su uku da 'yayansu daga yanxu.

**
Ahankali ake gudanar da adduoi da sauran abubuwan addini tareda sauke al-qur'ani da sadaka ana fatar samun sauqi.

Kulawa sosai da wata irin qauna da soyayya suke mata kaf zuriar banda zuriar gidansu aqeel data gama tarwatsewa babu wani nakamawa acikin zuriar gidansu shiyasa koda sukaji 'yarsu bulama tadawo kuma a nakashe kota kan zancen basubiba.

Su kuwa haj yakurah tamkar 'yar data haifa da cikin ta takejin rumanah duk wata kulawarta da dukkanin hidimarta takoma ta rumanah shima alhaji babaye kullum saiyazo gidan sbd yayi yayi tabari rumanah takoma gidansa taqi yarda tabari.

Watanta hudu a Nigeria yazo dubata babu adadi duk tareda suhailat suke zuwa Wanda itama tanajin farin cikin ganinsa da suhailat sbd ganin hankalinsa ya 'dan kwanta sosai duk sukazo idan zasu tafi daurewa kawai yakeyi yakoma sbd alqawarin adalci daya daukarwa kansa.

Ammy kuwa kusan tamafi maheer din zuwa kuma takan dade idan tazo.

Ahankali tafara samun sauqi sbd wasu gurare dasuka fara motsawa ajikinta Wanda hakan ba qaramin farin ciki da qwarin gwiwa yasakasuba nan aka sake maida himma ga sauke al-qur'anai da sadaka da adduoi.

Ba'a rufa wata biyu da fara motsinta ba tafara magana ahankali har tana iya tashi zaune da kanta ta tashi.

Lokacinda wannan saqon ya iso masa aranar suhailat harda hawayen farin cikin ganinsa cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa tayi sbd Sam kasa boye farin cikinsa yayi.

Kafin sati biyu dukkanin kuzarinta sun dawo lafiya kalau saidai bata iya komai da sauri ko qarfi Wanda hakan shima ahankali zai dawo.

Washe garin ranarda umma yakurah da ammy suka fada masa samun lafiyarta yatafi wannan karon suhailat qin biyosa tayi sbd ganinta kusa zai hanasu nuna kewar junansu.

Sai dare sosai ya isa Wanda tareda khaleefa dazaije gurin nuratu sukayo tafiyar dole suka sauka masaukinsu kai tsaye sai washe gari suka nufi gidan guraren qarfe goma shima sbd khaleefa daya hanasu tafiya tunda safe.

A babban palo suka tararda su umma da ammy harmada Jakadiya da sabuwar mai rainon abeel suna ganinsa umma tayi murmushi sbd tanajin dadi da farin cikin yanda yake tsananin qaunar rumanah dinsu.
Chapter 50 · 0% Book details