← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 51

Sashe 5

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarkin gida gobe tundaga 6ullowar rana aje abudewa wanda yakawo saqonnan na yarima ma'ajiyar abincin masarautar meenelik yaringa dibar duk abinda yakeso yana kaiwa gidansa harsai rana ta fadi sanann yanxu yacire rigarsa ya shimfida acika masa itada sutura mai tsananin tsada kalolo ba iyaka wanda saiya 'dauka daqyar sbd wannan ce kyautar yarima ta farko agareni Dan haka wannan itace kyauta mafi soyuwa araina kyautarda mutuwace zata rabani da ita
Aje asanarda yarima kyautarsa ta faranta ran mahaifinsa ayimasa albishirda zuwa qasarda yakeson bin baturen malaminsa karatu.

Jin haka Dan aike ya zube jikinsa ba inda baya rawa sbd farin ciki yadinga rero kirari da godia kafin yafice daukeda kayanda sarki yace yana nishi daqyar sbd yawansu da nauyinsu.

Kallon bulama sarki yayi kafin yakalli su waziri cikin farin cikinsa dabai 6oyuba yace,

Wannan kyautace daga yarima bazaiyi bautaba bawan dazai riqa kula da hutawatane daga yau anadasa.
#mamuhgee
[20/06, 22:50] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡

*6*
Sashen sultana zaarah aka nufa da Asma'u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.

Lokacinda aka kaita gaban sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.

'Dagowa tayi cikin wani irin farin ciki da murmushi takalli asma'u cikin sanyin lafazi tace,

Allah yayiwa yarima albarka bisaga wannan kyauta.

Sake kallon asma'u tayi dake durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa jakadiyarta.,

Akaita abata 'daki sashen bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara aikinta.

Angama sultana.

Daki aka bawa asma'u kuma cikin sa'a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da'din zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da 'yar tasarsa
Anan ne asma'u suka hadu da bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.

Duk wanda aka bawa samun guri yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.
Daga ita harshi ba wanda ya iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.

Kwanansu biyu da zuwa jikinsu ya'dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd Sam babu yunwa ga bayin masarautar.
Asma'u da bulama iyakacinsu da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.

Ganin basuda yunwa kuma babu azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga ayyukansu damuwar bulama 'dayace cikin jikin asma'u da mamani.

Sosai asma'u ta dangana ta rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana sake mata ba laifi.

Aiki da bauta takeyiwa sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.
Tunda sultana zaarah ta lurada cikin jikin asma'u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa hkr ta tsare asma'un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.

Cikin tsananin tausayawa sultana tace,

Karki damu asma'u Allah baya bacci kuma insha Allah za'a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba nasan zasu dawo.

Sosai sultana tasa jakadiya sassautawa asma'u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana keyiwa asma'u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita cinsu.

Kasancewarsu kusan sa'anni yasa sosai sultana tasa asma'u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta 'Dan sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna 'Dan ta6a fira wani zubin harda jakadiya.

Cikinta na isa haihuwa cikin ikon Allah suka haihu rana 'daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.

Dukkaninsu 'yaya mata suka Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.

Shiru yayi cikin jinjina alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.

Koda bulama yaga 'yarsa hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.

Huduba yayi mata kafin ya 'durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,

Kece kika cancanta daki za6a mata suna.

Yarima daya fito sashen sultan yaqaraso sashen sultana yana shigowa yaji zancensu kai tsaye yakalli yarinyar yakalli sultana yace,

Asaka mata UMMU-RUMANA..

Kallonsa sultana zaarah tayi fuskarta daukeda murmushi tace,

Mahaifiya kayiwa takwara maheer.

Mayar mata da murmushin kawai yayi tareda jinjina kai ahankali ya shafo fuskar jaririyar yace,

Allah ya raya ummu-rumanah.

Yana gama fadar haka ya wucewarsa sultana takalli bulama tace,

Allah yaraya ummu-rumanah.

Amin sukace cikin farin ciki da godiya harda jakadiya.

Yarinyar mamani ma shine yayi mata huduba mamani tasawa 'yarta suna NURATU.

Tunda asma'u ta haihu hankalinsu yasake kwantawa itada bulama tuni suka maida hankali ga bautarsu
Idan zatazo sashen sultana adaki suke barin 'yayansu itada mamani daga baya sultana tace tariqa zuwa da ummu-rumanah

Sosai lokaci yaja tuni ummu-rumanah ta fara girma
Daga ummanta sai sultana da jakadiya tafi sabo dasu sai nuratu dasuke wasa tare a can sashen bayi mahaifinta ta saba dashi sbd ana 'Dan basa damar zuwa ganinta itada ummanta wasu lokutan da haka rayuwa tayi nisa sosai.

Sultan an wayi gari baida amintaccen bawa kamar bulama sbd takai ko fita za'ayi wata qasar da amintaccen bawansa bulama yake zuwa gashi da tsananin biyayya da taka tsantsan sbd sultan nada qarfin mulki da iko sosai da wasu irin dokoki.

Ummu-rumanah nada shekara goma sha hudu cif aduniya Allah yayiwa bulama rasuwa sanadiyar ciwon ciki.

Anji mutuwarsa duk da kasancewarsa bawa hakadai asma'u da rumanah suka dangana da rashinsa saidai rasuwar ta ta6a asma'u sosai,
Ta rasa lafiya da nutsuwar zuciya tun tana daurewa tuni ciwo ya kwantarda ita hakan tasa rumanah karbar ragamar aikinta a sashen sultana.

Kwanciyar hankali tuni ta qauracewa rumanah ganin babu uba ga uwarta na jinya sosai

Sultana ma tana cikin damuwar ciwon asma'un Dana matuqar tausayin rumanah sbd jin asma'u takeyi tamkar 'yar uwarta ta jini rumanah kuwa dama amatsayin 'ya take agareta sbd tun tana shan nono tayi sabo da yarinyar.

Anyi maganin har andanga anbarwa Allah ikonsa amma jikin yaqi sauqi ganin haka sultana ta 'yantata nanda nan aka shelar an 'yanta baiwa asma'u.

Rumanah ga abin farin ciki amma Sam batajinsa ita kadai tasan yanda takejin zuciyarta ganin mahaifiyarta sai qarayin nisa takeyi.

Cikin dare Allah yakarbi rayuwar asma'u tabar 'yarta cikin wannan duniya mai ababen tsoro.

Rumanah kam zuciyarta bushewa tayi sosai tabawa kowa mamakin rashin kukanta har aka kai asma'un aka dawo.

Sultana zaarah lokacinda ta aika kiran rumanah tana zuwa ta durqusa gabanta kallon rumanar tayi batasan lokacinda hawaye suka taru a idonta ba tayi sauri shigewa qurya sai alokacin rumanah tasaki wani kuka daya tokare qirjinta ta zube agurin tanayinsa jakadiya tayi saurin jawota jikinta tana lallashinta.

Andauki tsayin lokaci kafin rumanah tasaba da rayuwa ba iyayenta ga 6angare guda mamani Sam bata qaunarta bare ta rage maraicin rashin uwa sbd da mamani da nuratu take kallo amatsayin jininta.

Sultana zaarah kuwa sosai take nuna qaunarta rumanah wanda itama rumanah tana qaunarta sbd ita take gani tana rage kewar ummanta.

Da haka rayuwa taja harsuka qara zama 'yan mata ta maida hankali sosai ga bautawa ummy kamar yanda take kiran sultana zaarah.

********
ABDULSHAMS IBN ABDALLAH MUHD shine sultan na yanxu dake mulki a meneelik wani yanki na babban birnin ethopia kamar yanda kakanni da iyaye suka bar masa,

Mulkinsu wani irin tsauri da zafi dashi ga wani irin qabilanci dasukedashi sbd Sam basa bayi ko borori da 'yan qasarsu saida akawo musu na wata qasar su siya shiyasa yawanci bayin masarautar daga qasashe dabam dabam suke mafi yawansu Nigeria sbd rashin tsaro na zama Dan qasa da 'yan Nigeria sukedashi.

Tun lokacin mulkin kakanni a wannan zuriar ta ABDALLAH muhd basuda yawan 'yaya maza saidai mata wanda hakan yayita kawo barazana ga barin sarauta da mulki daga zuriar.

Duk wani kalar arziki na duniya Allah ya hore musu shi kobana sarautataba amma banda yaya maza daqyar cikin yardar Allah suka samu namiji 'daya cikin 'yaya mata goma sha biyu da sarkin yakedasu daga matansa uku.

ABDULSHAMS shine yazamto namiji daya kuma ya gadi sarautar bayan rasuwar mahaifinsa ABDALLAH.

Tun yana yaro qanqani mahaifinsa yake cusa masa qaidoji da hukunce hukunce masu zafi sbd karsuyi sake sarauta tabar gidansu matuqar ba magaji sbd arubuce yaje a aje duk ranarda suka wayi gari sarki ya mutu ba magani to masarautar da duk wanda ke cikinta zasu zamo qarqashin ikon masarautar kilaimee tamkar bayi dundaga kan matan sarki da 'yayansa har bayinsu sbd wata tsohuwar muguwar gabace atsakanin masarautun.

Hakan yasa duk wanda yayi mulki basa tsayawa kan matansu da qwarqwarori suke qarawa amma duk da haka sunada qarancin maza sosai sai arzikin 'yaya mata.

Yanxu lokacin mulkin sultan abdulshams yanada matuqar zafi da tsanani amma duk da haka baiyi na iyayensa da sauran sarukan dasuka gabata.

Zafinsa yasa dukkanin fadin qasar da zagayen ake tsoron hukuncinsa shiyasa kowa a ankare yake ba'a take dokar sultan ko acikin matansa bare 'yaya kafinma akai ga 'yan qasa da bayi.

Matansa biyu sultana zaarah 'yar sultan jalaludden sarkin Libya.
'Sai sarauniya adama 'yar tsohon wazirin mahaifinsa.

'Yayansa goma cif duka mata sai yarima tak shine namiji.

Sultana zaarah keda yara hudu
Amatullah,hindu dakuma maryamah duk suna aure,
Amatullah da maryamah a Libya qasar mahaifiyarsu suke aure sai Hindu dake aure Kuwait,yarima shine qaraminsu.

'Yayan sarauniya adama shida dukkaninsu mata kuma duka sunyi aure sai autarta najwah.

Duk qwarqwarori da sultan yake kwana dasu Allah baiba ko 'daya daga cikinsu cikiba bare tahaifi 'da namiji
Hakan yake tsananin 'daga hankalinsa ga tsufa yafara kamasa yarima yafito fili yafada bayada ra'ayin mulki ko wani Abu daya danganci sarauta

Kwata kwata rayuwarsa bata yanayi damai sarauta sbd tunda yagama primary aka kawosa Greece karatu harya gama yacigaba da degree dinsa a los Angeles kafin yayi masters duk akan doctoring shiyasa rayuwarsa kwata kwata ta turawa ce,
Daga nan yadawo da rayuwarsa a Georgia inda Yayi settling yafara aikinsa anan.
Chapter 5 · 0% Book details