← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 51

Sashe 46

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon juna sukayi dakyau
Ganin yana qureta da kallo yasata sauke kanta ahankali tareda kwantarda abeel ta 'dago ta qura masa ido ganin yanda duk ya rame lokaci 'daya yayi wani irin canzawa saidai kuma abin tausayin shine yana cikin wannan halin ne sbd halinda rumanah take ciki.

Gangarowa hawayenta sukayi ta sauke kai ahankali cikin sanyin murya da nutsuwa tace,

Ranar farko dana fara ganinka aranar nafara Sonka maheer ibn abdulshams abdallah,,
Kaine namiji 'daya da zuciyata ke so saidai babban kuskuren danayi shine na nacewa na aureka a tunanina zaka soni wata rana saidai ashe babban kuskure da shishigi nayiwa qaddarar datake jirana..

Kallon cikin idanuwansa dasukai jajir tayi tasaki murmushi mai ciwo tace,

Haryanxu ina sonka maheer abdulshams saidai bazan iya cigaba da zama dakaiba maheer sbd girman soyayyar danake maka bazanso zuciyata ta tsanekaba.

Ayau ina roqonka sbd darajar 'Yayana da soyayyata ka sauwaqemin na samu rayuwar data cancanta dani wannan rayuwar ta gidanka ba tawa bace na tabbatarda tawa tana wani guri tana jirana.

Rintse ido yayi akaro na farko dayaji ruwa sun ciko idanuwansa sbd ita ya girgiza kai yanason magana amma yakasa.

Ta riqo hannunsa tana qoqarin maida hawayenta tace,

Wlh idan nacigaba da zama dukkaninmu zamu cutu qarshe dukkaninmu zamu fada hanyoyinda bazasu amfanemu ba sbd zan iya canzawa na zama wata daban,
Canzawata zatasa ka tsaneni
Tsanata dazakayi zaisa matarka ta canza sbd zata riqa ganin itace abar so nikuma zata riqamin kallon mahaukaciya qarshe dukkaninmu zamu zama abinda bama fatar kasancewa...

Na yarda da aurenka shine qaddarata kuma na karbeta da hannu bibbiyu kuma ina fatar Allah yasa na cinye wannan jarabawar zuwa yanxu sbd zuciyata tafara gazawa dan haka nake roqon alfarma ta qarshe daga gareka dan Allah free me from this relationship
Wlh I'm in so much pain zuciyata zata iya bugawa kowane lokaci please free me maheer.

Girgiza kai yayi yana kallonta da idanuwansa dasuka canza daqyar ya iya furta,

Suhailat I need you in my life please don't.....

Girgiza kai itama tayi kukanta na qoqarin qwacewa tace,

Wlh bazan iyaba maheer,
Wlh mutuwa zanyi I've endured enough,
Duk abinda kamin na yafe maka ina fatar kaima ka yafemin
goodbye yarima maheer abdulshams.

'Daukar abeel tayi ta rungume wani irin ciwo mai zafi nacin zuciyarta ta rintse ido hawaye masu zafi suka gangaro mata tasaka hannu ta goge fice dakin.

Kodata fita palo Carolina da sauran masu hidamarta duk suna tsaye kowanne idanuwansa cikeda hawayen rabuwa da ita.

Kallonsu tayi tareda sakin murmushin qarfin hali ta fice sbd bazata iya cewa komaiba ta nufi sashen rumanah.

Zaune take a palonta tayi lamo ko motsi batayi ta qurawa gefe 'daya idanuwanta dasukai jajir suka bushe dukkanin wani abincin karyawa an Jere mata a gabanta saidai ko motsi batayiba bare takalli abincin gashi har rana tafarayi,
Ganin halinda take ciki yasa dukkanin masu hidimarta da masu tsaronta yau jikinsu asanyaye yake ko babban motsi ba'ayi a sashen tsit kakeji.

Da shaqaqqiyar muryarta datasha kuka tai sallama tashigo palon taganta zaune da alama agurin ta kwana tun jiyan sabd ganin kayan jikinta.

Ahankali taqaraso gabanta ta durqusa ahankali ta dora mata abeel ajikinta.

'Dago idanuwanta tayi a wahalce ta kalleta takalli abeel ta tashi zaune daidai tareda qurawa abeel 'din ido ta 'dago takalli suhailat ahankali ta iya bude baki sbd tsananin nauyi da ciwon kan datakeji tace,

Shine da kansa yace yabaki bayan nima nace nabar miki sh......

Nagode sbd kema kinyi abinda bakowace uwace zata iyaba ciki hardani kuwa sbd bazan ta6a iya bawa kowa 'dana dana haifaba,

Ina qaunar abeel qauna mai tsafta sbd shi 'din 'dan maheer ne kuma ina kallonsa amatsayin jemal dina dana rasa saidai zamansa hannuna bamai yiyuwa bane Allah ya albarkaci rayuwarsa.

Juyawa tayi ta nufi qofa ta fita batareda tasake cewa komaiba sbd batason bayyanarda hawayenta gaban rumanah tabarta da jin cewar kamar itace silar rabuwarsu.
#mamuhgee

_*TARAYYA*_
_wattpad@muhgee_
_Haske writers association_💡

*42*
_Not edited_

Kasa motsi tayi tabi bayanta da kallo harta fice ta jima tana kallon qofar kafin ta maido kallonta kan abeel daya farka yana kallon fuskarta ta rintse ido tareda rungumesa tana jin wata sabuwar damuwar sbd rashin sanin abinda yafaru yanxun.

Ahankali ta lumshe idanuwanta mafarkin abbanta datai yau yana dawo mata.

"Ummu-rumanah kibi mijinki a dukkanin umarninsa matuqar basu saba addininki ba sbd shine gatanki kadai yanxu aduniya,
Ki gujewa mulki sbd haqqoqin dubban mutane da bazaki iya daukaba sbd rauninki na zamowa 'ya mace kibarwa Allah komai ki gyara aljannarki."""

Kalaman da mahaifinta ya sanarda ita a mafarki kenan saidai abinda takasa ganewa shine ta yaya zata sauka mulkin batareda ta kawo sauyi da zaman lafiya a qasar ba.

Bude ido tayi tareda jinjina shawararda zuciyarta ke bata dan kawo qarshen komai saidai hakan wani abune mai girma dayakeda matuqar hadari saidai dole zata aikata hakan koda hakan shine ajalinta zatayi dan kawo qarshen rayuwar da alummar qasar suka samu kansu.

Tabbas qaddararta itace ta koro iyayenta daga gida ta kawosu nan sbd gashi abinda yafaru tun qarnikanda ko kakanninta ba'a haifa Ashe tana cikin qaddarar gashi itace zata kawo qarshen abin.

Hawayen tausayin mijinta da 'danta tareda ammy ne suka gangaro mata ta sauke kanta tareda sakin kuka ahankali sbd tasan sune zasufi kowa kukan rashinta arayuwa sbd sune wainda takeda matuqar mahimmanci arayuwarsa ta yanda rashinta zai matuqar ta6a rayuwarsu.

Sunansa ta furta ahankali cikin zuciyarta sbd tasan mutuwarta zata tarwatsa zuciyarsa zatabarsa cikin mawuyacin hali saidai tasan suhailat na nan zata kula dashi.

Miqewa tayi ta nufi dakinta ta kwantarda abeel ta zauna gabansa ta qura masa ido tana fidda sautin kuka ahankali sbd kukane takeyi sosai.

Tana fitowa sashen rumanah kai tsaye shashen ammy ta nufa bata nuna mata komaiba tasanarda ita zataje Mali.

Ammy dake fama da ciwon kai mai tsanani takalleta da idanuwanta ahankali tace,

Allah ya kiyayeki ya hadaki da alkairin dake cikin tafiyar.

Amin ta furta ahankali tareda juyawa ta fice dan dama su amah suna Mali tuntuni da aka fara wainan rudanin.

Motocin dazasu kaita airport na fitowa daga masarautar tasaki wani irin kuka ahankali tareda rintse idanuwanta tana furta Allah yabani juriya da danganar rabuwa dakai maheer.

Suna isa airport basuyi minti ashirin ba suka tashi daga qasar Ethiopia zuwa mali.

Lokacinda ta wuce tabarsa daqyar ya iya fita yabar dakin ya nufi part dinsa yana qoqarin danne halinda zuciyarsa ke ciki amma yakasa saida jiri ya zaunar dashi kan kujera da qarfi ya rintse ido ga mamakinsa saiyaji kamar hawaye na neman zubo masa yayi saurin dafe kansa da hannu bibbiyu jin kamar zai rabe masa sbd yasan bazai ta6a iya cireta aransa ba.

Ahankali ta qaraso bayansa ta tsaya tareda zuba masa ido tana sake danne hawayenta..

Bude idanuwa yayi ahankali sbd he can feel her presence.

Juyowa yayi suka hada ido atake takasa riqe kukanta tafara girgiza kai tareda sakin kukan
Ya ware hannunsa 'daya alamar tahowa garesa da gudu ta qarasa ta fada jikinsa ya rungumeta sbd shikansa yana buqatarta kusa ayanxu.

Kukan datakene yafara bashi mamaki ya 'dago fuskarta ya kalleta atake yaji kwanyarsa ta qarasa hargitsewa ya bude baki zaiyi magana tayi saurin 'dora bakinta cikin nasa tana tsiyar hawaye.

Ahankali tasaki bakinsa tana kallon fuskarsa dake bayyane da damuwa cikin tsananin sanyin muryar kuka tace,

Ina sonka yarima maheer abdulshams,

Kaine farin ciki da rayuwar ummu-rumanah bulama,
Kaine abinda zuciyata bazata iya jure rashinsa ba,
Ina maka qauna mai girma a tun ranardana fara ganinka agabana.,
Wlh bazan taba iya aikata kuskurenda zai nesantani dakaiba bare kwatanta rayuwa babukai..

Kasan mutuwane kawai banyiba a daren ranar daka furta rabuwa dani maheer abdulshams,

Ummu-rumanah bazata iya rayuwa babu kaiba sbd kaine jigonta kuma jagorarta..

Share hawayenta tayi tareda jan numfashi kukanta na rage sauti tace,

Wlh haryanxu zuciyata zafi da takeyi da zancen daka fadamin kana tunanin zan iya rayuwane wlh mutu.....

Maidata yayi jikinsa da sauri ya rungumeta yana girgiza mata kai dan bazai iya ko maganaba.

Qanqamesa tayi tana cewa,

Na tuba ka yafemin.

Dora hannu yayi abakinta yana sake rungumeta ahankali ya furta,

Maheer abdulshams loves you ummu-rumanah bulama.,
Ummu-rumanah bulama kece mahadin rayuwar maheer abdulshams.

Murmushin qarfin hali tasaki ahankali tareda sake kwanciya ajikinsa.

Shiru sukayi dukkaninsu ajiyar zuciyarta kawai ke fita akai akai
Sai kuma shi dahar lokacin tunani da damuwar tafiyar suhailat ne kawai cikin ransa,
Tana buqatar shan iska zai barta tasamu sarari idan yagama da matsalar mineelik ya tabbatarda rumanah ta fita daga cikin wannan masifar zaije yadauketa su koma Georgia gabaki 'dayansu.

A daren ranar nan ta kwana gurinsa tareda abeel saidai kusan dukkaninsu babu mai nutsuwar yin bacci saidai shiru sukayi a kwance kowannen da abinda yake damun zuciyarsa.

Washe gari koda aka tashi aka tararda Allah yayiwa mamani rasuwa
Koda aka dudduba dan tabbatarda meya kasheta aka gano saran maciji ne har guri biyu a wuyanta da gefen hannunta sbd wani irin canzawa da fatarta tayi takoma Kore Kore alamar qarfin dafin macijin mai ha'darine.

Lokacinda Jakadiya ta kawo mata saqon mutuwar suna zaune kan dining maheer na tilasta mata cin abinci.

Kallon Nuratu dake jera musu sauran abincin breakfast din tayi da sauri tareda miqewa tsaye sbd ganin halinda tashiga lokacinda Jakadiya tagama fadar saqon da sauri suka rungume juna nuratu na sakin wani irin kuka ahankali tareda rintse ido tana girgiza kai.

Hawayen tausayin nuratun ne itama suka ciko idanuwanta ta bubbuga bayanta cikin son daure kukanta dake zuwa na tausayin kansu sbd sun tabbata marayu iyayensu dasukazo nan suka haifesu sun rasu sun barsu ayanxu sune kadai 'yan uwan kansu.

Cikeda tausayawa Jakadiya takallesu cikin sanyin murya tace,

Allah ya gafarta mata laifukanta ya sadata da rahamarsa ina miqo ta'aziya ga assultana da 'yar uwarta nuratu akan wannan rashi.

Ganin tana neman rikicewa da kuka yasashi yiwa Jakadiya wani kallo
Atake tayi gyaran murya tana cewa,

Nuratu kizo muje kiyiwa mahaifiyarki addua kafin a fice da ita.

Sakinta rumanah tayi tareda kallon fuskarta tana hawaye tace,

Allah yabaki haqurin rashinta yasakamiki dauriyar yimata addua.

Kallon rumanar tayi sbd jin bata ambatarwa mamanin rahamar ubangiji ba ahankali ta bude baki cikin tsananin sanyin murya tace,

Ina roqorwa mahaifiyata yafiya ki yafe mata sbd qauna da amincin dake tsakanina dake dan......
Chapter 46 · 0% Book details