← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kije na yafe sbd qauna da amincin dake tsakaninmu saidai haqqin ran 'yayana data dauka wannan tsakanintane da ubangijinsu shida ya haliccesu.

Ahankali ta furta,

ina fatar Ubangiji ya yafe mata.

Juyawa tayi ta fice rumanah ta juya ta zauna tana qoqarin saita nutsuwarta kartayi kuka saidai Sam takasa sbd duk yanda mamani taqita takashe mata 'dah ita din tatace.

Ta bayanta ya rungumeta jikinsa ahankali yana cewa,

Sorry luv.

Shigewa jikinsa tayi tana daina kukan dan tana buqatar rarrashin gabaki daya ta rasa ina ta dosa da rayuwarta.

Jin tayi shiru yasashi shafa kanta cikin sanyin murya yace,

Allah baya barin haqqin wani akan wani gashinan kin gani.

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sbd tunowa da abinda zatai dan kawowa kowa sauqi da qarshen masifar sbd a yanxu abeel dintane kawai ake jira ya gia yahau dan haka bazata taba bari 'danta yahau wannan karagar ba sbd ajikinta tanajin masifa da balain dake cikinta yana yawo cikin jininta ita kadai tasan yaya takeji take daurewa sbd shirye take da yaqar komai akan qarfin soyayyar datakewa mijinta.

Abu taji na fitowa ta hancinta ta taba ahankali tashafo taga jinine da sauri ta goge sbd kar Maheer yagani.

Shigowar ammy yasashi sakinta suka miqe gaba dayansu murya a tausashe suka gaidata ta amsa tana kallon rumanah dataga tayi wani irin fayau kamar ba jini a jikinta ta tsaya gabanta tareda riqo hannunta suka koma kan royal cushions dake palon suka zauna tana kallonta cikeda mamaki tace,

Rumanah ki fadamin gskia lafiyarki kalau?

Gefen Maheer daya kafeta da ido ta kalla ta sauke kai cikin sanyin jiki tace,

Lafiyata kalau.

Girgiza kai ammy tayi tace,

Rumanah wlh bakida lafiya wannan abun na cin jininki duba kiga kina canzawa rumanah karki rufeni kifadamin gskiar abinda kikeji.

Dawowa yayi kusada ita ya zauna yana zuba mata ido cikin tuhuma ya riqo hannunta zai duba tafin hannunta ta zame hannun tareda girgiza kai tace,

Lafiyata klau banajin komai....

Hancinta ya qurawa ido cikin daukewar numfashi yakai hannunsa ya shafo jinin dake gangarowa daga hancin ya kalla jikinsa na rawa ammy ma cikin tsananin tashin hankali take kallon jinin...

Ganin suna kallonta tayi saurin shafowa taga jini sosai ta miqe tsaye wani irin jiri ya dibeta ta yanke jiki gurin ta fadi idanuwanta rufe jinin na sake ballewa daga hancinta.

Cikin masifaffen tashin hankali sukayi kanta ammy tuni tafara kuka tana kiran sunanta

Shikuwa daukarta yayi hankali amatuqar tashe yayi bedroom dinta da ita ya kwantar ya fidda waya atake yakira khaleefa dasu dr abeena tareda sauran manyan doctors nasu.

Tissue yasa yana goge mata hanci saidai Sam jinin yaqi tsayawa gashi tafara wani irin jijjiga a rikice ya qanqameta jikinsa yana kiran sunayen Allah ahankali muryarsa na rawa dan yasan bazai iya kwatanto rayuwa babu itaba.

A gigice dukkaninsu suka iso tareda nurses da duk wasu kayan aikinsu atake suka fara qoqarin tsaida jinin dan maqala mata oxygen sbd numfashinta daya fara mata wuyar ja.

Dafasa khaleefa yayi tareda kallon yanda duk jikinsa ya 6aci da jini cikin kulawa yace,

Kaje daga palo gurin ammy zakafi samun nutsuwar bari mu dubata.

Palo khaleefa ya rakosa ya zauna kusada ammy yakoma ciki shi.

Riqo hannunsa ammy tayi cikin tsananin damuwa da tausayinsa dana abeel dake rungume ajikinta tace,

Zataji sauqi insha Allah.

Jinjina mata kai kawai yayi sbd ko bude baki bazai iyaba bare magana.

Atake rashin lafiyar assultana ya yada koina nan koina gari yafara 'daukar tsit sbd rufe shaguna da kasuwanni.
Acikin masarautar kuwa Sam ba wani dogon motsi tako wane bangare sbd jiran tsammanin farfadowarta.

Daqyar suka samu suka tsayar mata da jinin aka maqala mata oxygen tareda ruwa da sauran abubuwan da suka kamata amma har lokacin bata farfado ba.

Bayan duk sungama abinda zasuyi aka bar nurses uku dan kulada ita suka fice.

Lokacinda yashiga yaga yanda takoma lokaci daya
Ya zauna bakin gadon tareda 'dora hannunsa kan nata ya rufe ido
Shikadai yasan radadi da ciwon da zuciyarsa ke ciki ganinta ahaka.

Ahankali yace,

Tana farfadowa zamu wuce bazan iya zama anan ba kuma.

Dafasa ammy tayi tareda yarda da abinda yafada dan itama tagaji da nan 'din tana buqatar nutsuwar rayuwa kota maida hankali gurin istighfar ga ubangijinta.

Sai tsakiyar dare ta farka tareda bude idanuwanta ahankali ta qurawa masa ido yana zaune bakin gadon hannunsa cikin nata a damke idanuwansa a lumshe saidai tasan ba bacci yakeyiba.

Ahankali ta bude baki da siririyar murya ta furta,

Abu abeel..

Bude idanuwansa yayi da sauri tareda tashi zaune daidai yana kallonta fuskarsa na bayyanarda tsananin farin cikin daya shiga na ganinta.
#mamuhgee.

_*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡

*43*
_Not edited_

Murmushin qarfin hali tasaki tareda sake damqe hannunsa dake cikin nata tana kallon fuskarsa dashima ita yake kallo yana yiwa Allah hamdala cikin ransa.

Tashi zaune takeson yi ganin kamar batada qarfin jiki yasashi tayarda ita zaune tareda cire mata cannula dake hannunta ya gyara mata zama sosai.

Cikin sanyin murya da kulawa yace,

Ya kikeji yanxu?

Girgiza masa kai tayi tana kallon fuskarsa.

Jakadiya ce tayi knocking qofar dakin ahankali ta sanarda zuwan sultana.

Zare hannunta tayi cikin nasa tareda lumshe ido sbd yanayin datakeji ajikinta har lokacin.

Cikin nutsuwa ammyn tashigo idonta kan rumanah din
Hankalinta ya'dan kwanta ganin ta farka harta tashi zaune.

Qarasowa tayi tareda miqawa maheer hannu ya kama hannun da hannunsa daya cikin nutsuwa yace,

Ina kwana ya ammy?

Murmushi tayi tace,

Lfy klau..tana kamo hannun rumanah tace,

Ya jikin?

Naji sauqi ammy"""ta fada cikin qarfin hali da danne ciwon datakeji.

Miqewa yayi ya fita yana amsa kiran khaleefa dake kiransa kan maganar test result 'dinta dasuka fito.

Ammy dakanta ta kamata takaita toilet tayo wanka da brush tana fitowa taga doguwar riga mara nauyi akan dressing chair ta dauka tasaka ta shirya tana qoqarin busar da kanta sbd wankan tsarkin datayi na haihuwa ammy tashigo tareda nuratu dake daukeda babban tray Jere da breakfast ta ajiye zata juya rumanah takira sunanta ahankali.

Tsayawa tayi tareda juyowa cikin ladabi
Rumanah ta miqa mata hand dryer cikin sanyin murya tace,

Taimakamin.

Ammy na ganin hakan tasan magana zasuyi ta kalli nuratu tace,

Tayi breakfast.

Jinjina kai tayi alamar tou.

Ahankali take busar mata da gashin babu Wanda yayi magana acikinsu.

Tana gamawa ta daure mata gashin tareda ajiyewa a natse.

Miqewa tayi itama ta nufi inda take sallah tana idarwa ta dawo kan couch din dakin ta zauna har lokacin nuratu na tsaye kanta a sunkuye cikin tarin damuwa da kadaici.

Ahankali takamo hannunta ta zaunar da ita kusada ita ta kalli fuskarta kafin ta sauke kanta itama ta qurawa gabanta ido cikin sanyin murya tace,

Kiyi hakuri nabarki alokacinda kike tsananin buqatata,
Kin kuladani kin tayani kuka kin rarrasheni alokacinda na rasa nawa iyayen saidai ni nakasa miki hakan alokacinda kike buqatar wani ataredake..

Kallonta nuratu tayi hawayen datake riqewa suka gangaro mata tace,

Wlh idan nace miki bana buqatarki ataredani na miki qarya rumanah saidai yanayin rayuwa daya kawo bambamci arayuwarmu ayanxu rayuwarki daban take data baiwar datafi kowace baiwa baqin jini sbd mahaifiyarta data.....

Rintse ido tayi tareda budewa idanuwanta na cikowa da hawaye ta juyo ta kalleta cikin sanyin murya tace,

Ada damuke bayi rayuwarmu tafi kwanciyar hankali da nutsuwa tareda dadin gudanar da rayuwarmu,
Rayuwar bayi wata rayuwace mara yanci amma wlh wani lokacin tafi rayuwa irin wadda nasamu kaina aciki,

Nuratu idan zaka roqi Allah abu ka roqi alkhairinsa sbd wlh rayuwata ina baiwa tafimin kwanciyar hankali akan yanxu.

Gangaro mata hawaye sukayi sbd jin tausayin kanta da abinda zata fada tace,

Nuratu na 'yantaki daga yanxu ke ba baiwa bace kinsamu 'yancinki,
Babu wata rayuwar jin dadi da kwanciyar anan dan haka za'a maidaki gida acan zaki samu rayuwar kwanciyar hankali damukai burin samu idan ni bansamuba zan qoqarta gurin ganin ke kinsamu...

Kallonta nuratu takeyi hawayenta na tsananta gudu tace,

Tare mukayi alqawarin komawa gida.....

Zanzo wata rana nima idan nauyin alummar dake kaina ya sauka
Zanzo idan inada rayuwa da lafiya sbd burinane nima nahadu da dangin iyayena dan haka karkiyi wasa da damarki kice zaki jirani kije Allah zai sake sadamu da yardarsa.

Kuka nuratu ta fashe dashi tana girgiza kai tace,

Bansan ta yaya zan fuskanci mutanen da basusanniba nikadai nace musu dukkanin iyayenmu da sauran danginsu da akaje dasu sun mutu ba...

Itama kukan takeyi sosai saidai bazata iya cewa komaiba sbd wannan shine gatan datasan zata yiwa nuratu takoma gida ta fuskanci sabuwar rayuwa cikin amincin Allah.

Kuka sukeyi sosai na rabuwa da juna daqyar rumanah ta miqe ta bude wardrobe ta dauko wata jaka dake daukeda qatuwar sarqar zinari ta miqawa nuratu tareda juya mata baya sbd kukan datake riqewa tace,

Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi.

Ta baya nuratu ta rungumeta tana sakin sabon kuka tana cewa,

Kisani zan jira zuwanki har qarshen numfashina.

Daqyar suka saki juna suka fito palonta na biyu inda suka tararda ammy da maheer da khaleefa tareda Jakadiya suna jiran fitowarsu.

Fuskokinsu suka bayyanarda halinda suke ciki.

Ya qurawa fuskarta datai jajir ido kafin ya dauke kai yanajin damuwar ganinta hakan cikin zuciyarsa.

Gefen ammy ta qarasa ta tsaya ahankali ta bude baki tafada musu tafiyar Nuratu din zuwa qasarsu.

Ammy sosai ta yiwa nuratu addua da fatan alkhairi tareda cewa jakadiya nuratun ta sameta kafin washe gari ta wuce.

Bayan fitarta khaleefa yabi bayanta da kallo kafin maheer yayi masa magana da ido suka fita.

Bayan fitarsu ammy ta zaunar da ita tasa aka kawo wani abincin breakfast din.

A palon yarima maheer suka zauna cikin nutsuwa yace,

Khaleefa zaka karbi duk wani bayanin tarihin my queen da mahaifiyar nuratu ta bayar ka kaita har gida kafin ka karbi takardun iyayenta kayi amfani dasu ka nemomin asalinta.

Shiru khaleefa yayi yana sake tauna zancen sbd tafiyar ta jirgin ruwa ce sbd ta ruwa kawai zasubi su bulla garinsu nuratun kai tsaye a yanda akace gashi bai cika son tafiyar ruwa ba saidai kuma dole haka zai daure saidai suyi amfani jirgin dazasu isa cikin kwana biyu.

Acikin daren rumanah tayi kukan tafiyar Nuratu,
Iyayensu sunzo qasar dasu acikinsu gashi su zasu koma batareda ko dayansuba.
Chapter 47 · 0% Book details