← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 51

Sashe 49

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon khaleefa yayi da sauri tareda zagayowa daga table dinsa jikinsa na wata irin rawa tun kafin yayi magana khaleefa yaciro alamar masarautar daya fito ya miqa masa cikin turanci yace,

Nazone dan neman asalin sarauniyar qasata ummu-rumanah bulama..

Rawa jikin alhaji babaye yaqara yace,

Ina kasamo wainnan takardun?
Ina masu su suke?

Masu wainnan takardun sun rasu saidai 'yarsu wadda itace sarauniyar qasarmu ayanxu....

Wani irin kuka alhaji babaye yasaki tareda rungume khaleefa duk da dai yasan dole yayi bincike akan hakan kafin yagama yarda.

Waya yaciro yakira qanwarsu  hajiya yakurah yafada mata nan hankali ya tashi sbd farin ciki da murna tareda wasi wasin zamtowar zancen gskia.

Da kansa yakaisu gidansa akai musu masauki kafin yatabbarda zancen duk da yasan baza'a yimusu qarya dan a cucesu tun daga qasar Ethiopia ba kuma daga masarautarsu.

Washe gari cikin manyan motoci suka dunguma zuwa garinsu kutti dan sake tabbatarwa.

Sai tsakiyar dare suka isa kuma acikin daren aka tara duk dattijan garin dasukasan su bulama da asma'u tun zuwansu garin da duk abinda yafaru.

Kuka sosai alhaji babaye yayi dayaji irin rayuwar da 'dan uwansa da matarsa sukayi saidai kuma yanzu babu abinda yakeson gani kamar 'yar dan uwansa.

Daga alhaji babaye sai khaleefa suka koma sbd khaleefa jirgi zaibi yakoma bazai iya tafiyar ruwaba kuma sauran binciken da tabbatarwar idan sun haduda rumanah zasu qarasa tabbatarwa.

Koda suka koma gida sosai hajiya yakurah taso bin khaleefa suje tare saidai maigidanta yace tabari yadawo daga China saisuje gabaki dayansu da haka khaleefa yatafi sbd ciwo dake neman kwantar dashi sbd bai qaramar wahalaba yasha a tafiyar.

A yau saqon haroun ya iso gareta an kammala aikinta.
Shiru tayi bayan fitar Jakadiya sbd tunanin yaya maheer zai karbi zancen sbd dole tana buqatar aiwatarda abinda tayi niya dan tanaji jikinta yasaki sosai jininta qarewa yakeyi sbd tsananta da abin yafarayi ajikinta sbd jinin dataqi zubarwa har lokacin tasan daf take da rasa hankalinta dan wata irin zabura dake kamata yanzu duk da tana qoqarin boyewa ammy da maheer tanaji abin yafara cin qarfinta.

Kallon abeel dake kwance jikinta tayi zatai magana jini ya digo ta hancinta ya sauka kan fuskarsa tayi saurin goge masa tareda ajiyesa ta dauki tissue tana dafe kanta da jiri ke juyawa dashi.

Durqusa gurin tayi tana fidda wani irin nishi cikin azaba tsawon mintuna kafin tasamu taci qarfin abin tana kiran sunayen Allah harya lafa kafin tayi wani yunqurin miqewa ya turo qofar dakin yashigo cikin nutsuwa idanuwansa kanta yana kallon tissues din gabanta dasuke lalace da jini hakama hancinta zuwa bakinta duk jini.

Saurin goge hancinta tahau yi saidai kuma atake jinin yasake 6allewa ta rintse ido cikin wani irin hali tafara nishi mai wuyar fita.

Da wani irin gudu ya qaraso gareta tun kafi yakai hannunsa gareta idanuwanta suka fara qoqarin rufewa yayi saurin tarota jikinsa yana kiran sunanta da qarfi.

Ganin tana neman fita hayyacinta yasa ya bude bedside drawer dinta yadauko maganin da negasi yabayar ariqa bata idan jinin yazo mata ya bude gabaki daya ya zuba mata abaki cikin tashin hankalin saidai jinin bai tsayaba amma idanuwanta sun bude tafara qoqarin tashi tana karbar tissue din dayake qoqarin kaiwa hancinta tace,

Banda lokaci inason sanardakai abinda nake ashirin aikatawa ayau sbd banason na mutu abanza batareda na tsayarda abinda ke faruwaba.....

Wani irin tari tayi jini mai tarin yawa ya fito bakinta kamar amai
Atake ya rungumota abinda bai taba ba arayuwarsa hawaye suka gangaro masa yafara girgiza kai yana hanata magana..

Girgiza masa kai tayi awahalce tace,

Taimakeni na shirya muje mukawa qarshen matsalar sbd 'yan baya su samu nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanarda mulkin adalci.

Kasa motsi yayi saidata saki kuka ahankali tana kallonsa cikin rawar murya tace,

Karka manta ka min alqawarin tsayawa dani dan kawarda matsalar data lalata farin cikinmu dana wainda basujiba basu ganiba.

Cikin wani irin hali yace,

Na miki alqawari amma banda sadaukar da lafiyarki ko rayuwarki meyasa z......

Rufe masa baki tayi cikin wani irin yanayi tace,

Mu barwa Allah zabi zai mana mafita.

Amatuqar wahalce ya taimaka mata ta shirya sbd tuni alummar mineelik da kewayenta suka hallara sbd mahimmin saqon daza'a bayyanar garesu.

Duk yanda yakeson daurewa kasawa yayi lokacinda zasu shiga inda dukkanin jama'arta zasu ganta jawota yayi ya rungume da qarfi cikin rawar murya yace,

Kisani har abada bazan saki hannunkiba zamu fuskanci duk abinda zai tunkaromu atare, ummu-rumanah bulama kece zuciyar maheer abdulshams so please fight this battle for my love...

Ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda zamewa daga jikinsa tana riqe hannun ammy dake hawaye gefenta Jakadiya dake gefensu tayi saurin miqawa ammy tissues ganin jinin yanason sake tsananta.

Ammy dakanta ta goge mata tana danne kukanta.

Murmushi tasaki tareda riqe hannun ammyn ta karbi tissue din tana goge hancinta zuwa bakinta da hannunta dake rawa sbd ko tsayuwa daidai bata iyayi abinda yafi daga hankalinsu kenan.

Sultan ma aranar da safe ta bayarda takardar sakinsa dan haka shima tuni ya fito ya halarci taron tareda sauran dattijawon masarautar duk da ayau jikinsa a sanyaye yake da abinda yake faruwar saidai a safiyar yau 'din ya gana da dukkanin 'yayansa dasuka zo dan halartar wannan taro kuma ganinsu ayau din da maganganunsu sun sanyaya jikinsa sunbar zuciyarsa da dana sani musamman maganganun maheer dayayi masa gameda mutuwar iyayen rumanah...
Hakan yasa ya ajiye dukkanin makaman yaqinsa akawo qarshen masifar duk da su sunriga sunbi sahu.

Tana fita ko ina yayi tsit dukkanin alummar gurin suka nutsu ahankali haroun yabada umarni nan take aka bayyanarda wata irin sabuwar karaga mai tsananin kyawu da kyalli mai daukar ido atake dukkanin jamar gurin mamaki da tsoro yakamasu musamman maheer dabaisan da hakanba yakalleta da sauri saiyaga tana qoqarin danne abinda takejine dan daidaita nutsuwarta yafasa maganar dayayi niyya ya damqe hannunta dake cikin nasa sbd har lokacin a tsaye suke taredasu ammy da jakadiya da masu tsaron lafiyarta.

Cikin wata irin budaddiyar murya sarkin fada haroun ya bude wata irin zungureriyar takarda mai daukeda tambarin masarautar mineelik dake daukeda saqon assultana yafara karantowa kai tsaye da qarfin muryarsa yanda kowa zaiji.

"""" NI SARAUNIYAR MINEELIK UMMU-RUMANAH BULAMA AYAU SHA BIYU GA WATA NA BIYAR A SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NA SOKE KARAGAR MINEELIK DAN KAWO QARSHEN MULKIN ZALINCI INA GABATAR MUKU DA SABUWAR KARAGA GA WANNAN MASARAUTA...HAKA KUMA AYAU SHA BIYU GA WATAN BIYAR SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NI UWAR MAGAJI SARAUNIYA UMMU-RUMANAH NA SAUKA KAN MULKIN MASARAUTAR MINEELIK TAREDA 'DORA SABON SARKI ABDALLAH ABDALLAH AMMED""

Atake dukkanin gurin yadauki wata irin kabbara da koke koken farin ciki da sbd wannan wani irin babban alamarine yazo musu na sauyi daga mulkin azaba musamman Abdallah Abdallah ammed mahaifin khaleefa mutum ne dazai kawowa rayuwarsu sauyi na adalci gashi shikansa baisanda zancenba.

Tsit aka sakeyi lokacin wasu irin majiya qarfin bayi kusan goma sha biyar suka ciccibo karagar mineelik Wanda keda wani irin girma tareda hularta.

Wani irin baro mai tsananin girma da fadi daukeda wani irin mahaukaciyar tukunta mai tsananin tiriri yaran negasi kusan su ashirin da biyu suka turo aka ajiye tsakiyar filin harabar.

Ta lumshe idanuwanta dasuka fara rufewa suna gani dishi dishi ta budesu daqyar ta iya 'daga hannu ta bada umarni atake haroun yabada umarni aka 'daga karagar aka saka ciki atake tafara nitsewa tana narkewa cikin ruwan dalmar tun tana gani dishi dishi sbd jinin daya balle hancinta atake idanuwanta suka rufe ruf ta yanke jiki ta zube gurin jini na qarasa balle mata ta hanci da bakinta.
#mamuhgee

*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_

*45*
Not edited.
Saki jikinsa yayi sbd wutar data daukewa jikinsa da wani irin qarfi ammy ta jijjigasa tareda kiran sunanda da qarfi ya durqusa tareda jawota jikinsa ya dauketa gabaki 'daya yabar gurin da ita.

Anso tsayarda nadin sarautar amma haroun ya fitarda saqonta na gaba dake cewa duk abinda zai faru kar a tsayarda nadin dakuma takardarta tagaba dake cewa a raba mara masarautar biyu a rushe Rabin a gina masallacinda yafi kowane girma a qasar Ethiopia.

Hakan yasa aka cigaba da nadin yayinda sultan dake zaune har aka gama bai motsa daga inda yakeba saida aka watse aka gano ya rasu zaune agurin gakuma jinin da aka ganin ya digo daga hancinsa.

Lokacinda su negasi suka rufu akanta dan ceto rayuwarta alokacin ne aka zo da saqon rasuwar sultan Wanda ya girgizasu ya qarasa wargaza dukkanin sauran nutsuwarsu musamman ammy data kasa riqe kukanta maheer yayi saurin rungumeta yana riqe nasa hawayen sbd Allah yasani yana qaunar mahaifinsa duk mugun halinsa sbd koyaya ya zama mahaifinsane.

Cikin qanqanin lokaci rasuwar sultan da halinda assultana take ciki tareda canza karagar mineelik suka yadu 'yan jaridu da kafafen yanda labarai sukaiwa masarautar wani irin dandazo ana yada abinda ke faruwa.

Dukkanin iyalan marigayi abdulshams sun halarto cikin tsananin baqin cikin wannan rana data riskesu musamman 'yayan marigayiya adama dasuke ganin sun rasa uwa da uba.

Da maraice akai jana'izarsa inda dubban alumma na nesa dana kusa suka hallara inda yawan jama'arsa yasa maheer jin sanyi sanyi aransa tareda yiwa mahaifinsa adduar samun rahamar Ubangiji.

Duk damuwar dayake ciki ta halinda rumanah take ciki bai koma gurinta ba sai dare bayan an watse.

Kai tsaye sashen ammynsa ya nufa inda ya tararda ita tareda sauran 'yan uwansa ya qarasa kusada ammyn ya zauna yana kallonta cikin nutsuwa da tausayawa ya riqo hannunta ahankali ya iya furta,

Allah yaji qansa ammynah.

Kwantarda kanta tayi kafadarsa tareda cewa "amin" da muryarta data shaqe kafin ta 'dora da fadin,

Kaje gurin rumanah dan sanin halinda take ciki duk da meenah da jakadiya na gurinta.

Jinjina kai yayi jikinsa na qara sanyi da tuno wani tashin hankalin dayake ciki.

Lokacinda ya isa sashenta har lokacin bata farfado ba sai jinin daya tsaya Wanda suke sakaran jinintane yayi matuqar qasa sosai.

Zaune ya kwana gabanta yana mata addua cikin wani irin hali dabai ta6a tsintar kansa aciki ba.

Washe gari koda akaga bata farkaba hankula sukai matuqar tashi musamman da jikinta yayi wani irin fari fari Kore Kore ga 'yan jarida dasuka kasa suka tsare a masarautar sunason ganawa da sarauniyar data kafa sabon tarihi a qasar daba tataba.
Chapter 49 · 0% Book details