Sashe 36
Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammy tayi saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta 'daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin 'dagota suka gansa kansu idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.
Cikin wani irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar dake tattare da wannan karagar.
Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,
Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.
Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.
Ammy dake zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK.......
#mamuhgee
Kuyi manage na fitane so mu kama gobe.
_*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_
*35*
Not edited
*Asalin Labarin mineelik*
Soyayya da cin Amana haɗi da Yaudara suka, kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836. Mafarin rigimar daga mutane huɗune, jigogin masarautar, Musaman Sultan Jamal wanda shi ya haifar da kome....
Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa, yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami, wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham, fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi mutune magananne, da kuma son raha,
"Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba."
"Wai shin Jamal baka gajiya da magane, haba tun da muka fito kaiɗai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana hakuri haka dan yunwa muke ji." inji Kojo.
"Shi kenan kojo nayi shiru kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba."
Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar sauran.
Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, ɗan tafiya kaɗan sukayi ɗayansu amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace.
"Ku dakata naga wani abu, kamar Zinari."
"Amari nima nagani tsoron siffar abin yasani shiru gashi can kamar mage ko?" Inji Jamal,
Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me ɗan nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine babbansu, cikin fushi yace.
"Dalla kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al'ajabi da ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito muje."
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
"Na rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma ni sai naga abinda ya turewa buzu naɗi"
Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,
Cikin laluma kojo yace.
"Shikenan zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman zinariyar."
Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka kunna wuta suna shan ɗumi,( bawai dan lokacin sanyi ba'a mutanen da suka kuna wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)
Zama sukayi a gurin, sannan suka ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi, sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.
Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar dasu.
Asalinsu wadanan, Fataken yan garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo ɗaya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,
Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daɗin zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.
Sai Autansu Jamal wanda ya kasance mutum ne hakuri da juriya ga barkwace da iya zama da mutane, kuma yana da shiga rai dan duk inda ya zauna sai kasamu ana alfahari dashi, sai dai yana da abun dariya dan idan yazauna kusada kai sai ya cika maka cikinka da barkwace da raha.
Wannan kenan....
Washi gari da safe duk suka tashi, nan suka karya a gurguje suka shiga dajin, niman zinarin nan, har rana takusan faɗi basu gani ba, tsurawa dajin ido amari yayi yace.
"Jamal jiya ba'a nan muka ga kyalin zinarin mai sufar mage."
Gyaɗa mishi kai Jamal yayi cike da bashi kwarin gwiwa, murmushi Ajani yayi sannan yace
"Amari zan tura kojo gari ya sayo mana kayan aiki sai mun tono wannan zinarin na yarda da kai."
Cikin farin ciki Amari ya rungume Ajani yana cewa,
Yene dan uwa.
Gurin tantinsu suka dawo suka ciro kuɗi silalar akabawa Kojo, yaje ya sayo kayan aiki.
Tafiya ce ta wuni guda dan haka ya haye rakuminshi ya kutsa cikin gari, bai isa ba sai da duhu ya fara rabawa, sannan ya isa gidansu anan ya kwana washi gari ya shiga kasuwa ya sayi abinda suke bukata wanda, na kayan tono,
Yana gamawa ya aza kayan akan rakuminshi,sannan yabar garin,
Tafiyar kaman dai yanda yazone sai da dare ya fara ya isa gurinsu dan ba iyakar kayan aikin yasaya ba, har da kayan abinci yasaya musu,
Zama sukayi a gurin suka ci abinda ya kawo, sannan suka shiga hira yanda zasu tono rijiyar zinarin.
Suna gurin har dare ya farayi sannan suka shige tantinsu.
****
Washi gari suka je inda suka hango zinarin suka shiga tonoda kwashe kasa, a hankali suka ta aikin tono har dai sukayi nisan zango ga dare yayi dole suka hakura zuwa gobe.
Washi gari ma haka suka cigaba da tonon ba dare ba rana har sai da suka shafe kwanaki goma sha takwas da yini daya babu zinarin babu labarinshi karshe hakura sukayi da tono, duk suka zauna jigum, cike da bakin ciki Amari ya fashe da kuka, wanda ya kashe jikin yan uwanshi, rarrashinsa suka shiga yi, kafin yayi shiru mikewa yayi yace.
"Dole sai na isa ga, Ebo sarkin bokaye dan shine zai iya duba min abinda idanuna ya gani."
Cikin son mara mishi baya suka mike take suka nufi cikin gari, dukda dare ne haka bai hanasu tafiya ba, har suka shiga garin gidansu suka nufa, suka kwana washi gari suka tashi dukkansu suka nufi gidan Ebo.
Sarkin bokayen garin, tun daga bakin kofar gidanshi suka hangoshi kwarjale, irin wanda mahajata ke raɓawa akafaɗarshi hannunshi rike da sandar tsafi, goshinsa yashafa bakin gari, inda yaja jan gari a goshinsa,
"Lalle lallae da zuwan sarakunan karnin farko, barka da zuwanku, a koda yaushe k'addara kamar zare ce mai kaifi, amma shahara da ɗaukaka tana biye a bayanta ku shigo ciki."
Jikinsune yayi sanyi, zama sukayi akan fatar zakin dake shimfiɗe, a tsakar ɗakin, shi kuma ya koma kan kujeranshi.
"Ina jinku."
Yace musu, tunda suka ɗauko niyyar zuwa gurinshi, yaji haka ajikinshi sai dai lokacin da ya hangosu yaga tagomashin ɗaukaka wanda yake ɗauke da duhun na ban mamaki.