← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 51

Sashe 31

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsananin murna rumanah tace,

Tun jiya yakamata ace ke nafara gani da mamani amma shine kikaqi zuwa sai yanzu danace anemoki ina mamani?

Baki washe tace,

Mamani qila wani aiki ya hanata zuwa nima sbd tun jiyan nake yawo a hanyar sashen nan sbd kawai naganki amma bansamu damaba yanxu ana cewa kekenemanmu na aje aikina nazo bakisan yanda na matsu nagankiba rumanah nayi kewarki sosai kinbarni cikin kadaicinki...

Hawaye suka sakata kasa cigaba da maganarta
Rumanah ma hawayen ne suka ciko mata idanuwa ta riqe hannunta tace,

Nayi kewarki nima nuratu saidai bayanda zanyine sbd kinsan da zabi ake bawa mutum nafison zama taredaku duk da ayanxu komai ya canxa arayuwata saidai matsayinku nanan keda mamani bazan ta6a canzakuba arayuwata.

Murmushin qarfin hali nuratu tayi tace,

Mamani bazata taba daukarki ayanda kika dauketaba.

Ni zan cigaba da daukarta matsayin yayar mahaifiyata har qarshen rayuwata bazan taba duba abinda takeminba tunda na saba.

Karkice haka rumanah sbd yanxu akwai banbanci bazanzo na rasataba sbd yi miki wani abu yanxu daidai yakeda rasa rayuwarta.

Karki damu da wannan yanxu zo muci abinci tare nayi kewar hakan sbd bansaniba kozan sake samun irin wannan damar tacin abinci tare dake.

Zama sukayi a babban dining din mai kujeru goma sha biyu nuratu na 'dar 'dar rumanah najanta da magana sbd tasaki jikinta ahaka sukaci abinci nuratu taci abinda takeso ta qoshi suka nufi palonta na qurya nan suka fara fira
Nuratu takalli cikin rumanah dayayi mata kyau matuqa musamman sbd bai sakata qiba ba tsawo yayi sosai.

Murmushi tayi cikin kulawa tace,

Nayi farin cikin ganin rayuwarki ta canxa rumanah gashi zaki haifar mana 'yaya jinin sarauta.

Kallonta rumanah tayi tasaki murmushi kawai sbd tunaninta ba akan firar tasu yakeba.

Agurinta nuratu ta wuni sai tsakar dare ta tafi koshi da sharadin gobe Jakadiya zata saka acanza mata aiki adawo da ita gurinta.
Mamani kuwa sunyi jiran zuwanta harsun gaji bata zoba gashi dokace akan rumanah bazata fita koinaba idanba da qwaqwaran daliliba harsaita haihu.

Washe gari aka dawo da nuratu aiki gurinta duk yanda taso hanata aiki tabarwa sauran kuyangin qi tayi saidatayi.

Kowace safiya da maraice sai Ammy ta Aiko mata da madara mai zafi itada suhailat harsukai kwana uku inda tun tana dannewa harsaida damuwarta ta daqushe kuzarinta matuqa dan ita kadai tasan halinda zuciyarta take ciki na rashin ganinsa gashi da alama bazata sake ganinsa ba saita haihu qila hakan ke sata kwantawa tayi kukanta sbd ji take nutsuwarta na neman gagararta abincima tun nuratu na iya yinta dan ganin taci har abin yafi qarfinta ta sanarda Jakadiya rashin cin isashen abincinda  rumanar keyi.

Lokacinda Jakadiya taje ta sanarda ammy hakan yarima na tareda ita bai 'dagoba amma ammy kallo 'daya tayi masa tagano halinda yake ciki musamman dama tana lureda shikansa miskilanci da mulkine yahana agano halinda yake ciki na rashinta.

Jakadiya tayiwa wani irin kallo nan take tagano me take nufi ta gyada kai ta wuce zuciyarta fal tsoro da mamakin irin sonda yarima kewa rumanah haka ta wuce taje kitchen ta bada umarnin ayi dukkanin girkinda akasan yarima maheer naso a shirya a palonsa na musamman zaici abincin daren tareda matansa.

Da daddare koda Jakadiya tazo kiranta cin abinci cikin yanayi na  rashin walwala tace batajin dadin cikinta bazata iyacin abinciba yanzu sai zuwa anjima.

Ba musu Jakadiya ta tafi

Koda yafito cin abincin cikin wata irin shiga ta musamman ta kayan shan iska qamshinsa na fita ahankali.
Suhailat dake zaune da cikinta ya kalla cikeda kewarta da tausayinta ya ware mata hannu ta taso ahankali tashige jikinsa ta rungumesa tareda sakin ajiyar zuciya.

Cikin kulawa ya dagota tareda kallon fuskarta da cikinta ya shafi fuskarta ahankali yace,

Hey hw are you?

Murmushin mai ciwo tasaki na qarfin hali tace,

Lafiya klau I missed you""ya fada tana zamewa daga jikinsa ta zauna kan dining sbd ita kadai tasan me ta hango a cikin idanuwansa.

Zama yayi yana sake kallonta ganin jikinta yayi sanyi lokaci 'daya duk saiyaji lissafinsa na sake kwancewa abincin gabaki daya yafita ransa.

Itama abincin fita ranta yayi saidai hakanan ta tsakuri kadan taci ta miqe tazo tayi kissing forehead dinsa tace,

Gud night""ta fice tana mayarda hawayen idonta.

Harta fice bai motsaba sbd damuwa da takaicin kansa dayaji akaro na farko.

Saqone yazowa Jakadiya daga yarima maheer cikin gaggawa ta nufi sashen rumanah ta bada umarnin duk wata baiwa dake sashen rabarshi cikin mintuna biyu kacal.

Babu 6ata lokaci dukkaninsu suka watse bayan koina yadauki sabon qamshi sai masu tsaron qofar shigowa ne kawai.

Kwance take lamo bakin gado idanuwanta a rufe tayi nisa cikin tunani.

Ahankali taji qamshinsa yana shiga hancinta ta bude ido tareda lumshewa zuciyarta na sake shiga damuwa sbd tasan har abada bazaizo sashentaba sbd atarihin sarautar mineelik ba'a taba yin sarki ko yariman dayaje 'dakin matarsaba saidai ita taje to mezaisa shi yazo gurinta.

Shafo fuskarta yayi ahankali cikeda kulawa yana kallon kyakkyawar fuskarta tayi saurin bude idanuwanta dasuka ciko da hawayen ganinsa saita samu kanta da mayarda idanuwanta ta rufe.

Rintse ido yayi cikeda mamakin kansa ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa murya qasa qasa yace,

Are you angry?

Bude ido tayi takallesa sbd bata taba tunanin zai kulaba harya tambaya.

Idonta dake kansa yakalla yana sake matse hannunta cikin nasa yace,

Tashi zaune.

Ba musu ta tashi zaune ya saki hannunta ya fito palo tabisa da kallo zuciyarta na qara mutuwa a sonsa,
Jin soyayyarsa takeyi har cikin jini da ruwan jikinta kowane bugawar zuciyarta da sonsa take fita tana fata da roqon Allah yasa kar soyayyarsa tasakata kaucewa hanya takoina koda kuwa sonsa da kishinsa zasu kasheta.

Jakadiya na ganin fitowarsa tayi saurin qarasowa tace,

Allah yataimaki uban magajin mineelik akwai abinda ake buqatane?

Hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa cikin wani irin miskilanci yace,

Ahado abincin cin mutum biyu.

Cikin qanqanin lokaci ta dibi abincin cin mutum biyo ta jero a tray takawo masa ga mamakinta hannu yasa yakarba ya juya dakin yabarta da baki sake sbd tsananin mamaki.

Duk yanda yaso tasakar masa fuska qi tayi yasamu ya lalla6ata taci abincin ganin shi baici ba yasata daukar abincin itama ta basa babu musu yaringa ci harsaidata kwatanci ya qoshi ta ajiye tana kallonsa da mamaki yadauki tray din yamiqawa Jakadiya dake palo ta fice da kayan.

Brush yakaita har toilet tayo suka dawo ta zauna bakin gado ya zauna kusada ita tareda kallon fuskarta dahar lokacin take kadaran kadahan duk saiya rasa me ke masa dadi baimasan mezaice mataba sbd baisan menene yake faruwaba gabaki daya ta qarasa dame masa lissafi ya dafe goshinsa tareda rintse ido ya bude ya miqe zai tafi kawai yadawo yajawota jikinsa ya rungumeta batareda yace komaiba.

Rungumesa itama tayi tareda barin hawayenta datake riqewa suka gangaro tana sake qanqamesa.

Tun jekadiya na jiran fitowarsa harta gane ba fitowar zaiyiba tabar palon takoma palon farko ta dasa sabon jira.

Tunda tabaro gurinsa mararta tafara ciwo ahankali tana shiga bedroom dinta takwanta tana qoqarin danne ciwon datake ji amma alamarin yafara qarfafa kafin tayi wani yunquri ciwon mara ya taso mata gaba 'daya gashi cikinta yanxune yashiga cikin wata na bakwai.,

Cikin qanqanin lokaci ta tabbarda naquda ce ta taso mata mai tsananin azaba sbd bata taba jin irin wannan ba a duk haihuwarta tun tana boyewa tuni yaci qarfinta koda Carolina taji kamar nishinta a dakin da sauri ta fita zuwa neman mutane duk da dare ya tsala sosai har anyi kiran farko.

Asubar farin yabaro part din yakoma nasa ita kuwa zazzabi ne mai qarfi ya rufeta bayan wankan datayi da asubar amma bata nuna masaba saida ya fice takwanta tana rawar sanyi mararta na mata ciwo ahankali.

Qarfe takwas na safe ta shirya daqyar tana daddaurewa sbd ta masa alqawarin zuwa gurin ammy yin breakfast su hadu acan.

Nuratu na lureda kamar batajin dadi amma tayi shiru sbd ganin kamar batason yin ko magana suka fito suka nufi sashen sultana ana biyeda ita bayi kuwa sai zubewa sukeyi suna bata hanya cikin tsananin girmamawa.

Jakadiya nacan tareda masu karbar haihuwa sashen suhailat hankulansu duk atashe sbd haihuwar  tazo mata da gardama matuqa
Shikansa lokacinda labarin ya iso masa hankalinsa ya tashi dan haka ko gurin ammy bai nufaba ya kira doctors din dake karbar haihuwar kasancewar yasansu duka matane suke karbar haihuwa a masarautar in brief sukai masa bayanin haihuwa ce zatayi ta wata bakwai kuma tazo da gardama sosai.

Kafin su isa sashen ammy ta lurada akwai abinda yake faruwa a masarautar sbd koina yayi tsit babu dogon motsi nuratu ce ta sanarda ita suhailat ce ke naquda.

Faduwa gabanta yayi zuciyarta na cikeda mamaki da tausayin suhailar da ita kanta batace komaiba sai sanyi da jikinta yayi tana mata fatan haihuwa lafiya.

Cikeda kaduwa da rashin sukuni ammy ta kalli Jakadiya tace,

Ya Allah karabasu lafiya saidai ina cikin damuwa da fargabar yaya haihuwar rumanah zata zo itama Allah kadai yasan mezata haifa.

Numfashi mai qarfi da sanyin jiki Jakadiya tasaki cikin rashin sanin abinyi itama tace,

Mafita 'dayace itace idan har anason sirrin mutuwar iyayen rumanah yazamo sirri daga gareta muyi adduar kar asamu namiji daga gareta idanma ansamu namijin mutuwarsa itace mafita.

Kallonta sultana tayi da sauri tana sake shiga rudu tace,

Mutuwarsa na nufin qarasa bankado komai Wanda kinsan hukuncinda zamu fuskaanta agun sultan zaifi musan hanyarda zamubi musan wannan sirrin yacigaba da zama sirri kamar yanda sultan yafada tun farko...
Saidai kuma zuciyata na quna da fargabar yanda zan fuskanci rumanah ranarda tasan mune sanadin mutwar iyayenta....

Da qarfi ruwan haihuwa suka 6alle mata lokaci 'daya sbd masifa da tashin hankalinda tashiga lokaci 'daya

Cikin tashin hankali suka juyo cikeda mamaki da tashin hankalin abinda taji kafin suyo kanta ta durqushe agurin cikin tsananin azabar ciwon mara nan take naquda mai qarfi ta taso mata.
#mamuhgee.

*_TARAYYA_*
_wattpad @mamuhgee_
_Haske writers association💡_

*32*
Not edited
_A gagguce_
Dafe cikinta tayi cikeda tsananin azaba da wani irin juyi da cikin keyi mata.
Arikice Nuratu ta riqota tana kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali
Su ammy atare sukayo kanta cikin sobon tashin hankali da fargaba
Ammy ta riqota tana kiran sunanta cikin damuwa take kiran sunanta.
Chapter 31 · 0% Book details