← Book details Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 51

Sashe 38

Tarayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,

Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.

Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.

Ammy dake zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK.......
#mamuhgee

Kuyi manage na fitane so mu kama gobe.

*_TARAYYA_*
_wattpad@mmamuhgee_
_Haske writers association💡_

*36*
_Not edited_
_A gaggauce_
Mineelik nada kwarjini da wani irin haske na tsananin kyawu Wanda yasaka Sam babu mai ganinta daga haifinta sai mai kulada ita shiyasa bakowane yasantaba musamman daya zamto itace kujerar mulkin mineelik ayanda abin yake mahaifinta yariga yayi amfani da wani irin sihiri akan karagar da sunan mineelik yanda ko bayan mutuwarsa babu Wanda zai iya raba mineelik da karagarta kuma barinta a nahiyar na nufin mutuwar duk Wanda ke nahiyar kuma babu Wanda yasan da hakan sai ita mineelik din da mahaifinta sbd ganin bai haifi namiji ba yasa aka fara farautar karagar mulkin.

Mineelik na zama cikakkiyar budurwa qannan mahaifinta su hudu suka hada kai suka kashe mahaifinta mutuwar wulaqanci sbd wani irin zalamar son hayewa karagar saidai bayan kashesa suka kashe junansu agurin sbd kowa nason shine zai hau.
Lokacinda mahaifin mineelik zai mutu saida ya shafawa karagar jininsa dake zuba na suka hudu dasukai masa cikin tsananin azaba da taurin zuciya tareda fushi mai tsanani ya daf karagar yace,

Ni penya maqagin wannan karagar ayau jinina ya zuba sbd wannan dazata zamewa duk wani makusanci agareta masifa  ayau ina mata baki mai hadeda tsinuwa duk Wanda zai hauta tazamo ajali mai masifa agaresa matuqar ba MINEELIK-ASSULTANAH bace take kanta har ranar dazata na'da wani akai da kanta sbd jinina da aka zubar akanta daga wannan qarni nawa ta haramta ga dukkanin qarni masu zuwa.

Lokacinda mineelik ta fito bayan mutuwar mahaifinta aranar duk Wanda ke bousk yaganta sukaga zallar kyawun halittar dabasu taba ganiba saidai cikin rashin sa'a fitowarta tasaka rayuka da dama mutuwa dan kuwa wani irin haskene da maganadisu atareda ita dake jan mutane zuwa gareta Wanda wannan abin shine atareda karagar mai janyo mutane da rufewar zuci da ido akan hawanta.

Ranarda mineelik tahau karagarta amatsayin assultana aranar akayi wani irin tashin daya faru aranar shine koda gari ya waye duk Wanda ke nahiyar babusa.
Tashin hankali data shiga shine tabarwa datayi alamun mulkintane bazaiyi kyawuba sbd karagar tayiwa jininta qarfi kasancewarta mace.

Ita kadai tayi rayuwa mai tsayi,shekaru masu tsayi batareda kowaba,
Kadaici,qunci,baqin ciki da kewa sune abokanan rayuwarta sai karagar wadda ahankali take zuqe mata tausayinta sbd babu wani Wanda za'a yankewa hukunci a zubarda jininsa shiyasa abin yake cinta itakadai makari 'dayane mahaifinta yasanarda ita na wannan karaga shine soyayya mafi qarfi amma idan idan sadaukarwar abu mafi soyuwa tashigo.
Sanin kaf acikin duniyarta babu Wanda zai iya ko 'dago kai yakalleta sbd kwarjininta bare ya iya samun soyayyarta saidai ta tabbatarda wannan azarbabin da  gaggawar tareda rashin tsoro da kwadayin sai bil adama.
Wannan shine burin
Hakan yasa ta rufe daularta babu  wanda yake ganinta sai ita tafara fitowa duniyar bil adama domin kuwa babu abinda take buqata da tsananin buri kamar soyayyar da babu irinta a qarnin.

Aduk shekara da kalar suffan datake fitowa saidai bata taba dacewaba amma alqawarine bazata daina neman soyayyaba harsai ta mutu. 

     Shiru sukayi dukkansu kowanne najin zuciyarsa a bushe babu wani tsoro ko fargaba sbd dama nema suka fita duniya dan haka su sunga zinari kuma bazasu danganaba harsaisun mallaki wannan karaga Ajani ne ya gyara zama yayi gyaran murya yace,

"Toh shi zinarin yana tare da ita kenan?

        Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da tabbarda abinda zai fada yace,

"Ita da kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.

              Kallon kallo suka shiga yiwa junansu saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin idon aqoob yace,

          Shirye muke da mallakar wannan dukiyar kota halin yaya koda soyayyar tatace mun shirya nema.

      Murmushi bokan yayi yana jinjina qarfin zuciya da buried tareda rudu irin nasu sannan yace,

"D'ayanku zai faɗa soyayya da ita amma kafin nan sai kunyi jiran  shekara ɗaya, wanda haka zai kasance kamar ganganci da wasa da rayuwarkune sbd hadarin dajin dakuma tsawon lokacin dakuma mataki uku masu matuqar hadari,
idan kuka tsallake mataki uku da zai faru kafin bayyanarta toh tabbas soyayyar  ɗayanku zai kulu da ita, sai dai ba soyayyar bace mai muhimmanci dukiyarce mai mahimmanci domin sonda zai gwada mata shi zai sanyanta buɗe mishi alkaryanta da taskar mineelik.

       Kallon juna suka sakeyi kowannensu idanuwansa acikeda rashin tsoro ajani yace,

"Toh boka matakai uku da zamu bi dan samun kusanci da ita menene fa'idar haka."?

  Mikewa bokan yayi tsaye, ya shiga zagayesu har ya tsaya a tsakiyarsu murmushi yayi yace,

Zakusansu da sharadin taskar arzikin tamuce muduka.

       Kallonsa sukayi cike da mamaki da jinjina kwadayinsa saidai zasu iya yin komai da mallakar taskar  kojo ya kallesa  yace,

"Mun amince, zamu raba da kai.

Dariyar  jin dadi yayi yace,

Tareda yarana biyu za'ayi wannan tafiyar tareda rubuta sheda a faifan fatar raqumi da jinin dukkaninmu za'ai rubutun kowa zaibada nashi arubuta a ajiye tarihi ya shaida wannan taskar arzikin mineelik tamuce mu duka.

Babu musu kowanne yafitarda 'yar qaramar wuqarsa dake some a qafafunsu suka 'diga jininsu a 'yar qwarya akai rubutun atake ya ratayesa a bangon dakin.

Yaransa biyu suka shigo yonas da haji yakallesu yace,

Gasunan kuma tabbas akwai haske mai disashe duhu akwai duhu mai disashe haske.

            Dayake zuciyoyinsu a shirye suke sun kafe kwaɗayi da son zuciya ya rufe musu ido ba tare da wani bata lokaciba suka amince Jamal dake gyara zaman wuqaqensa dake shanye da dafi kala dabam dabam na macijai da kunamu harma da dafin kada yace,

"Tunda nine zan fara aikin kwada soyayyata dole kasona yazamo mafi nauyi a raqumi.

       "Jamal kasonka shine mafi nauyi a raqumi sbd kaine zaka bamu gudunmawa mafi girma a cikin tafiyar,
abinda zai faru idan kuka isa dajin domin jiranta akwai tsoratarwa daga muyagun aljanu da dabbobi masu firgitarwa da suke yawo cikin dajin,   

     matakin farko zai farane daga kwanaki uku kafin bayyanarta zaku kasance kamar makiyan juna a ranar farko,
Zakiji tsana da qarfin son kashe juna mai qarfi na shigarku saidai karku bari hakan yaci qarfinku sbd dayafi qarfinku zaku kashe junanku cikin rashin imani.

rana na biyu kuwa bazaku ga giftawar tsuntsaye ko wata dabba ko dayaba ko wni iri har kukan namun dajin bazaku ji ba.

a rana na uku da zata bayyana wani mugun zafi da kishirwa zai buwayeku kamar zaku mutu, domin zaku ji har cikin jikinku zai koma kamar babu ruwa da jini a ciki, zuwa yamma ko dare zata bayyana, kai Jamal aikinkane kutsa kai cikin dajin domin haɗuwa da ita duk rintsi duk tsanani babu waiwaya.

                    Shiru sukayi cike da al'ajabi suke kallon kallo sabida jin abinda zai faru dasu wanda suke gani kamar faɗar bokane,

            Kallon bokan jamal yayi cikin nutsuwa yace.
"Wannan indai shine sharuɗan mun amince.

         Murmushi boka yayi sannan yace,

Tafiyace mai zuwa babu tabbacin dawowa abin bautarku ya kubutar daku.

           "Toh ni dai har yanzun abinda nakeson ji shine me zamu mata musamu dauko dukiyar mu mallaketa" Inji Amari.

          Kallon Jamal bokan yayi cikin murmushi ba shi yayi tambayar ba amma ya maida idanunshi kan jamal,

ɗaukar duwatsunshi yayi ya watsa har lokacin idanunshi nakan jamal,  juyawa yayi yace,

"Lokacine zai nuna mana abinda zai faru ynz zan baku wasu madaurin dantse ku ɗaura gudun karku cutar da kanku.

"Wannan zai kareku daga cutar da juna, sannan babu wani abinda zai cutarku nagama daku sai ranar da yasamu nasaran isa birnin Sarauniya mineelik, zamu karasa aikinmu nakarshe."

     Mikewa sukayi baki ɗaya suka fita koda suka isa bakin kofa, kallon jamal yayi cike da tausayi, sannan yace.
"Duk bayan lokaci mai dan tsayi ina son Babbanku yazo ya faɗa min cigaban da kuke samu."

Kallon 'yayansa yayi ya jinjina kai cikin muryar jarumta da bankwana yace,

Abin bauta yasa musake haduwa.

     Haka sukayi bankwana dashi suka tafi.

              ****
  Tunda suka tafi, kaman yanda bokan ya faɗa musu haka ya faru, sabida sun ɗaura ɗanbar wani kudiri a ransu, ranar farko, suna kwance sai suka fara jin shashekar kuka, kamar na yaro kaman na babba haka aka cigaba da razanasu da wani irin mahaukacin kuka, kafin aka samusu dariya irin na bantsoron nan, can da dare yayi tsakiya, sai kana kwance a cikn tantinka za'a zo ana kiranka daga kan ajani aka fara,
Chapter 38 · 0% Book details