← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 51

Sashe 16

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai qarfe 'daya da rabi yatashi daga barci
Ya bude idanuwansa dake cikeda bacci ya kalli agogon gefen gadonsa yaga time ya lumshe ido ya tashi zaune ya sauko gadon ya nufi toilet yayi brush yayo alwala yafito yayi sallah azahar yana gamawa ya tube harzai shiga wanka yadawo yayi amfani da wayar bedroom din yakira wayar palon qasa
Carolina dake kicin ta nunawa rumanah dake yanka fruits pancake dindata zuba ta fita da sauri.

Tana zuwa ta dauki wayar cikin girmamawa tace,
OK sir"""bayan tagama sauraran abinda yafada.

Aje wayar tayi harta juya sultana ta tambayeta abinda yace ta fada mata cewa yayi akai masa breakfast dinsa sama maida kallonta ga TV tayi tace takirawo mata rumanah.

Tana zuwa tace,

Ammy gani.

Rumanah ki hada breakfast a tray kikaiwa maheer sama.

Yawu ta hadiye ahankali tareda gyada kai ta wuce Dan hadawa.

Sanyi jikinta yayi amma ammy tafi qarfin komai agurinta,

Shirya komai tayi a tray mai kyau ta fito palon ammy ta nuna mata hanyar zuwa sama ta juya jikinta nafara rawa tana qoqarin saita kanta.

Harta fara hawa sultana tace,

Rumanahh.

Cak ta tsaya numfashinta na fita da sauri ta juyo.

Idan kinje karki tsaya palo kikai masa har cikin bedroom dinsa.

'Daga kai tayi ahankali ta juya tacigaba da hawa.
#Mamuhgee.
[30/06, 23:05] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_

*19*
Cikin nutuwarta ta tura qofar palon tashiga da siririyar sallama taga baya palon ta sake hadiye wani yawun tana qoqarin daidaita numfashinta da nutsuwarta ta nufi qofar bedroom din data gani tayi knocking ahankali sbd sanin bayason hayaniya.

Jin shiru yasa tasake knocking din amma shiru ganin kar abincin ya huce tayi laifi kuma ga tunanin bayason yin mgn ne yasa ta murda cikin tsoro tsoro ta shiga tareda rufe qofar ta juyo ta tsaya jiran umarni
kanta asunkuye yake jin shiru yasata dagowa taga baya dakin saitayi tunanin qila yana dayan dakin harzata juya sai qofar bathroom ta bude ya fito daure da towel a qugunsa light brown sabo qal murdadden jikinsa da muscles sai glowing yakeyi ruwan wanka na gangara alamar tsantsin fatarsa,
a tsorace ta kalli qofar idanuwanta yashiga cikin nasa da sauri ta juya masa baya duk ilahirin jikinta da muryarta na rawa tace,

Yi,,,ha...kuri ammy tace na..

Tray din hannunta ne ya kufce sbd rawar da jikinta keyi tayi saurin riqewa tana qoqarin saita nutsuwarta sbd jin baice komaiba har lokacin.

Bayanta ya qurawa ido duk da tajuya baya yana iya ganin yanda numfashinta ke fita da qarfi sbd kafadunta dake sama suna sauka baisan da ita akazoba saidai kuma baiyi mamakin ganintaba sbd sanin waye ammynsa idan tanason mutum.

Closet dinsa ya nufa yaciro kaya marasa nauyi,
Wata black transparent Louis vuitton longsleev yasaka da farin wando na Louis Vuitton sai turarensa na Clive Christian imperial Majesty.

Duk abinda yakeyi ko ajikinsa baburuwansa da tsayuwarta

Zama palo ya nufo batareda yace mata qalaba ganin harya fice baice mata komaiba ta biyo bayansa,

A palon ta tarardashi yazauna yana kunna wayoyinsa daya kashe
Sanin yanda jinin sarauta yake yasa ta matso gabansa a natse ta ajiye tray din kan table din gabansa ta bude masa komai cikin tsoro tsoro sbd gudun laifi.

Fridge ta bude ta dauko ruwa marasa sanyi sosai tazo ta ajiye masa.
Kallonta yayi wannan karon ba 'Dan mamaki sbd wannan shine karo na farko dazaici abinci agidansa da ruwa ajiye gabansa tun baici abincinba batareda yace akawo masaba,

Koyaushe idan zaici abinci suhailat da mai aikinta Carolina basa kawo masa ruwa kullum saiyace akawo masa bayan yayi nisa dacin abincin.

Ficewa tayi tasauko ta nufi kicin suka cigaba da aikinsu.
Bayan mintuna Carolina takoma takwaso kayan.

Saukowa yayi su amah dake fitowa daga dakinsu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa.

Daukar fammah yayi yariqo hannun amah yana cewa,

Heyy daddy's girls.

Zama yayi kusada sultana yana ajiye fammah kusadashi yace,

Gud morning ammy?

Morning or afternoon maheer look at the time.

Bai kalli agogonba yace,

Nace ina kwana ne ammy sbd bamu haduba tun safiyar yau sai yanxu so.....

Murmushi tasaki tareda dafa hannunsa dake kan nata ta juyo da kyau takallesa cikin kulawa tace,

Yaya suhailat I hope kunsamu shawo kan matsalar?

Shafa kan amah yayi yace,

Amah take your sister and go to your room idan nagama mgn da ammy zanzo okkk?.

Tashi sukayi riqeda hannun juna suka nufi room dinsu da gudu cikin wasa.

Lumshe oily eyes dinsa yayi batareda yajuyo yakalli ammyn ba yace,

Anmata cs babyn bezo da raiba
Sbd wahalar datasha sosai bamason ta farko yanxu saitayi 48 hours.

Kallonsa sultana tasakeyi cikin tausayawa tace,

Allah yabata lafiya yakuma tsare gaba amma babyn mace ce ko....

Kasa qarasawa tayi sbd faduwar da gabanta yayi na rashin wace amsa zai bata.

Its a boy.

Kallonsa tayi amatuqar firgice da tsananin mamaki saidai tayi saurin yin istighfar sbd agurin Allah komai mai yiyuwane.

Shiru tayi zuciyarta na wasi wasin abinda takeda niyar yi akan zaman rumanah dashi saidai tsoro yafara shigarta,
Idan dama 'yaya mata Allah yaqaddaro maheer zai fara haifa kafin yaya maza idan ta tura rumanah gurinsa tasamu ciki yanxu yaya kenan..
Rufe ido tayi Cikin Cikin zuciyarta tace,

Ya Allah kasa 'Dan nan daya shi maheer zai Haifa harsai sunsamu makarin dazai karye abinda ke bibiyar sarakunan mineelik.

Fitowar rumanah daga kicin zatazo tambayar ko ammyn nason wani tana ganinsa ta juya tun bata qarasoba sultana tabita da kallo tana cewa,Allah yakaremin ke 'yar amanata.

Tashi yayi yanufi dakin yaransa ya tararda suna drawings ya zauna bakin pink gadon amah yayi crossing legs ya qura musu ido sun saba da dadynsu bamaison magana bane yasa basu damuba presence dinsa kawai nasasu farin ciki.

Saida maraice yaje asibiti ya dudduba reports din suhailat sai bayan magrib yadawo lokacin ammy na bedroom dinta.

Kai tsaye ya wuce sama wanka yafarayi yasako jallabiya fara qal tareda tareda sakin gashinsa dakeda 'Dan tsawo ya sauko ya nufi gurin ammy.

Yana bude dakin tana budewa ta fito harsaida qirjinsu ya hadu da juna tayi saurin ja da baya tana sauke kai
Shikuwa yi yayi kamar baisan meya faruba ya shigo tayi saurin ficewa.

Dakinta taje tana shiga ta tube tafada wanka.

Tana fitowa tayi sallar ishai ta fesa spray ta saka kayan bacci Riga da wando farare masu santsi tana cikin daure gashinta Carolina tashigo tace sultana nakiranta.

Aje daurin gashin tayi ta dauki diguwar riga bai budadden gaba tasa tareda rufe kanta da hular rigar ta fita.

Zaune ta tararda ammyn bakin gado cikin shirin bacci cikeda girmamawa tace,

Ammy gani.

Yauwa rumanah idan kingama shirin bacci kije sama dakin maheer ki kwana can idan zaki kitafi masa da tuffa.

To tace kanta asunkuye tareda juyawa ta fice..

Wannan halin na biyayyar rumanah akan kome akasata yasa take qara qaunarta.

Bata koma dakiba kicin taje ta bude fridge ta dauko apples din guda biyar ta jera a glass bowl da 'yar qaramar wuqa ta fito ta nufi saman.

Sanin qila baya palo yasa ta bude qofar palon ta shiga ta nufi bedroom dinsa tayi knocking ahankali.

Saidatayi so uku taji shiru tasan bazai amsaba yasa ta bude dakin tashiga.

Zaune yake yana waya da doctor Edward daya kirasa yana fada masa wasu results din suhailat dasuka fito.

Gabansa ta isa ta aje kan table din daya Dora qafafunsa ta juya
Palo taje ta dauko masa ruwa da cup tadawo ta ajiye daidai lokacin ya gama waya ya miqa mata hannu tabasa ruwan yakarba yasha
Kamar bazaiyi magana ba yace bana buqatar apples din yanxu take them back.

Dauka tayi tamayar fridge din palonsa tadawo ta dauke cup da ruwan dayasha tamayar saita kasa dawowa cikin dakin ta tsaya qofar dakin tana zullumin komawa kuma bazataso taqi bin umarnin sultana ba koda kuwa a mafarkintane.

Tun tana tsaye qofar bedroom din hardai ta zauna bakin qofar dakin ta jingina da qofar ta lufe idanuwanta tana tunanin rayuwarta yanda ta jujjuyawa yau wannan gobe wancen,
Tafaro amatsayin 'yar bayi,
Tadawo baiwa daga baiwa takoma tamkar sa 'daka yanxu kuma gata a 'yantatta kuma matar 'Dan sarki batasan kuma gobenta meta tanadar mataba.

Da asuba ya tashi yayi alwala yasaka jallabiya da farar qaramar hula yasa ya nufi qofa Dan zuwa masallacin da dake kusa dasu na wani balaraben qasar.

Yana bude qofa yayi tuntube da ita kafin yayi qoqarin hana kansa kaiwa qasa tuni ya fada samanta da sauri suka kalli juna cikeda mamaki yake kallon idanuwanta dake cike taf da tsoro.

Kallonta yakeyi batareda yadagataba kokuma yayi mgn.

Idanuwansa yamaida kan qirjinsu dake hade numfashinta dake fita da qarfi yana qara hade jirjinsu.

Hawayen azabarda hannunta keyine suka gangaro mata kuma bazata iya cewa yadagaba.

Hawayen yabi da kallo kafin yakalli cikin idonta cikin wata irin murya yace,

Inada nauyine?

Rufe ido tayi ahankali tareda girgiza kai.

Sake kallon idonta yayi yagano wani Abu yatashi ahankali ya miqe tsaye.

Tashi tayi ta dafa zata miqe takasa sbd azaba Dan taji lokacinda kashin hannunta ya targade.

Hannun yakalla nantake yagane taji ciwone yagane dalilin kukanta kenan.

Hannu ya miqa mata cikeda bin umarni ta kama ya miqar da ita ta juya da sauri zata fice ya riqo hannun tareda dawo da ita harsaida ta fado jikinsa hular kanta ta Zame.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya zuba mata idanuwansa tareda kamo hannun ya matsa still idanuwansa na kanta

Rintse ido tayi da qarfi sbd zafi
cikin lazy voice yace,

Akwai zafi?

Saki jikinta yayi daqyar ta iya girgiza kai.

Mamaki tabasa wani malalacin murmushi ya fito gefen bakinsa ya sake matse hannun sosai sai kawai ganin yayi ta zube jikinsa idanuwanta na rufewa.

Shiru yayi yaji tabbas suman azaba tayi ya dago fuskarta yakalleta cikin maqoshinsa yace,

Unbelievable.

'Daukarta yayi ya kwantar a kujerar palon ya tayarda sallarsa hankali kwance saida yagama tukuna yadauko ruwa a fridge yazuba mata kadan

Ajiyar zuciya tasaki tareda bude idanuwanta ahankali
Kan fuskarsa idanuwanta suka sauka ta lumshe ido tasake budewa sai kawai hawaye suka fara gangaro mata.
Chapter 16 · 0% Book details