← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 51

Sashe 32

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gaggauce suka kamata sukai sashenta da ita inda tun kafin su isa ta qarasa rikicewa sbd azabar naqudar.
Cikin gaggawa Jakadiya ta isa gaban sultan dake zaune cikin royalhall suna jiran haihuwar suhailat ta zube qasa kanta qasa ta sanarda shi ummu-rumanah ta shiga naquda yanxunan.

Da wani irin kallo ya dubeta zuciyarsa na shiga wani sabon farin cikin sbd yasan cikinsu biyun dole asamu namiji insha Allah.

Wani murmushi yasaki na qasaita cikin nuna isa yace,

Kije idan akasamu namiji a mineelik yau namiki na miki alqawarin dukiyarda bazaki iya qirgata da kankiba sai antayaki.

Cikin fargaba tayi godia ta fice hankalinta tashe sbd daga ita har sultana a gigice suke basa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sbd fargabar haihuwar rumanah dakuma babban sirrin dataji Wanda basusan ta yaya zasu fara fuskartartaba saidai abinda suka sani kome zatayi wannan sirrin bazai fadu garetaba babban tsoronsu da tashin hankalinsu kar Maheer yaji wannan alamari.

Kai tsaye sashen yarima ta nufa lokacin yana zaune palonsa na farko zaune ya dora qafafunsa kan table din dake gabansa ya rufe idanuwansa kallo daya zaka masa kasan kadaici yake buqata baya buqatar hayaniya sbd yanayin naqudar suhailat dayake cinsa musamman yanda yasan ta wahala haihuwarta ta qarshe gashi yanxu har lokacin bata haihuba yana iya sensing azabar datake ciki.

Gabansa Jakadiya ta tsaya tareda rusunawa cikin jimami tace,

Allah yataimaki uban magajin mineelik uwardakina ummu-rumanah ta shiga naquda yanxunan..

Idanuwansa dake rufe ya bude ahankali ya zuba mata suna sake canxawa sbd dama tuni suka canxa sbd zaman jiran na kashesa.,

Miqewa tayi ta fice jikinta a sanyaye sbd gabaki daya ta rasa nutsuwarta jitake kamar zata zauce sbd fargabar tashin hankalinda zai biyo baya idan rumanah ta haihu ta tambayi abinda taji ayau din.

Wayarsa daya kashe ya dauka ya kunna tareda kiran Dr ammenen muryarsa na bayyanarda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa yace mata tabar Dr noorah da nurse agurin suhailat taje gurin rumanah takuma babbatarda tana basa bayanin komai harta haihu idan kuma taga da damuwa takirasa kawai zaizo yakarbi haihuwar da kansa duk abinda zai faru yafaru.

Aje wayar yayi zuciyarsa kamar zata buga,
Yanxune yake sake takaicin haihuwarsu anan sbd acan shine zai karbi haihuwar kowaccensu da kansa musamman ita datake ta farkonta tana tsananin buqatarsa.

Dafe goshinsa yayi ya miqe yayi ciki ganin kamar zai iya rasa hakurinsa yaje musamman dayaga anfara jan lokaci babu wadda ta haihu.

Duk iya galabaituwa kowaccensu ta galabaitu sbd kowacce gadan gadan naqudar ta taso mata babu sauqi,

Duk Wanda ke cikin mineelik hankalinta a tashe yake tsit koina ana jiran tsammani
Sultan ma wannan karon saida hankalinsa yatashi shi fargabarsa kar doguwar naqudar tasa a rasa 'yayan dake cikin.

Ammy duk inda nutsuwa da kwanciyar hankali suke basa tareda ita ko zama takasayi addua tajeyi tana qarawa musamman datake jiyo irin azabarda rumanar ke ciki sbd tana palo suna ciki tareda masu karbar haihuwar.

Zufa mai zafi Jakadiya ta sharce lokacinda Dr ammenen takalli nurse tace,

Get ready ga babyn nan fitowa yanzu Ku kawo komai kusa.

Zufa Jakadiya ta gogewa rumanah data fice hayyacinta cikin tsananin tausayi da tashin hankali take mata sannu.

Cikin wata irin rikitacciyar azaba tayi wani irin nishi mai qara Atake baby ya fado Dr ammenen ta qarasa jawosa tareda yanke uwa ta 'dagasa sama ya buga wani irin kukan jarirai babu qaqqautawa.

Kadan yarage Jakadiya bata fadawa rumanah ba sbd rudewa da ganin abinda aka haifa.

Miqa mata shi Dr tayi jikinta na matuqar tsuma ta karbesa aka nado cikin farin zanin auduga mai tsananin laushi ta qura masa ido tana jera ajiyar zuciya ba qaqqautawa.

Wata sabuwar azaba ta tasowa rumanah cikin tashin hankali Dr takalli cikinta tana cewa nurse wani babyn na zuwa.

Jiki na rawa Jakadiya ta fito ammy data jiyo kukan jariri ta matso bakin qofar jikinta na 'dan rawa zuciyarta kamar zata fado sbd bugawar datakeyi a qofar sukayi karo da jakadiya hannunta na rawa ta karbi jaririn tana qoqarin budewa taga menene cikin rawar murya Jakadiya tace,

NAMIJI NE.

Da sauri ammy ta dago ta kalleta tareda hadiye yawu ta qurawa yaron ido jajir dashi babu inda ya dauko rumanah Sak maheer ne saitaji bazata iya cutatar dashiba.

Nurse ce tazo ta karbesa sbd aankeshi dazasuyi su kintsashi kafin dayan babyn yafado sbd naqudar takoma qasa tsananin wahala take sha ko ayanxun.

Jiki na matuqar 6ari Jakadiya ta isa qofar sashen maheer tun a qofar ta zube tareda 'daga murya tace,

Allah yataimaki uban magajin mineelik ummu-rumanah tasauka lafiya ansamu magajin mineelik da yardar Allah.

Zabura yayi daga kishingiden dayake yana sakin ajiyar zuciya da qarfi yana rufe ido sbd zaman jiran dayake shine abu mafi azabtuwa a tsawon rayuwarsa ayau ya raina zamtaowarsa likita tunda bai taimaki matarsaba lokacinda takeda tsananin buqarsa.

Fitowa yayi cikin wata irin qasaita hannuwansa zube a aljihunsa ya tsaya nesa da jakadiyar yana kallonta kamar tana daukeda abinda aka haifar yace,

Kije ina miki albishir da zama jakadiyar magajin mineelik tareda kyautar werik'i(gold)

Murna fal cikin ranta tace,

Ameseginalehu(godiya)

Miqewa tayi zata fita abakin qofa taci karo da 'yar saqo daga sashen suhailat ta durqusa qasa cikin girmamawa da rawar jiki tace,

Gimbiyar yarima ta sauka ansamu NAMIJI saidai likita tace sanarda yarima bazata sake haihuwaba mmahaifarta tasamu matsala wannan itace haihuwarta ta qarshe.

Zaro ido Jakadiya tayi cikeda tsananin mamaki da farin ciki tareda tausayin suhailat tajuya takoma gurin maheer tasanar dashi atake ya sake lafta mata wata kyautar zuciyarsa na harbawa da qarfi
Ya zauna ahankali tareda lumshe ido yana yiwa Allah godia.

Koda Jakadiya takoma sashen rumanah haihuwar tazo gadan gadan nan wani babyn ya fado Dr ta ciresa nanma sukaga namiji atake aka shiryasu jikin Jakadiya babu inda baya rawa ta zube gaban sultan kanta qasa cikin tsananin farin ciki tace,

Allah yataimaki kakan magajin mineelik ummu-rumanah ta sauka lafiya ansamu 'yan biyu duka MAZA sai gimbiyar yarima itama ta samu 'da namiji
Ina yiwa sultan farin cikin ganin wannan rana mai tarin cikar buri da biyan buqata,
Ayau mineelik ta samu qaruwar 'yaya uku uku duka maza ina sake taya sultan murnar ganin wannan rana.

Wani irin murmushi yake fitarwa mai bayyanarda farin cikin da zuciyarsa ke ciki bamai misaltuwa bane
Dukkanin Wanda ke royalhall din farin cikine mai tsanani a fuskarsa nan take aka buga bell din mineelik aka sanarda haihuwar magajin mineelik atake labarin farin cikin ya bazu koina Ethiopia ta dauka kowa farin ciki yake da wannan burin na qasar daya cika.

Dayake ba qaramar wuya dukkaninsu suka sha ba ana kimtsasu sai bacci banda rumanah data rufe idone kawai zuciyarta cikeda tashin hankali da fargaba tareda baqin cikin abinda kunnuwanta sukaji mata ammy na fada da bakinta.
Hawayen idonta suka gangaro batareda tadamu da gogesuba ta bude idanuwanta dasukai ja hawayen nacigaba da 6alle mata.,

Idan kunnuwanta sun jimata daidai ammynta ke fadar sune suka kashe mata iyaye kenan ba mutuwar Allah sukayiba qarfi da yaji aka rabasu da rayuwarsa,aka rabasu da 'yarsu,Ashe shiyasa aka 'yantasu???

Girgiza kanta tayi hawayenta na tsananta tace,

Ammy bazatayi hakaba nice banji daidaiba,ammy bazata iya kashe kowaba bare iyayena.

Sakin siririn kuka tayi tareda kifa kanta a pillow.

Suhailat kuwa bacci tayi sosai sbd ta galabaita fiyeda yanda ta tsammata saidai tana haihuwar taji batajin komai.

Lokacinda aka kaiwa maheer yaran duka yana tareda khaleefa daya iso ranar khaleefa ne yakarbi sauran biyun maheer kuwa Wanda aka fara haihuwa ya karba akaro na farko dayaji jikinsa yayi sanyi sbd soyayyar yaron dayaji shima yau yahaifi magajin kansa bama na mineelik kawaiba.

Qura masa idanuwansa yayi ganin yaron shine Zak sai lips din mahaifiyarsa daya dauko ya sa hannu ahankali ya shafo lips din tareda sakin wani irin murmushi qasa qasa yayiwa yaron addua kafin ya furta,

ABEEL HASSAN.

Kallonsa khaleefa yayi cikeda farin ciki ya maimaita sunan yana jinjina kai kafi ya karbesa ya miqa masa babyn suhailat da ba'ason motsasa sosai.

Qura masa ido yayi cikeda tausayinsa da qaunarsa mai qarfi shima shiya dauko Zak saidai zamansa qarami sosai yasa yafisu haske.

Addua yamasa sosai cikin rada rada ya furta,

Jemaal.

Koda ya karbi Hussain din abeel abrar bayan yamasa addua ya rada masa,

ABEEL HUSSAIN

Koda aka kaisu gurin sultan kowa saida yatabbatarda yau ranar daban take arayuwarsa ya 'dagasu daya bayan daya yayi musu addua kafin aka sanar dashi sunayen da yarima maheer ya rada musu sultan mai damuba sbd ayau angama masa komai arayuwa ya 'daga abeel cikin babbar murya yace asanarda kowa ga magajin mineelik ABEEL HASSAN.

Atake akaje dakin tarihi aka saka sunansa da sunan mahaifiyarsa nan aka fara shagulgulan haihuwar.

Har dare ammy bata samu ganin rumanah ba sbd tunda tayi wanka take rufe a dakinta tace bata buqatar kowa Hutu take buqata.

Lokacinda aka kawo mata yaranta qura musu ido tayi hawaye na gangaro mata sbd idan bar aka iya raba iyayenta da ita za'a iya rabata da 'yayanta saidai batajin hakan zata iya yiwuwa koda zata rasa rantane.

Rungumesu tayi tareda rufe ido qaunarsu data mahaifinsu na shigarta tako ina.

Da daddare lafiyyan abinci kala kala aka aika gefen kowaccensu aka jera.

Duk yanda Jakadiya da ammy sukaso ganinta qin bari tayi ta dasun shigo zata rufe ido tana bacci idan sun fita zata cigaba da kukanta.

Kukane takeyi na rashin Sanin abinyi sbd ko ganin kowa batason yi.

Lokacinda labarin haihuwar tasamu adama da 'yar dakinta mamani kadan yarage adama bata yanke jikiba mamani kuwa kasa daurewa tayi saidatayi kuka taji sauki sauqi cikin ranta.

Koda aka kawo mata yaran saka musu albarka saidata kai zuciyarta qololuwa gurin bugawa kafin ta iya kallonsu idanuwanta na cikowa da hawayen baqin ciki tasaka musu albarkar dole.

Suna fita ta miqe batareda takalli mamani dake matsar hawayeba cikin tsananin tashin hankali tace,

Duk yanda za'ayi ayi yaran nan bazasukai ranar sunansuba batareda sunbar duniyaba kije yanxu ina buqatar kadaici gobe zan fada miki abinda zakiyi sbd inason alhakin mutuwarsu ya rataya akan kakarsu da jakadiya sbd inason qulla gaba mai tsanani tsakaninsu da yarima tareda matansa kuma inason sultan ne da kansa zai yankewa sultana hukuncin kisa ta yanda abin zai riqa bibiyarsa yana damunsa da haka zansamu sauqin aikina akansa.
Chapter 32 · 0% Book details