Sashe 40
Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kura mata ido yayi cike da jin ba daɗi da kuma hango yarda da Amana da tabashi sai ji yayi akaron farko bazai iya cika wani mugun kudiri a kanta ba, sunkuyar da kanshi yayi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki wanda bawai dan maganar da yake mata bane sai dan akaro na farko da zuciyarsa ta hango masa kuskure da suke shirin tafkawa ne Wanda zai iya bibiyarsu har jikokin jikokinsu na qarni mai zuwa.
Cikin nutsuwa tasake kiran sunansa tace,
Karka damu nimai riqe sirrinkace.
"A'a mineelik ina tsoron karki guje nine.
"Ina tare da kai nace ka yarda dani.
Gyaɗa kanshi yayi sannan yace,
"Nayi kokarin neman nakaina amma abu yaci tura daga nan kome na taɓa sai ya lalace kai ko kayan mutane na taɓa ya tashi aiki sbd baqin Jini da baqin qashin tsiya da'ake cewa inadashi daga nan mutane suka shiga jifana da mai kashin tsiya bani da albarka a rayuwa haka bai isheni ba sai na faɗa niman aure nanma mutane suka shiga korata a kofar gidajensu suna goranta min ynx waye zai yarda ya bani auren ɗiyar shi yanda tsiya da fatara ya kewaye rayuwata,
Qarshe ko qofar gidajen mutane sunhanani bi idan nabi qofar gidan mutum aranar saiya rafka babbar hasara tou tsangwama da qyama yasa nabar garin nashigo duniya shi yasa na shigo dajin nan sbd jin labarin ha'darinsa naso koma meyene aciki ya kasheni.
Abin tausayi abin dariya yar karamar dariya tayi wanda ya bayyanar da jerun kyawawan hakoranta farare.
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ɗan rufe bakinta cike da qaunarsa mai qarfi dake zuciyarta tace,
"Tabbas akwai abin dariya a rayuwar bil adama sbd kamar munfisu yarda da qaddarowar Allah ne.
Kallonta yayi da sauri cikin rawar murya yace,
Mekike nufi da bil adam ke kincire kankine daga bil adaman?
Kallonsa tayi cikin takaicin zancen datayi ta girgiza kai cikin son gyara zancen tace,
Dukanmu bil adama ne saidai wasunmu kamar basuda daukar qaddara sbd banga abin gudu da qyama ananba.
"Hmm kece kike ganin haka amma abin ba haka bane, aiku mata baku ɗauki kome da muhimmanci ba, tunda ba damunku abin yayi ba.
Girgiza kai tayi ni na amince zan aureka a duk yanda kake sile 'daya sun wadaci sadakin auren.
Mikewa yayi a razane tare da tsorata sbd baitaba kawo wata maganar aure atsakaniba yace,
Banda komai dazan inganta rayuwarki na kare martabarki amtsayin mijinki dan haka bazan iya lalata miki rayuwa ba.
Jikintane yayi matukar sanyi har tana dana sanin fada masa hakan sbd har cikin ranta takejin damuwarsa sbd tausayinsa mai qarfi da yayi wasi zuciyarta kamu tareda soyayyarsa mai qarfin gaske dan haka zata inganta masa rayuwa,
Zata basa kaf arzikinta saidai zata daukesa sunkoma duniyarta rayuwa acan zaifi musu dadi.
Ahankali ya furta idan har kin amince da aurena a yanda nake dinnan tabbas zan sadaukar da rayuwata gurin nema dan inganta miki rayuwa.
Yarda dashi yasa take kwanciya tayi baccinta batareda sakin dukkanin jintaba shikuma yana ganin tayi nisa a bacci
yasaci jiki ya nausa yamma da saurinsa da gudunsa sai tsakiyar dare sosai ya isa inda su Ajani suke tun daga nesa yake musu kukan wata tsuntsuwa dansu gane shine tafe dan karsu harbo masa hari daga nesan.
suna jiyosa cikin bacci duk suka mike
Suka fito rumfarsu yana isowa gabansu ya zube a wahalce yana fitarda numfashi tareda sakin ajiyar zuciya.
Amarine ya rungume shi cike da kewar kanin nashi yace,
"Da fatan anyi nasara?
Murmushi yayi ya nemi guri ya zauna, sannan yace,
Nasara tazo ne tareda matsala sbd tace na aureta.
Nan ya faɗa musu komai.
Shiru sukayi kafin Haji yace,
Toh ba zaiyu bane mu karɓi dukiyar da karfin cin tuwo basaika auretaba.
Wani mugun kallo amari yasakar masa zaiyi magana yonas dan boka yace,
Meya hana kai kaje gurinta sauka karbo da qarfin cin zaki bama na tuwo ba.
Zaburowa haji yayi tareda fisgo takobinsa mai tsananin kaifi ya nufi wuyan yonas Jamal yayi saurin tarewa yace,
Ba yanzu zakuyi wannan ba kubari mukarba daga baya kun kashe kanku,kafin ya kalli haji din cikin ido da Wani irin kallon banza dayayi masa cikin rashin jin daɗi abinda yace,
Lallai kusani koda barazana bazan karɓi dukiyarta ba sai da amincewarta.
Arazane suka hau kallon juna cikin wani irin mamaki da tabbarwa da maganar da boka yafada musu bayan tafiyar Jamal din da dayansu yaje.
ganin irin kallon da sukewa juna yasa shi shan jinin jikinshi sbd kuwa ya tabbatarda akwai wani abu dasuke boyewa.
Kuna qoqarin boye min wani abune akan mineelik?
Babu Wanda ya basa amsa sai kojo dayace masa,
Ko 'daya kashirya gobe zamuzo amatsayin nemanka muke daga nan zamu daura auren muyi abinda yakawo mu muje wata harkar sbd idan muka tsaya sanya zamu qarasa rayuwarmu ne a wannan dajin.
Juyawa yayi zuciyarshi bata aminta dasu ba ya fice yana tunane tunanen abinda suke boye masa dan kuwa yasan tabbas akwai abinda suke boyewa.
Bayan tafiyarshi Kojo ya kalli Ajani cikin bushewar zuciya da takaici yace,
Aqoob yayi gaskiya na cewar Jamal zai iya fara sonta na hango damuwa a cikin idanunshi ba jarumta ba kuma da zaran yasan da kudirinmu akan mataqin qarshe na mallakar dukiyar toh ba zai taɓa yarda damu ba kuma komai zai lalace.
Shiru sukayi dukkansu sbd bazasu taba bari banzar soyayyarsu ta kaisu ga rasa abinda suka sadaukar da rayuwarsu gurin nemaba.
Koda ya isa asuba tayi har haske ya'dan fara yayi saurin kwantawa yana wasi wasi akan mineelik da abinda suke boye masa,
hango wautarshi yayi da ya amince da bukatar ya yaudareta sbd yadaura ko a tsakaninsa da bil adama yar uwarsa ne haqqi baya barinka bare sarauniyar aljanu mafi hadari ko acikin sarakunan.
yana gurin har gari ya waye kafin tafito ya shiga daji nima musu abinda zasu ci.
Koda ya dawo taga rashin walwala akan fuskarshi tambayarshi tayi ko akwai wani matsala yace,
Babu kai tsaye yana juya mata baya sbd bayason kallon fuskarta yanzu jin yake zuciyarsa na karyewa da abinda suke shirin yi yanajin kamar bazai iyaba.
Shiru tayi ta cigaba da zama tana satar kallonshi da zaran sun haɗa idanu zata ɗauke kai tana murmushi haka shima yake qaqalo murmushin qarfin halin.
Kusan ita tayita janshi da hira, har ya sake da ita suka cigaba da hidimarsu can suna zaune sai suka jiyo sautin muryan mutane na doso inda suke mikewa tayi ta koma bayanshi tana leka inda take jin muryan mutanen.
Shikuwa dayasan da zuwansu bai wani nuna damuwaba saidai fargaba da wasi wasin abinda sukazo ayi wato auren.
Tabbas yanajin wani irin tsoro, fargaba shakku da wasi wasin aikatawa.
Cikin nutsuwa suka tunada gargadin boka aqoob dayace saisunyi matuqar taka tsantsan karta zargi wani abu ko taganosu dan kuwa rayukansu zasu rasa dukkansu idan aka samu matsala shiyasa
Su ajani ne suka iso har inda suke ja yayi da baya a tsorace su kuwa suka diro raqumansu da wani irin tsuma da far in ciki jikin na rawa suka qaraso gabansa cikin babbar murya kojo yace,
Jamal kasan abinda kayi da halinda kasamu ciki daka gudu aka rasaka?
Fiyeda kwana hudu muna yawo cikin dajin nan nemanka bayan mun share satittika muna yawon qauyuka nemanka mekakeyi wannan hadararen dajin....?
Kuka ajani ya saka cike da bakin ciki yace,
"Yau da ɗan uwanmu na raye ai kafi karfin wulakacin badan haji yace mu shigo ta daji ko kazo ka rataye kanka ba,
Gidanmu ya qone qurmus bayan barowarka shiyasa muka tabbatarda zamanka a gidanma kuma wata rahamace kayi hakuri mu koma musan yanda zamu dora itace muyi wani gidan bazamu sake bari a wulaqantakaba zamu samo maka mata mu daura maka auren dakakeso.
"Babu inda zani dan ni na sami wacce zata aureni da zuciya ɗaya bata damu da dukiya ko arziki ba.
Cikin Sauri da 'doki yonas yace,
Zamu aura maka ita yanzu dai kazo muje gida idan munje a daura maka ita acan tunda yanzu idan anyi bakada gurin sakata.
Shiru yayi alamar nazarin zancen kamar gaske.
Ita kuma cikin nutsuwa takallesa ganin yashiga tunani ta dafashi ahankali ya matsa mineelik ta bayyana daga bayanshi.
A tsorace sukayi baya zuciyoyinsu na rawa saidai jaruman gaske ne bazasu bari kyawunta da kwarjininta ya rikitasu ba.
Cikin sauri kojo yace wannan ba irin matarka bace bazata zauna dakaiba idan taga talauci zai illatata.
"Na rantse da abin bauta bazan barta ba ina sonta kuma zan aureta idan kuka ce bazaku barin na aureta ba zan kashe kaina na huta.
Cikin fusata Amari yace.
"Ka daɗe baka mutu ba wannan matar tafi karfinka ka nemi wata mana kokuma mu munema maka wata.
Ahankali ta matso kwarjininta da wata irin haiba dake fitowa daga gareta na girgiza zukatansu saidai buri da kwadayinsu yasa suke kannewa cikin jarumtarsu cikin wata irin murya mai dadi tace,
Ku auramin shi nikuma na muku alqawarin taskar arzikinda dar qarnin qarshe zuriarku bazatai talauciba,
Ina sonsa zan auresa ahaka kuma nayi alqawarin ko bayan mutuwa zan qaunace bazan barsaba wannan alqawarine daga sarauniya datafi kowace sarauniya mulki,
wannan son dayake min yafi min kome a duniya.
Wani irin kallo sukayiwa junansu cikin gamsuwa da burinsu yazo a sauqin dabasu taba tsammaniba.
Kojo ne ya matso gabanta suna fuskantar juna cikin rashin tsoro yace,
Mun amince zamu daura muku aure a yanxu basai anje koina ba saidai bawai dan kinada arzikin dazaki bamuba dan da alama kema nema kikeyi.
Murmushi tasaki ahankali tareda kallonsa takalli sauran dakuma raqumansu tace.
Idan sarauniya tayi alqawari bata canxawa,
Alqawarinta kamar rubutu ne akan dutse har abada baya canxawa.
Murmushi yonas yayi tareda kallonta cikin ido yace,
Mukuma alqawarinmu idan muka dauki burin abu kamar rubutu ne ajikin dutse baya goguwa sai muncimmasa.
Murmushi tayi tace,
Buri da alqawari basa haduwa sbd 'daya saiya danne 'daya yake tabbatuwa amma Ku sani zaku tuna hakan wata rana.
Kallonta sukayi a 'dage kafin amari ya kalli Jamal daya qura musu ido cikeda tunani kala kala aransa game dasu yace,
Yanxu za'a daura aurenka da sarauniyar ranka saidai kasani soyayya gubace mai kaifin gaske kafadawa 'yaya da jikokinka wannan.