← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 51

Sashe 30

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari qarfe goma na safe masarautar tacika da baqin mineelik Ethiopia sbd daukar matan yarima maheer uwayen magajin mineelik tareda sultana zaarah da aka mayar mata da matsayinta lokacinda labarin cikin rumanah ya isa ga sultan.

Harda jakadiya da itace zata karbi ragamar kulada cikin rumanah tun daganan Libya harzuwa haihuwarta.

Lokacinda aka fito da rumanah cikin wani irin shiri na adon doguwar royal gown cikinta yafito sosai tana tafe kusan bayi da guards goma zuwa sama Suna bayanta.

Kallonta ammy tayi jikinta na sanyi
Jakadiya ma cikin ta qarawa ido numfashinta na fita da sauri tasaki ajiyar zuciya.

Gogan kuwa tunda yaga abubuwa sunfara canxa masa daga yanxu ya rintse ido tareda budesu yayiwa Jakadiya kallo 'daya tagano manufarsa ta qarasa ta tarbi rumanah din ta suka nufi motar da zaishiga aka bude mata tashige nan kowa yashiga motocin suka nufi airport.

Tunda suka shigo motar hannunsu suke sarqe dana juna saidai babu mai iya magana acikinsu dan kowanne da halinda zuciyarsa take ciki.

Ko acikin jirgi tafiyar babu Wanda yake iya magana acikinsu sbd kowa da abinda yake kai kawo acikin zuciyarsa.

Suhailat dama tuntuni tasan ita farin ciki yaqare arayuwarta daga ranar da mijinta yafara son rumanah musamman yanxu datakejin duniyar dakomai ya fice mata arai gashi ciwon dakecinta yafara fin qarfinta musamman yanxu datake yawan ciwon mara mai tsanani.

Qarfe hudun asuba jirginsu ya sauka a Ethiopia.
Matse hannunta dake cikin nasa yayi ta juyo takallesa da idonta dasukai ja sbd tsananin damuwar dake ziciyarta.

Ahankali ta zare hannunta ta miqe ta wuce gaba su Jakadiya da sauran suka mara mata baya tana qoqarin maida hawayen dake qoqarin zubo mata.

Bayanta yabi da kallo idanuwansa na canxawa
Hannunsa suhailat ta riqo idanuwanta cikeda hawaye cikin rawar murya da kulawa tace,

Zan zamo bangon jinginarka aduk lokacinda kake buqatar hakan.

Rintse ido yayi idanuwansa naqara canxawa suka fito jirgin.

Motar rumanah daban ita kadai da masu tsaronta kuma itace agaba sai sauran nasu lokacin gari baigama haskeba.

Ruwa yaji ankelaya masa yayi saurin bude ido yatashi a matuqar zafafe saiyaga jini kaca kaca a jikinsa da sauri yatashi tsaye aka mayar dashi zaune da qarfi tareda dora masa wata doguwar takobi mai tsananin kyallin sbd kaifinta tsoro bai kamasa sbd dama yasan hakan zata iya faruwa ko yau ko gobe....

Cikin wata irin murya data amsa amo har cikin qwaqwalwarsa yaji ance"""asauke kansa Daga gangar jikinsa a qawata qofar shigowa masarautata dashi kowa ya 'dan'dana kalar mulkin assultana the redblood Queen.

Daga takobin akayi da qarfi za'a sare kansa yayi wani irin yunquri yana hada mugun zufan daya jiqa dukkanin jikinsa yakalli adama dake gefensa itama ta farko tana hada nata zufan da alama itama wani mugun mafarki tayi kamar shi sbd harma tafisa rudewa sbd rawar da jikinta keyi.
Saukowa yayi kan lafiyayyan qaton gadonsa yanajin wani irin tashin hankali na shigarsa busar data cika masarautar tashigo kunnensa kenan su maheer sun iso.
#mamuhgee

_*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_

*31*
Not edited.
Kallon adama dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta ke rawa saidai Sam bata tata yakeyiba mafarkinsa ya girgiza tunaninsa da zuciyarsa matuqa sbd su mutane ne dasuka yarda da mafarki,
Basason 'yaya mata sbd muguwar aqidar dasuke ciki ta wani irin mulki da ake gudanarwa na tsantsar iko kowa yasan mulkin mace a mineelik masifa ce dabaza'aso maimaitawaba sbd jinin matansu bazai iya controlling na abinda yake tareda throne dinba kamar namiji shiyasa mulkinsu yake zama tamkar masifa ko annoba sbd mulkine na tsantsar zubarda jini Wanda babu yaro ba babba bare mata bare maza,ba tsoho ba tsohuwa.

Alqawarine yadauka bazai taba bari mace ta mulki mineelik ba koda zai rasa ransane sbd yasan duk macen dazata hau zaiyi wuya basuyi ajalin junaba dayaga haka ya roqi Allah yayi gaggawar daukar ransa.

Cikeda rudu adama takallesa tana goge fuskarta dahar lokacin take gumi tace,

Sultan nayi mugun mafarkinda gwara nayi mutuwar qasqanci a hannun 6arayi dana fuskanci irin abinda Nagani a mafarkin.

Bai kalletaba bare yatsaya sauraran abinda take fada sbd tunanin daya cika zuciyarsa akaro na farko arayuwarsa dayaji mulki yafara fita ransa sbd duba da irin mutuwar da sarakunan mineelik keyi yayi tunanin zai iya tsallakewa ya sauka mulkin salin alin batareda fuskantar irin qarshen sauran sarakunan ba shiyasa ya tattara duk dagewarsa akan ganin maheer ya karbi mulkin amma yaqi gashi matarsama ta haifi namiji arabasa da wannan masifar abu yaqi yiyuwa ta wani 6angare ga daular shiefffs na jiran rashin magajinsu su zamo bayi a qarqashinsu Wanda yafison ya sare kansa daga gangar jikinsa dayaga wannan baqar ranar yanzu kuma ga wata masifar nason 6ullowa sbd baisan me mafarkinsa na assultana yake nufi ba.

Hannunsa ya daga ahankali ya shafo fuskarsa cikin mamaki saiyaga zufa ne ke tsatsafo masa,
Rabon da yayi zufa a rayuwarsa harya manta.

Irin tarbarda akayiwa isowarsu ta qara sanyaya jikin rumanah sbd tafara fargabar itama me zata Haifa sbd ganin irin dubban jama'ar dasuka dogara da abinda zata haifa.

Lokacinda mamani tayi ido biyu da rumanah da cikin dake jikinta wani mugun jiri mai qarfi ya 'dibeta nuratu tayi saurin tareta tana kallon idanuwanta dake cikowa da qwallar baqin ciki tace,

Mamani lafiya?

Kasa riqe hawayenta tayi sbd baqin cikin daya rufe zuciyarta tace,

Har abada bazanyi lafiyar zuciya ba sbd bulama da asma'u har bayan barinsu duniya basu bar kurwata ta zauna lafiya ba bayan duk balain dasuka sako rayuwata aciki dan haka wlh bazan zauna nashaqi numfashi mai dadiba sai ranar dana gama lalata dukkanin zuriar da suka bari aduniya....

Sakinta nuratu tayi cikeda mamaki da baqin cikin halin mahaifiyar tata muryarta na rawa tace,

Mamani dazaki cire abinda yake ranki gameda rumanah dakin cire sbd zai kaikine matakin halaka sbd yanxu tariga ta taka wani matsayinda duk Wanda yayi mata wani ganganci zai iya rasa rayuwarsa sbd dukkanin burin daular nan da zagayenta akanta da cikinta yake dan haka ki nesanta kanki da ita sbd gujewa rasa rayuwarki..ke mahaifiyatace ina sonki fiyeda komai amma bazan iya kallo ki cuci rumanah ba dan haka karkiyi abinda zai barni da rashin zabi face na fadi gaskiyar dazaki rasa rayuwarki.

Tana gama fadar haka tabar gurin cikeda damuwa
Duk murnarta da farin cikin ganin rumanah din ya 6aci sbd mamani.

Kukan 6aqin ciki mamani tasake tana tsinewa bulama da asma'u ta juya ta nufi gurin adama da sai alokacin zata fito tarbon.

Kallo daya tayiwa cikin rumanah taji tari mai qarfi ya sarqeta kamar ranta zai fita
take ta gigice da gudu akaje aka kawo mata ruwa ta karba tasha idanuwanta dasuka firfito sukai jajir sbd tari numfashinta na fita da sauri ta juya tabar gurin nanma idonta ya sauka kan na suhailat dake tsaye gefen Maheer ai take taji qaramar hauka na neman kama zuciyarta tana isa palonta na farko dukkanin bayi da kuyangin part din suka fice sbd gudun laifi lurada halinda take ciki.

Mamani data sake biyota da ruwa ta miqa mata har lokacin itama jitake kamar ta cinnawa mineelik wuta kowa ya babbake ya mutu ko zataji abinda ya tsaya mata a maqoshi ya fada.

Karbar ruwan tayi tasake sha tana cewa,

Burina dana gina tun ina budurwa bazai taba rushewaba kan baiwa 'yar bayi,
Babu Wanda bazan iya raba gangar jikinsa da kansaba kan burina sbd burina shine burin karagar mineelik..

Cikin tsananin damuwa da baqin cikin mamani daya kasa dannuwa aranta tace,

Duk inda bulama da asma'u suka sauka saisun bar masifar data addabi kowa awajen
Shiyasa bazan numfasaba saina tabbarda na tarwatsa rayuwar rumanah da abinda ke cikinta.

Kallonta adama tayi da jajayen idanuwanta baqin cikinta na ninkuwa tace,

Ko bulama ne aduniya bai isa ya shiga tsakanina da hawa throne din mineelik ba bare 'yarsa dan haka ni adama ayau ina sake daukarwa kaina alqawarin kawarda ko wanene ya shiga hanyata ta cimma burina
Idan nace ko wanene ina nufin ko wanene ciki bancire kowaba.

Cikin takaici mamani tace,

Allah yasa gurin haihuwa ta mutu daga ita har abinda zata haifa kowama ya huta.

Kobata mutu gurin haihuwa ba ta haifi namiji saiya mutu kozan rasa rayuwatane"""adama ta fada  tana miqewa tsaye.

Tsayawa tayi tareda juyowa takalli mamani itama mamani ita takalla sai alokacin kowannensu yadawo nutsuwarsa jiki na rawa mamani ta zube tana sunkuyar dakai

Adama fuskewa tayi sbd duk duniya daga ita sai bokanta ne suka San da sirrinta sai yanzu da 6acin rai yasata fadar abinda ke ranta saidai kuma ga alama tasamu wadda zata riqa amfani da ita Dan cimma burinta musamman da kusancinsu da rumanar zasuyi amfani tunda tana yiwa mamani kallon uwa.

Wani irin babban sabon sashe da aka zubawa tsaro na musamman aka kaita Wanda yake gefen part din yarima maheer duk wani abin jin dadi da hutawa anxuba mata shi ga kuyangi na musamman da aka kawo mata.

Bayan duk wata aladar tarbonsu anyi angama da daddare bayan tayi wanka ta saka kayan bacci ta kwanta bakin gado tareda lumshe idanuwanta ta bude ahankali tareda kiran sunansa cikin zuciyarta.

Suhailat kuwa sbd yanayin jikinta da gajiya yasa tana kwantawa bacci ya dauketa cikin tsananin gajiya.

Abincin da aka aikawa kowaccensu daga part din sultana zaarah babu wadda tasamu damar ci har gwara suhailat tasha madara mai zafi sbd sanyi datakeji kamar zai kamata.

Rumanah kuwa kwance take tayi lamo cikin zurfi a tunani da tsananin son ganinsa sbd har lokacin takasa daina tuno yanayin dasuka rabu 'dazun hakan na raunana zuciyarta da kuzarinta ahaka bacci yadan 'dauketa tanayi tana farkowa hardai akai asuba tayi sallah takoma ta kwanta nanne tasamu baccin yadauketa sosai.

Qarfe goma ta fito palonta anan ta tararda dining shaqe da kalolin abinci ta kalli qofa kamar tana jiran isowar wani hardai tagaji ta nufi dining tana fidda wani irin qamshi mai dadi.

Fara cin abincinta kenan taji muryar data sakata dakatawa ta juyo da sauri suka hada ido da nuratu dake cikin tsananin farin cikin ganin rumanah din.

Miqewa rumanah tayi zata nufeta Jakadiya data kawo mata nuratu din tayi gyaran murya dole ta tsaya tana kallon nuratu cikeda farin ciki
Nuratu 'dince taqaraso gaban rumanah tana kallon cikinta tana sake bayyanarda farin cikinta zata zube qasa rumanah ta riqota tareda Rungumeta duk da tsinin cikinta baibari sun rungume juna sosaiba.
Chapter 30 · 0% Book details