← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 51

Sashe 15

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa Sam bai lurada rumanah ba aka dauki suhailat akai cikin jirgi da ita yabi bayansu sultana da yara tareda rumanah da jikinta ke sanyaye suka rufa masa baya.
Amatuqar sanyaye take sbd wannan shine karo na farko data taba fitowa daga cikin masarautar tun duk tsawon rayuwarta.

Ganin yanayin suhailat dakuma ummu-rumanah yasa sultana yanke shawarar qin zuwa Libya binsu zatayi sbd batasan wani irin riqo su maheer din zasuyiwa rumanah idan basa ganin idon kowa duk da tasan ba ruwan maheer da ganin idon kowa akan alamarinsa.

Suna shiga jirgi a darare ta zauna kusada sultana tana kama jikinta kanta a sunkuye har jikin ya daga sama ta rintse idanuwa tareda qanqame jikinta.
#mamuhgee
[29/06, 21:22] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_

*18*
Tun acikin jirgi aka fara bata taimakon gaggawa jinin ya tsaya amma Sam bata farfadoba koba'a fada masaba mmatsayinsa na likiti yasan ba lallaine abinda ke cikinta ya rayuba musamman dasuka duba cikin ya daina motsi,
Adduarsa da damuwarsa itace suhailat ta tsira koda za'a rasa babyn ne.

Su amah dake taredasu sultana tuni sukai bacci
Sultana takalli rumanah da har lokacin bata iya gano yanayinda ta kar6i aurenta da maheer, farin cik kokuwa sabanin hakan saidai Sam yanayin sanyi na rumanar yakasa saka tagane yanayinta.

Cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.

'Dagowa tayi takalleta tareda amsawa cikin sanyin murya kafin ta sunkuyar dakai.

Rumanah karki sakawa ranki sbd maraicinki da zamtowarki baiwa duk wannan abin yake faruwa dake
Jarabawar ubangiji ce dakuma qaddararsa Wanda tuni ya qaddaro miki hakan,
Na tabbarda Allah zai haskaka rayuwarki sbd kinrugumi qaddararsa da dangana.,

Ina taredake rumanah,ke amanace agurina bazan taba bari ki cutatuba matuqar inada zarafi da ikon hanawa,

Naso kubutar dake daga wannan rayuwar ta hanyar 'yantaki sbd ki haramta ga yarima saidai bansan hakan zai qarasa hargitsa komaiba sai kuma Allah yayi yanda yakeso bamuda wani ikon hanawa saidai rumanah qaunar danake miki bazata sa nayi sonkai a wannan al'amariba
Yanxu ke ba baiwace kinada iko da ra'ayin kanki matuqar bakya son wannan auren nayi miki alqawarin zansaka maheer yasakeke zan mayardake masarautar iyayena ki rayu cikin aminci da kwanciyar hankali.

'Dagowa tayi takalli sultana
Duk wannan alamarin hawaye ko 'daya bai taho mataba sbd tariga ta rumgumi kome yazo da Wanda zaizo amma yanxu wasu irin hawayene suka ciko fararen idanuwanta takalli sultana ta sunkuyar dakai tareda rintse idanuwanta cikin sanyin murya tace,

Ta yaya zan bude bakina agabanki ammy nace banason zama acikin zuriarki,
Har abada ammy kece mai zartarda hukunci akaina nabisa koda 'yanci koba 'yanci bazan cewa aa ga duk hukuncinda zai fito daga bakinkiba,
Ni baiwace sai yanda akayi dani haryanxu ni baiwace agurinki banida zabi sai Wanda kuka zabarmin.

Lumshe ido sultana tayi cikeda tausayin rumanah batason takurata amma zasu bawa wannan auren dama basusan abinda Allah ya tanada acikinsaba.

Shiru suka sakeyi kowa da tunanin dayakeyi aransa.

Qarfe hudu na asuba suka isa,

Gida aka wuce da sultana da rumanah tareda yara shikuma maheer tuni motar asibinsa tazo sukai asibiti cikin gaggawa sbd yasan ma dole cs zasuyi mata.

Suna isa gidan sultana ta fito motar da kanta tasaka password na securityn gate 'din gidan sbd tasani.

Shiga sukai driver yayi parking suka fita yashigar musu da luggage dinsu har first palon dake qasa kafin ya aje keys din motar ya wuce dama drivern dake kaisu amah school ne.

Da gudu su amah suka nufi bedroom dinsu bayan Mac driver yakira Carolina a waya yace sundawo tadawo itama tace gatanan zuwa shiyasa suke murna sbd sunason Carolina tana kula dasu sosai.

Lafiyayyan babban bedroom din dake gefen nasu amah sultana tace rumanah ta shiga kafin itama ta wuce Wanda yazamto kamar nata idan tazo.

Jan kayan sultana tayi tabita dasu tashigar mata har dakin ta ta ajesu kafin tafara qoqarin gyaran dakin sultana ta dakatarda ita da cewa,

Rumanah kibarshi kiyi sallah tukuna.

Ba musu tace to tareda ficewa taje dakinta
Kasancewar batada kwadayin babbar rayuwa yasa duk tsaruwa da haduwar dakin bata tsaya wani kalle kalleba ta shiga bathroom tayo alwala tana fitowa ta bude akwatinda takesaka ran zata samu abin sallah tasamo doguwar Riga da gyalanta ta nada ta fito taje dakin sultana taga inda take kallo tana sallah takoma ta tayarda sallah.

Bayan tagama ta cire rigar sallar ta zauna shiru tana qara bawa sultana lokaci kafin ta miqe takoma 'dakinta tayi knocking ahankali kafin tabude tashiga cikin ladabi da girmamawa tace,

Ammy barka da safiya.

Kai kawai ta daga mata sbd gajiyar da rashin bacci dake tareda ita amma bata iya kwantawa matuqar ba gyara mata dakin akayiba aka canza bedsheets sbd ankwana biyu ba'a cikinsa duk da komai nanan lafiya klau ba'a cewama babu mutane acikinsa sbd babu ta inda iska zaishigo bare yayi qura.

Zanin gadon tafara yayewa daidai shigawar Carolina dakin nan ammy takalleta cikin turanci tace takawowa rumanah new bedsheets.

Da sauri ta karbi na hannunta data cire taje takawo wani fari qal sbd kusan gidan basu cika amfani da kowane kalar bedsheets ba kamar fari.

Karba tayi ta shimfida tafara gyaran dakin sbd Carolina taso karba tace tabarsa ita kanta sultana tafison aikin rumanah sbd itace kawai ke mata aiki yayi mata yanda takeso.

Tsaf tagyara dakin ta wanke toilet ta kunna AC da burner nan take dakin ya canza ta fice.

Tana fitowa taga Carolina nata aikin gyara koina an kunna duka ac ac da fridge fridge ta bude store ta debo ruwa da drinks ta jera ako wane frudge harna sama inda dakunansu maheer da suhailat suke
tuni gidan ya dauki sanyi da qamshi masu dadi
Itadai dakinta tashiga tayi wanka tasaka doguwar Riga baqa ta dawo ta zauna bakin gado tana jiran sultana takirata asata aiki sbd ita tafi sabawa da aikin wahalar Sam zama guri daya ko Hutu bata saba dashiba.

Sultana bayan takira maheer bata shiga itadasu amah bacci suka kwantayi cikin nutsuwa sbd agajiye suke sunsaba da Hutu su Sam jikinsu bayason gajiya.

A asibiti duk yanda sukaso ganin ta haihu da kanta abin ya gagara sbd taqi farfadowa duk wata allura sun mata har naquda suka qwaqwalo mata ta hanyar fasa mata ruwan haihuwa amma shiru shiyasa suka shiga emergency theater da ita kai tsaye sbd suna gap da rasata Dan tuni suka gano babyn ya dade da mutuwa.

Bashine yayi mata cs din ba doctor Edward yayi mata shiyasa haryasamu damar zuwa office dinsa yayi amfani da wayar office dinsa yakira sultana yasanarda ita halinda ake cikin.

Zama yayi tareda jingina bayansa jikin kujerar ya lumshe idanuwansa
Kwanakin nan he is in so much stress daga wannan sai wannan kansa har Sarawa yakeyi sbd baisaba da irin wainnan damuwarba.

Cikin ikon Allah anyi komai lafiya aka kaita dakin hutawa Dan har lokacin bata farfadoba,

Lokacinda duba gawar babyn saida yaji mumman faduwar gaba tareda dafe goshi kafin yasaki boyayyar ajiyar zuciya sbd ganin namiji ne,

Yana son duk abinda matarsa zata Haifa masa sbd jininsa ne saidai bazaiso ta haifi namiji ba yanxu sbd bazai iya bari uwar 'yayansa ta fada cikin harkar sarautar mineelik ba shiyasa ya godewa Allah Dan shikadai ne yasan meyasa yayi hakan.

Saidayaga komai yadaidaita jiran farfadowar suhailat kawai akeyi ya nufo gida.
Driver yakira yazo yadaukesa.

Yana isowa babu kowa a palon qasa sai Carolina dake aikin girka abinci a kitchen yawuce sama kai tsaye.

Komai Carolina tagyara a saman tundaga bedroom dinsa harna suhailat da palonsu.

Tubewa yayi ya shige bathroom ya shiga bathtub dinda tuni Carolina ta hada masa ruwan wanka cikinsa masu zafi kasancewar ya dade baidawoba yasa suka zama masu 'dumi.

Lumshe ido yayi sbd jin nutsuwa tafara jikarsa.

Ya jima kafin yayo wanka yafito ya shirya cikin kayan bacci masu laushi ya kwanta cikin gadonsa dake daukeda pillows masu laushi kusan guda takwas tareda shigewa duvet ya lumshe lazy eyes dinsa.

Sai qarfe goma sha 'daya su ammy suka tashi nan kowa yayi wanka yafito palo breakfast.

Batareda sultana ta kalli Carolina tace taje takira rumanah.

Knocking qofar tayi kafin tashiga.

Kwance take amma ba bacci takeyiba tana ganin Carolina ta tashi zaune tana jiran jin mezata fada.

Sanarda ita tayi ana kiranta ta juya ta fita.

Saukowa tayi gadon ta gyara hular doguwar rigarta data zame sbd gashinta da baya daure ga tsancinsa ta nufi qofar ta fita.

A palon ta tararda sultana zaune cikin doguwar rigarta mai tsada kamar koyaushe saidai duka sarqoqin kai dana wuya na sarauta datake sawa ko yaushe acan nan babu ko daya ajikinta saidai sarqoqin qafarta da bata rabuwa dasu.

Sosai tayi kyau cikin simple shigar shiyasa rumanah tasaki fuskarta da wani qayataccen murmushi ganin kamar hankalin sultana din ya kwanta ta qaraso gabanta tareda durqusawa cikin girmamawa tace,

Barka da tashi ammy.

Itama murmushi tayi cikin sakewa tace,

Rumanah abinci zamuci nace kifito kuma kisaki jiki nan gidan mijinki ne su amah yanxu tamkar 'yaya suke agareki saiki ringa kula dasu kema.

Girgixa kai kawai tayi kafin ta miqe ta nufi Carolina dake jera abinci a dining room tana zuwa ta sakar mata murmushi tareda karbar mata tray din samosas dake hannunta itakuma ta dauko sauran kayan suka nufi dining suka aje kafin taje tasanarda ammy angama komai.

Saidatayi serving ammy da duk abinda tasan tana breakfast dashi sbd ko acan itace tasan komai na abincin ammy.
Su amah kuwa Carolina ce tasan me sukeso ita tayi serving dinsu fammah ma abaki Carolina din ta tsaya tana bata sbd tasaba mum dinta ke feeding dinta idan tanan.

Harzata juya ammy tasata dawowa ta zauna a takure sbd rashin sabo acan tasaba layi sukebi abasu abinci suje susamu guri su zauna suci.

Cikin tsananin sanyi take cin abincin ammy na lureda ita takyaleta sbd tasan zata saba ahankali.

Itace tafara miqewa ta nufi hanyar kicin Dan taya Carolina gyaran kicin din dakuma girkin lunch.

Bayan su sultana sungama ita takwashe komai tagyara gurin sbd itadai idanma batayi aikiba batajin dadin jikinta.

Sultana palo tazauna kallon wani Arabic progm yayinda su amah sukai dakinsu Dan kallon cartoon.

Bata gane maganar Carolina itama bata gane tata amma suna kwatanta ganewa ahaka suka fara aiki suna qoqarin sabawa da juna.
Chapter 15 · 0% Book details